Ameen Da Ameena Part 65 To 95 - Hausa Novels - RealityLoaded


 Zaman sh'irunne ya ish'eta, tanason tayi magana amma tana gudun kar yamata wulak'anci yayi banza, itakuma babu abinda ta tsana sama da wulakanci, sh'iyasa ma ta gudurce aranta bazatayi masa magana ba har sai lokacin da yaga dama yayi mata maganar.


Wak'arsa kawai yakeji ko a jikinsa, amma fa so yake yayi yakaita ya dawo saboda akwai abinda zaijeyi yanzun,

so yake tagaya masa inda zai kaita bawai alallai sai yabud'i baki yayi mata magana ba.

Lokaci d'aya yaja tsaki"Mtswwww"

yayi sh'iru bece uffan ba, ita kuwa Ameenah sai ta juya fuskarta gefe tana ta zumb'urar baki ganin har nine 9 ta kusa, ita batason Mama tayi mata fad'a ne sh'iyasa.

Ameen ne ya k'ara jan tsaki ana biyu, tare da cewar"Ke dallah tash'i ki fitarmin daga mota tunda bakisan inda zaa kaiki ba" Kinwani yi sh'iru sai kace mutuniyar kirki, nanko a shaid'ananci inajin sh'aid'anma ya fiki iyawa".

Daurewa tayi, tayi magana kamar zata fash'e da kuka tace cikin inda- inda.

  "Ni........ai baka.....tam..bayen inda...zaka kaini ba, kawai jinayi kayi parking basai in tunanin wani abun zakayi gunba".

  "to tash'i ki fita kinemi keke napep _D'an sahu_ kihau inyaso sai sh'ima kimasa sh'irun karki fad'a masa inda zai kaiki kigani in be je yasayar da kanki ba".

"G/k'aya ne"

"G/k'ayan ma nan da nan kusa kusa mtsww iyayin banza kawai". ya fad'a yana wani harare - harare.

Motar ya figa, dasuka sh'igo tadinga nuna masa hanya har suka.

bud'e motar tayi ta fita, tabar masa kayan daya d'ora mata a cinya akan kujerar data tash'i,

  bayadda zaiyi ya d'auko ledar da bag d'in aransa kawai dan dai Mamy ce tace ayi amma wallahi da bata isa ya kahota ba, ballantana har yawani sh'iga gidansu"mtsww" ya k'ara jan tsaki a karo na uku.

Bayan ta fita ta sh'iga gida tasanarwa da Mama zaa zo gaish'eta tace to.

"Bismillah ka sh'igo mana"

lums'he idonsa yay sannan ya d'ora k'afarsa cikin gidan,

wayarsa tafara ruri, ya d'auko ya duba ganin My only Mum yasa sh'i saurin d'agawa"Hello Assalamu alaikum"

Mamy"

daga ciki wayar kuwa Mamy ce tace"ka kaita gidan?,

"Aaa yanzu zamu sh'iga dai."

Tace"ok ka d'an bawa Mamanta wanii abun mana,"toh Mamy"

yace tana kash'e wayar.

Domin a rayuwarsa yana girmama duk wani abu dazata sash'i, bata tab'a sash'i abu yak'iyi koda ace kuwa bayaso, yasan bazata sash'i abinda ba dai-dai ba.

Ciki suka sh'iga a parlour ya tadda inda Mama take, kai a k'asa yagaish'eta kamar kuwa yasan surikarsa ce.

Bayan sun gaisa yayi mata sallama tare da ajiye mata y'an d'ari -d'ari bandir uku,

da ky'ar Mama ta karb'a, tayi masa godiya sosai sannan ya fita.

Dayafito a ransa yake cewa"A haka kamar masu tarbiyya hmmm amma y'arsu agun rawa kamar jiki ya karye. Yawani yatsina fuska tare da sh'iga motarsa.

[08:37, 8/28/2016] Foulani Cerdiya: Har zaija motar kuma sai yaji kamar tsayuuwar mutum a gefensa dan haka ya fito ya duba, turus yayi ganin ta tafito d'auke da jug na ruwa.

kallonta yayi da mamaki yace"yadai??

kw'arjini yayi mata sh'iyasa batason ganin tayi masa kallo cikin ido.

"Aa dama Mama tace bakash'a ruwa ba zaka tafi sh'ine na biyoka dash'i.

