Addu'o Domun Samun Karuwa na Haihuwa ga Wacce Bata Haihuwa

TAMBAYA TAMBAYA TAMBAYA


ALLAH MAI IKO KENAN, WASU SUN SAMU SUKA CE ALLAH IDAN KA BAMU DAYAWA BA ZA MU IYA KULA DA SU BA, DA 1 KO 3 YA ISHE MU, BARI MU YI "FAMILY PLANNING" WASU KUMA GA SHI NEMA SUKE YI IDO RUFE ALLAH YACE LOKACIN SU BAI YI BA

Assalamu Alaikum Malam, ina neman addua       da zan ringa yi na samu haihuwa, nayi bari sau daya na haihu wata shida, Tun daga nan ban sake ba, shekara 10 yanzu shiru ba labari

        AMSA
Wa AlaikisSalaam: Allahu Akbar Haka Lamarin Allah Yake Daman wasu Suna nema wasu Kuma Suna Cewa Allah ba su so ya ishe su har ma sune suke Kayyadewa Kansu abun da za su Haifa bawai abun da Allah ya hukunta musu zasu samu ba. Allah ya shirya.

Kema wata kila inda ace kin Zama Daya daga Cikin Masu Haihu Akan Lokacin su, da Yanzu Haka wata kila kun Fara shirya yadda zaku huta ke da Mijin ki, Wai sai ace idan an Haihuwa dayawa Za'a gagara rike su ko kula da Tarbiyyar su Za'a bar Yara Suna Yawo akan Layi ba'a San ma inda suke kwana ba, Ayya toh ai Daman idan ka Dauki Ɗiyar ka ka ba wa Wadda Bai da Tarbiyya Bai da Addini Bai San Darajar Na gaba da shi ba, Bai da aikin Yi to Babu yadda Za'ayi iya ya Rike Ɗiyar ka, ko Yaro 1 ne sai Allah ya Jarrabe su ya kawo akan titi Yana Yawo.

Toh Ni dai ban San wani Addu'a Akan wannan ba, Amma ki dauka Cewa Haka Allah ya kaddara Miki Babu Yadda Kika iya da kaddarar Allah, Sa'annan ki dauka Cewa Allah Yana Jarraba ba ki da ke da Mijin ki domin ya ga ya zakuyi? Sabida Haka idan kun ji tsoron Allah kun mayar da komai naku daga Allah ne Kun yarda Cewa Lallai Allah shi yake bayar da komai ga Wadda shi yake  so, kuma ya hanawa Wadda ya so, shikenan sai ku ci gaba da yin Addu'a In Sha Allah indai Allah ya rubuta Miki Cewa Za ki Haihu da Wannan Mijin naki, toh In Sha ko ba ki Sha Maganin komai ba idan Lokacin ki yayi za ki Haihu da shi komai Lokaci ne kada kuyi Gaggawa ga Lamarin Allah. Akwai wasu Matan Matan Kuma Matsalar su na Jinnu ne, toh wannan Babu Yadda zata iya sai an Kawar Mata da Jinnun tukuna ta Fara Haihuwa.

Sabida Haka Kawai a kullum ke da Mijin ki ku yawaita yin Addu'a Sosai toh In Sha Allah indai Allah ya rubuta da Rabon ki Haihu da shi In Sha Allah za ki Haihu da shi.

Idan Kuma Mijin ki Bai da Tauhidin hakan, Ma'ana shi da Dangan sa sun saka ki a Gaba Cewa ba ki Haihuwa, dalilin Haka ne kullum suna tayar Miki da Hankalin ki Babu Natsuwa ko Kwanciyar hankali, toh ko a dalilin irin wannan idan Allah ya so ya ba ku Haihuwar tare da shi, sai Allah ya Rike Kayan sa ya hanaku, Amma matukar da ke da shi da Iyayen sa duk sun Yarda cewa bawai yin kanki bane wannan ai daga Allah ne, Haka Allah ya so ya gan ki kuma yafi su sanin dalilin da ya sa ya Jinkirta Haihuwar ki, ko kuma Lokacin da ya rubuta za ki Haihu Lokacin Bai Yi ba, to kin ga Babu yadda Za'a Yi ki Haihu Sa'annan Suka qi dane Sabawa Allah na Cewa ai kene kawai Kika Qi Haihuwar bawai daga Allah bane. To akwai matsala.

