HULƊAN DA TAKE TSAKANIN ALJANU DA ƊAN ADAM

 

            DARASI NA [1]



NAMIJIN DARE KO MACEN DARE

Wato hulɗar soyayya dake gudana tsakanin mutum da aljan,

 Ma,ana

Tsakanin macen mutum da Aljani namiji ko tsakanin Aljana mace da mutum namiji.


MATSAYIN ALJANI A WAJEN HAUSAWA

        Masana sl'adun Hausawa sunyi rubuce-rubuce da dama akan Aljanu da matsayinsu a rayuwar bahaushe.

      Sun kuma tabbatar da imanin Bahaushe akan samuwar aljanu, duk da yake baya ganinsu, amma yayi imani da samuwarsu da kuma kasancewarsu ɓoyayyu, masu kuma ban tsoro, masu ƙarfi akan mutane, kuma masu iya cutar dasu.

         Za,a iya fahimtar hakan tun daga sunayen da Bahaushe yake kiransu dashi.

  Bahaushe yana kiransu da waɗannan sunaye  kamar haka:

 • ISKOKAI.

         Wannan suna ya samo asaline daga bahaushe saboda baya ganinsu kamar yadda baya ganin iskar da muke shaƙa.

MASU ABU.

      Shi kuma wannan sunan ya samo asaline saboda su aljanu suna nuna isa ga dukkanin abinda suke nufin aikatawa ko suke buƙata.

  • MUTANTANI.

         Wannan kuwa saboda sunyi tarayya da mutane ta ɓangaren jinsi da hali.


       Abin nufi shine:

           Suna da jinsin maza da mata, suna aure kuma suna haihuwa, kuma suna cin abinci da dai sauransu.

     Koda yake imanin Bahaushe a zamanin baya , ya yarda cewa , Aljanu basa mutuwa, amma yanzu malaman ruƙya, sun tabbatar da cewa aljanu suna mutuwa.

       Sai dai suna da tsawon rayuwa ba kamar mutane ba.

         Ta fuskar yadda Bahaushe ya fahimci Aljanu kuwa:

1• 'Ƴan bori suna ganin cewa akwai farare da baƙaƙe.

• Fararen sune masu sauƙin mu'amala da mutane.

• Baƙaƙeen kuwa sune masu mugunta da sharri.


2• Malaman da suke ruƙya sun kasasu kaso biyu dangane da mu'amala dasu.

1• Musulmai.

2• Kafirai. 


         Bayan bayyanar muslinci a ƙasar Hausa, Bahaushe ya fara amfani da sunaye irin haka wajen kiran aljanu:

• Aljani.

• Ifritai.

• Rafani.

• Shaidani.

Da dai sauransu.


       Dalili kuwa saboda waɗannan sunaye sunzo acikin  nassin Al-ƙur'ani da Hadisin Manzon ALLAH {s.a.w}

      Saboda haka a yau, Bahaushe yafi amfani da waɗannan sunaye, saboda sunfi kusanci da addininsa na Muslunci.

            

WURAREN ZAMAN ALJANU

      Kamar yadda yake kowane abu mai rai ko mara rai yake da mahalli-wajen zama, haka suma aljanu suke da nasu mahallin-wajen zaman.

       Bahaushe yayi imani da cewar aljanun dake rayuwa a ƙasar Hausa suna rayuwa a ko'ina a ƙasar Hausa.

        Suma sunan yare-yare, yadda mutane suke yare-yare suma haka suke yare-yare.

         Sannan kuma akan samesu a wurare sanannu kamar guda huɗu, sune kamar haka:


1• Wajen Gari.

2• Cikin Gari.

3• Cikin Gida.

4• Jikin mutum.


        Waɗannan wurare duk aljanu suna zama kamar yadda bayanai zasu zo akan hakan ɗaya bayan ɗaya.


   Wuraren zaman Aljanu a wajen Gari suna zama a wurare kamar haka:-


1* Kan Duwatsu.

2* Gindin Manyan Bishiyoyi/Itatuwa.


kamar haka:-


• Bishiyar Kuka.

• Bishiyar Tsamiya.

• Bishiyar Gawo.

• Bishiyar Gamji.

• Tumfafiya.

Da dai sauransu.


3* Dokar Daji.

4* Cikin Ruwa/kogi.

5* Gidajen Tururuwa.

6* Fako/Tsan dauri.

7* Suri[Kunkuwa.

8* ]Tsohuwar Rijiya.

Da dai sauransu.


        Dukkan waɗannan wuraren da Aljanu ke zama ne a wajen gari inda babu mutane.


WURAREN ZAMAN ALJANU A CIKIN GARI 

   

Sune kamar haka:-

1• Mararrabar Hanya.

2• Kangon Gida.

3• Makabarta.

4• Juji ko Bola da wuraren zubar da shara.

Da dai sauran su.


      Dukkan waɗannan wuraren da Aljanu ke zama ne acikin Gari tare da mutane.


WURATEN ZAMAN ALJANU ACIKIN GIDA 

     

Sune kamar haka:

1• Ban ɗaki.

2• Tsakar Gida.

3• Ƙofar ɗaki.

4• Turakun Dawaki.

Da dai sauransu.


        Duk waɗannan wuraren da Aljanu suke zama ne acikin Gidan da mutane ke rayuwa.


WURAREN ZAMAN ALJANU A JIKIN MUTUM


Shine:

       Suna zama a ko'ina ajikin mutum, amma inda sukafi zama shine acikin ƙwaƙwalwa.

      Wannan yana da dangantaka da kiransu da suna ƙwanƙwamai.

       Duk waɗannan wuraren da Hausawa ne ke cewa mazaunin Aljanune, kuma mafi yawansu malaman Ruƙya da littattafan Muslinci sun tabbatar da hakan.


        Wannan tabbatarwar na daga cikin abubuwan da suka ƙara ƙaimin imanin Bahaushe da Aljanu kuma hakan ya ƙarfafa shi wajen cigaba da mu'amala dasu.

    Duk da samun wayewar kai  na zamani da bunƙasar ilimin Addinin Muslinci.


ALLAH shine mafi sani.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

2 Comments to "HULƊAN DA TAKE TSAKANIN ALJANU DA ƊAN ADAM"

  1. Masha Allah wato kayi bayani masu janhankali kwarai kuma masu fa'ida wanda yakamata ace dayawan jama'a susani kuma su kiyaye Allah yaqara basira da ilimi mai albarka

    ReplyDelete