Illar Da Rowa Take Janyowa a Takankanin Al-Umma


1. Mai rowa ba ya dubi ko tunawa da ayoyin sadaka kyauta da taimakawa rayuwar wani.

2. Marowaci ba shi da tausayi don rowar sa na rufe ma sa ido ya kasa jin kai ga mabukaci na kusa ko na nesa ga yanke zumunta.

3. Marowaci ba ya iya rama alheri duk yadda ka ji6ance shi ranar da bukatar ka ta matso sai ya kaurace ma ka, rowar sa ta mantar da shi alherin ka.

4. Morowaci ya na da saurin gori na dan abinda ya yi wa wani, ga tuna jerin abinda ya yi ma ka koda kadan ne don shi gare shi iya kokarin sa ke nan

5. Rowa na hana ka amfani kanka, har ta kai ka kasa ciyar da kanka da iyalan ka, ko tufatar da su yadda ya kamata ta hana ka daukar nauyin iyali da kyautata ma su.

6. Rowa na zubar da mutumci, ta jawo maka kaskanci da hassada in ka ga mai alheri ya yi wa wani karimci ka yi ta jin haushi

7. Rowa na sa ka na korar mutane ma su son ka daga jikin ka don tsananin bakin hali da kin wani ya amfana da kai

8. Rowa na raba masoya a guji juna, in ko kaga marowata sun hada kai to ka guje su don dutsi da dutsi in sun hadu Tartsatsin wuta su ke yi

9. Burin marowaci baya cika, munin zuciyar sa na jawo masa rashin rabo da kwana cikin takaici.  Ba zuciyar alheri sai ta rama mugunta da son daukar fansa

10. Marowaci ba shi da yalwar kirji ko budaddiyar zuciya. Saurin fushi ne dashi da saurin fada da kin yafe gaba in dai akan ihsani ne ga wanin sa

11. Ranar lahira ba komi a littafin marowaci a 6angaren tausayi da jin kai da ciyarwa da sada zumuncta ko taimakon wani

12.  Dan uwa mu guji rowa don kullum shaiɗan a kewaye yake da kai yana neman rabonsa, bai rabuwa da kai sai numfashinka na ƙarshe. In ka mutu baka samun ladan dukiyar da ka bari fa, sai wanda ka nufi alheri da ita. Sau da yawa marowaci baya haifan kowa sai marowaci dan uwan sa

Ubangiji Ka rinjayar da mu kan shaiɗanunmu kasa mu cika da imani, ameen

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Illar Da Rowa Take Janyowa a Takankanin Al-Umma"

Post a Comment