Abu na gaba kuma shi ne, idan tun a Lokacin da kike Cikin Mahaifiyar ki Cewa Allah ya rubuta Miki Cewa Lallai fa ko kin Auri wannan Mijin ba za ki taba Haihuwa da shi ba, to duk Shan Maganin ki duk Kashe kudin ki Babu yadda Za'a Yi ki Haihu da Wannan mutumin sai dai Wadda Allah ya rubuta Miki Cewa za ki Aure shi kuma ki Haihu da shi.

Domin akwai abun da gaba Dayan Ma'aurata suke mantawa da shi shine Lamarin Ubangijin mu, an yi Aure sai ki an fi Shekara 10 Mace da Mijin ba su Haihuwa ba wasu Shekara 2 ko 3 Babu Ko Barin Cikin, Amma kuma sai ki ga da wannan Mijin ya sake ta tayi iddar ta Auri wani daban, sai ki ga Nan take har ta dauki Ciki, kin ga anan Daman Haka Allah ya rubuta Mata Cewa Dole ne sai da wannan Mijin na biyu zata Haihu, Amma ko Shekara nawa zasu Yi da Mijin Farkon Nan sai ki ga Babu Haihuwar, Amma da an sake ta ta Auri wani sai ki ga Cikin har ya samu. Amma fa bawai Ina nufin ki ce Mijin ki ya sake ki bane A'a ba Haka nake nufi ba Ina ba ki misali ne.

Haka Nan za ki ga Namiji Bai Haihu da Mace ba misalin Matar sa 1 ne sun Dade Babu Haihuwar, Amma da ya Kara Auren wata sai ki ga Nan take har an samu Ciki, to Daman Haka Allah ya rubuta Masa Cewa duk yadda ya Kai ga Son ya Haihu da Wannan Matar ba zai taba Haihuwa da ita ba, domin Allah Bai rubuta Masa zai Haihu da ita ba Babu yadda zai Yi ya Haihu da ita sai ki ga Yana sake ta ta Auri wani Haihu da shi shima ya Auri wata ya Haihu da ita.

Irin Haka kuma sai ki ga an dage ana ta neman Haihuwar Amma wallahi sai Allah ya Jarrabe ku ya hada ku da Yaro fitinanne Wadda baya jin Maganar ku, domin me kun Yi Gaggawa kun yiwa Allah Tsitsigi a Lamarin sa Dole ku samu Yaron da zaku dawo Kuna Allah wadai da Haihuwar sa.

To Haka Lamarin Allah yake tafiya, don Haka wannan bawai abun Tashin hankali bane ga Wadda ya San ilmin Addinin sa da Kuma Wadda yake da Tausayin Mace, wasu Mata dayawa Suna samun matsala Sosai ga Mazajen su da Dangin Iyayen Mijin su wasu Matan Aure a Irin Haka Mijin su ya Qi kula da su Wai don ba su Haihuwa sai nemi Haihuwa ta kowanne Hanya wasu su koma yin Zina Haka Rayuwar yake a yanzu, kullum Kina Cikin tashin hankali da masifar Mijin ki da Iyayen sa, Alhalin ke bawai kene kike bawa kanki Haihuwar ba, inda ace duk Mace ita ne take bawa kanta Haihuwar da sun tsira daga gorin Dangin miji da shi Mijin ta.

