Illar da Bleaching Yake Janyowa Mata Bayan Sunyi Aure

Macen da ta samo farin fuska daga shafe-shafen mayuka na bleaching, yana daga cikin dalilan dake sa mutuwar aure! Shafe Shafen Mayukan bleaching da mata sukeyi domun suyi fari yana haifar da rashin haihuwa! 

Yar uwa duk wanda yace miki maza fararen mata kawai sukeso, to karya ne. A cikin maza akwai masu son fararen mata, sannan akwai masu son bakaken mata. Ba kowane namiji ne ke son farar mace ba.

Nasan wanda aka shirya aurensa, ansa ranar auren da yarinyar da yabiya sadakinta, anajiran ranar tazo a daura aure. Shi angon baya nan dama.  Se ya dawo a satin da za'a daura wannan aure. Gashi yarinyan tayi bleaching  ta yi fari, sai ya ganta, sai ya ce, kafin yaje ya dawo yasan baka ce, shi baya ra'ayin farar mace ballantana farin mai.  Auren da aka fasa kenan, har yau yarinyar nan batai Aure ba.

'Yar uwata idan kika canza fatarki ta asali daga baki zuwa fari, idan mutum ya aure ki kuma mai son farar mace ne shi, ba tare da saninshi ba, bayan aure fatarki ta fara bayyana, har yakaiga  sanin cewa wannan fari kin siyo shi ne da kudinki. Zai daina sonki, idan ya ga kin fara dafewa kuma, sai ya fara wulakanta ki, kuma a karshe ya rabu da ke.

Kawar ki baka fata, da ta yarda da halittan ta, batayi bleaching ta canza fatar ta ba kuma, sekiga  Allah ya kawo mata miji mai son baka kamar ita, sa'annan ya aure ta, kuma su zauna zaman lafiya da mutuntawa, soyayyar ta kullum zai dinga karuwa a zuciyarsa domin ya aure zabin zuciyar sa. 

A cikin matan tsofaffin shuwagabannin kasarmu Najeriya da mataimakansu, da wadanda suka gaje su, akwai wadanda suka auri mata farare, da wadanda suka auri mata bakaken fata.

A cikin matan masu mulkin Najeriya a yanzu da tsoffin gwamnoni, akwai wadanda suka auri mata bakaken fata da kuma wadanda suka auri farare. Haka a cikin ministoci, ’yan majalisar tarayya da na jihohi, da kowane bangare na ofishin jama’a.

Duk wacce take son zama a gidan mijinta, ta yanda soyayyar ta za ta dinga karuwa a zuciyar mijinta, to wajibi ne ta yarda da halittar da Allah ya yi mata, Allah zai sa duka sauran mata ya dinga musu kallon maza, ita ekadai zai dinga yima kallon maza. Mijinta kenan.

'Yar uwata ba macen da mijinta ya ke sakin ta wai saboda ita baka ce, sai dai wacce tayi bleaching ta kode, kuma alamun asalinta bakar ce. 'Yar uwata, ko ance muku maza farare kawai suke so? 
To idan hakane, ya akai bakaken suke auruwa. 

Dafatn zamu gyara kuma muma kanmu fada. Bissalam

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Illar da Bleaching Yake Janyowa Mata Bayan Sunyi Aure"

Post a Comment