KARATUN LITTAFIN FIQHU NA 001


KARATUN LITTAFIN "FIQHU"

         
DARASI NA 001

MAWALLAFI
👇👇👇👇👇👇👇
(Dr. Salihu Ibnu Ganim).
_MAI GABATARWA
👇👇👇👇👇👇👇
(Muhammad Tukur Jalingo).

 KASHI NA DAYA:-
Ya kumshi abubuwa kamar Haka:

1. Tsarki.

2. Sallah.

3. Zakkah.

4. Azumi.

5. Aikin hajji.

6. Layya da yanka na suna.

7. Jihadi.

 *_KASHI NA DAYA:-_*
 1- Ibadu.
Rukuni na daya daga cikin rukunnan Musulunci shi ne: Tsarki.

⭕Ma’anar tsarki a yaren larabci da malamman fikhu.

Tsarki a yare shi ne: Tsafta da tsarkakewa

 A wajan malamman fikhu shi ne: Gusar da abun da ya taba jiki wanda ke hana Sallah da sauran su.

 _RUWA:-_
Nau’in Ruwa: Ruwa nada nau’i uku, su ne;

_NA DAYA:_ Ruwa mai tsarkakewa shi ne kuma wanda ya tabbata akan siffar sa wadda aka halicce da ita, kuma shi ne wanda ke dauke hadasi ya kuma gusar da najasa, wadda ta yadu a wuri mai tsarki, Allah Ta’ala ya ce:

﴿ وَيُنَزِّلُ عَلَيْكُمْ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً لِيُطَهِّرَكُمْ ١١﴾

_Ma’ana: “Kuma yana saukar wa a gareku daga sama ruwa domin ya tsarkake ku da shi”. (Anfal:11)._

_NA BIYU:_ Ruwa mai tsarki, shi ne wanda ya gauraya a kalar sa ko a dandanon sa, ko kamshin sa da duk abun da ba najasa ba, kuma shi ne ruwa mai tsarki akaran-kansa, sai dai shi baya gusar da hadasi, domin gaurayar da ya yi na siffa daga cikin siffofin sa.

_NA UKU:_ Ruwa mai najasa, shi ne wanda ya gauraye da najasa kadan ko mai yawa.

-Ana iya tsarkake ruwa mai najasa ta hanyar cire najasar da ta gauraya da shi, ko zuba ruwa a ciki domin gusar da ruwa mai najasa.

-Idan mutum musulmi ya yi kokwanto game da ruwa, mai najasa ne ko mai tsarki ne, to zai yi gini akan yakini ne, kuma shi ne asalin abun da ya tabbata na tsarkin ruwa.

-Idan wani abu ya yi kama da abun da ya halatta ayi tsarki da shi da wanda bai halatta ba, to sai a bar shi, sai ayi taimama.

-Idan tufafi ya yi kama da mai najasa ko abun da ya haramta, sai ayi gini akan yakini, sai mutum ya yi Sallah guda daya da shi.

Mu Hadu a Darasi Na Gaba In Allah Ya Kaimu.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "KARATUN LITTAFIN FIQHU NA 001"

Post a Comment