Wata daga ranar da Mijin ta ya Gane Cewa ai ba ta Haihuwa Allah ya Jarrabe ta da wannan Matsalar shikenan ta Shiga uku Wallahi, Jin dadi da Natsuwa da Kwanciyar hankali iya yin bacci Mai Kyau ta Dena shi kenan, Mijin ta ya sake nuna Mata Soyayya da Kauna ta rabu da shi kenan har Abada, Maza wannan Jahilci ne Bai kamata ba San Zalunci ne wannan da Rashin Tausayi.

Wata Mata tana bani Labari yadda suka Yi Auren Soyayya da Mijin ta Amma wallahi da suka Yi Shekara 1 ne ko 2 Babu Haihuwa, ki Zo ki ga Yadda Zaman su ya dawo, Yadda Kika San Annabi da Kafari yadda Kika San Auren Dole aka Yi Masa, Amma ta CE min wallahi a ranar da Allah ya Bata ciki tace Masa tana da Ciki, tun daga wannan Ranar har Zuwa Haihuwar ta zuwa yanzu, yadda Kika San Yau ne aka Daura Auren su ko kuma gobe ne Za'a Daura Auren su Haka Mijin ta ya dawo Yana kula da ita sosai Yana lallabata wallahi. Nace Mata Daman Haka maza suke, Kin ga kenan inda ba don Allah ya taimake ta Allah ya bata Haihuwa ba, toh wallahi a Ina ji bakin Cikin da zata deba sai Allah ne kaɗai ya sani a Karshe ma ta kamu da Ciwo a Ranta, Sa'annan yace zai Kara Aure kullum Wulakanci.

Shiyasa wallahi Wai Yan Matan da suke yin Aure a yanzu, Wai Budurwa sai ki ga tayi planning tun kafin tayi Aure Wai ita kada ta je gidan Mijin ta Haihu da wuri, ko kuma Wai sai ta je ta tabbatar da Eh lallai gidan Zaman ta ne, shikenan sai ta je ta cire Robar Planning din, ko kuma shi Saurayin Yace ta Yi Planning ana Bikin Su saura sati 2 ko wata, ko Kuma an Yi Auren kina Haihuwar ki Lafiya-lafiya yace kiyi planning, toh Wallahi idan kin Yi ke ne abun zai Zo ya dagawa Hankali, yadda Kika ga wannan Matar Mijin ta ya juya Mata baya ya chanja Mata Fuska kema Haka Za'a Yi Miki, idan ko kin Yi Wasa Allah ya Jarrabe ki kin Dena Haihuwar kenan har Abada ha za ki sake Haihuwar ba Haka Illar family Planning yake, domin na San Wadda Mijin ta ya saka ta tayi planning Wadda ake sawa a Hannu Bayan wasu Shekaru ya dawo yace shi Haihuwa yake so ta je ta cire, sai ta je ta cire Suna Jima'in Amma Babu Haihuwar sai ya koma Zargin ta Akan Cewa ai ta Qi ta Cire, Alhalin Kuma ta cire wallahi duk yadda Za'a Yi a samu Ciki ya Shiga ciki ya Qi Shiga Mijin ya koma Fushi da ita Akan Wai ta Qi Haihuwa, karshe yace shi Kara Aure zai Yi tunda ta Dena Haihuwa yanzu. Shin idan ya sake ki a wannan Halin me ya Miki? Idan Bai sake ba ya bar ki a Cikin Gidan ya Auro wata kina ganin tana Haihuwa ke kuma kin dene, shin me ya Miki? Sabida Haka Yan Mata wallahi ku ji tsoron Allah ku bi Lamarin Allah a Sannu a Hankali.

Sabida Haka ke ku ci gaba da yin Addu'a da jingina Lamarin ku zuwa ga Allah in Sha Allah idan Lokacin ku yayi zaku Haihuwa. Fatan kin Gane Koh??

Wallahu A'alamu.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Addu'o Domun Samun Karuwa na Haihuwa ga Wacce Bata Haihuwa"

Post a Comment