Dabino da Madara: Anfanin Shan su a Jikin Mutum
Thursday, September 7, 2023
Add Comment
A kasar IndiYa wadda a yau ita ce a sahun gaba ta fannin ayyukkan da suka shafi na kiwon lafiya da magani na zamani. Ya kasance al’ada a gare su domin tun a zamanin da sun kasance suna hada dabino da kuma madara a guri daya sai su sha da manufar inganta lafiya da karin kuzarin jiki da kuma magance wasu kananin rashin lafiyoyi da ke addabar su a yankunansu.
Shi dai dabino yana kunshe da wasu irin muhimman sinadirran da ke da dimbin alfanu ga jikin dan’adam, wadanda karancin wadannan sinadiran na iya haifar da wata illa ga jiki. ko baya ga haka, yana da wasu fili dake zama a matsayin maganin wasu cuttuka. A dalili da haka, dabino maganine ko baya ga zaman sa abinci.
A yayin da ita kuma madara take zama a matsayin protein da ake bukata dan ginin jiki, lafiyayyun kassa da hakora da kuma dai-daituwar aikin kwakwalwa.
Da irin dimbin sinadirran da ke a cikin dabino da kuma madara wannnn ne ya sa suka ninka duk wani maganin da za mu iya siya na Bature amfani. Domin sun za mu bitamin da ba wani hadi na kimiyar dan’adam a cikin su ballantana su haifar da wata matsala.
Dukan su suna kumshe da sinadirin Calcium wanda yake a gazawa kassan jiki, da kuma hakora.
Domin haka mai neman samun kwarin jiki zai iya fake amfani da madara da dabino.
Don shi ne ma ya sa ake danganta shi da kara kuzari wato yana hura karfin jiki.
Mai jin kasalar aiki ko saurin gajiya ko rashin karfi sai ya jarraba shan madara da dabino.
Hadin dabino da madara na taimakawa dan magance kananin cuttuka.
Kiba: Masu fama da rama maza ko mata marasa jiki kuma suke da bukata su yi kiba to sai su rinka shan madara tare da dabino.
Yana sa jiki ya samu wadata: Idan ana bukatar a jima ba a ci komai ba to sai a nemi dabino da madara kofi daya a sha, to a ranar fa sai dai a yi ta shan ruwa. kuma da zaran ka sha ruwa to za ka ji karfi kamar a lokacin ne ka ci abinci.
Yaran da yunwa (tamowa) ta kama ko wani da baya iya cin abinci ya koshi saboda da wani dalili to sai a fake masa dabino da madara.
Mai fama da karamcin sinadiran Bitamins da minerals a jiki to ya daina kashe kudi yana ta faman kwankwadar kwayar bature, sai ya fake dabino da madara.
Dabino da madara na kyautata aiki da kuma yanayin lafiyar zuciya.
Yana kiyayewa da karfin jiyojin jiki. Dan haka mai jin kasala ko neman karfin jiyojin jiki sai ya rinka shan madara da dabino.
Yana baiwa hanjin ciki damar samun motsi su fitar da iskan da ya gurbace idan ciki ya kumbura su fitar da kashi a sauwake.
Suna kara gani saboda dukansu suna kumshe da dimbin sinadiran Bitamin A.
Mai gani bishi-bishi sai ya fake amfani da madara da kuma dabino.
Mai yawan tinani na barkata sai ya rinka shan madara da dabino.
Mai saurin manta abu shi ma ya rinka amfani da dabino da madara.
Masu neman laushin fata musamman ga matan da suke son a ko yaushe a ga fatarsu kamar ta yara to sai su fake shan madara da dabino.
Mai fama da zafin ciki kamar na olsa sai ya rinka cin dabino kamar kwara bakwai tunda safe sannan bayan mintuna kalilan ya sha madara.
Mai neman karfin hadda da basira da samun dai-daituwar tunani shima zai rinka sha.
Gargadi
Kasancewa yanayin jiki da lafiya ta sha banban, abincin da wani zai ci ya sha ruwa ya ji ya gamsu, wani idan ya ci wannan abin cin sai ya sha magani.
Akwai mutanen da gabaki daya madara ba ta ba su lafiya. Takan kumbura masu ciki ta sanya su gudawa ko fitar da iska ko tashin zuciya. Wasu kuma na fama da basir matsananci wanda abu kadan mai dan zaki zai tado masu da shi. Wasu na fama da ciwon suga kuma an hanasu shan duk wani abu mai zaki.
Masu fama da irin wannan lalurar sai su kiyaye da wannan hadin.
Haka kuma idan ana shan madara to a kiyaye da cin kifi domin yana gurbata ciki.
Yanda ake hadin dabino da madara a cikin sauki ana shi ne:
Za a iya amfani da garin dabino sai a dibi cokali daya babba a sanya ga rabin kofi na madara ko a jika dabino idan ya jika sai a gauraya ruwansa dana madara.
Sau daya ya wadatar a kullum.
Related Posts
Subscribe Our Newsletter
0 Comments to "Dabino da Madara: Anfanin Shan su a Jikin Mutum"
Post a Comment