"Ok nagode ya fad'a yana ciro jarkar ruwa daga cikin motarsa, "ina dash'i in zansh'a basai kin kahomin ba ? right?,

ya fad'ayana wani d'age gira dan haka sai anjima"

yaja motarsa yabar gurin,

wani malolon bak'in ciki ne ya cikata ganin yamai da'ita like statue, tafi minti uku agurin kafin daga baya taja matattun k'afafunta wanda da kyar suka iya d'aukarta tayi cikin gida, amma kafin tash'iga tasamu tad'an zubar da ruwan, dan kar Mama tasan besh'aba domin bazata ji dad'i ba.



BAYAN SATI BIYU.

Lokacin da zaa tsaida magana yayi, gash'i suna so acikin dangin babanta wani yazo domin ayi maganar dash'i, kowanne akaje gidansa sai ya nuna ai kawai su hak'ura, wani in sunje masa da maganar yakance a week d'in zebar k'asar haka dai har sukaje gidan wani kawun baban Ameenah, to sh'i dayake bawani me kud'ine sosai ba, sai ya yadda, amma da wajewar bazai yimusu kayan d'aki ba.

Sukuma sun yadda saboda dai ayi abu cikin mutunci yafi.



BAYAN WATA D'AYA.

Antsaida bikin *Ameena da Ameen* nanda wata uku masu zuwa.

Awata ranar alhamis da yamma Mamy tazo gida itada Haleema, aka dunga sh'igo musu da buhuhhunan sh'inkafa da macaroni da taliya su maggi gish'iri, doya dadai sauran tarkace wanda Abba ne yasa akaho musu, anannema Mamy take sanar dasu karsu bawa kansu wahala akan kayan d'aki d'annesu yace subarsh'i, sh'i zai musu komi,

Godiya sosai sukayi, saboda sunji dad'i domin suna cikin zullumin kayan d'akin dama.

  Kai kuyi hak'uri nagaji da typing wlh

Masoyana ina sonku aduk inda kuke kuma Foulani na amsar gausuwarku, Samee tawa Sameen Munay ina jin sak'on gaisuwarki sosai kuma ina amsawa, Allah yabar k'auna.



~Maman triplet~

[10/24, 7:08 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [19:06, 8/30/2016] "Yar Fara: *AMEENA DA AMEEN*

©Foulani Cerdiya

®NWA

67~68




BAYAN WATA BIYU.

Lokacin biki yagaba to, ankaho lefe nagani na fad'a, duk wanda yazo yaganin kayan saiya yaba domin kyawunsu kuma kana gani kasan Naira tash'a kuka.

Dan da Mamy da Haleema ne takanas sukaje dubai suka had'o mata kayan lefen sannan da furnitures dazaasa a d'akin.

Me gyaran jiki takanas Mama ta d'auko mata daga sakkoto, tazo tana mata gyara, ko giftawa zatayi tawaje sai kinji k'amsh'i, haka ko zama tayi na d'an lokaci a wajen in ta tash'i, sai ta bar maka tsarabar k'amsh'i.

A wata ranar alkhamis ana ya saura sati d'aya bikin Mamy ta sauko daga stairs, tayi d'akin Haleema dash'igarta tace"Haleema ko zakije gidansu Ameenah ki kai mata wannan, turarene me ky'au wanda na sayo mata a dubai.

"Aa Mamy kingafa Yah ameen betab'a zuwa gidan nasu ba tun bayan zuwan dayaje kaita, kawai yanzu kice yaje yakai mata,

"ok bari insa a kirash'i.

"Mamy gani"

Yah ameen ya fad'a yana tsugunnawa.

   "dama canai kaje gidansu Ameenah kakai mata wannan".

Mamy ta fad'a tana mik'amasa ledar.

Wani fad'uwar gaba yaji, yarasa meyasa indai zaa ambaci sunan Ameenah sai yaji gabansa ya fad'i.....

"Ungo mana son"

"ok" ya fad'a yana karb'a.

Part d'insa yanufa yaje ya ajiye jakar a kan bed d'insh'i yash'iga d'aki, yayi wanka ya fito ya zauna a parlour yakunna Tv yana kallon tash'ar larabawa.

Wayarsh'i ce tafara ringing yana dubawa yaga k'aninsa Habeeb ne me biyemasa wanda yake karatu a egypt, d'agawa yayi ya kara a kunnensa

"Hello"

"Hello ang"...

Bek'arasa fad'ar abinda zaice ba ya katsesh'i

"Dallah karka cikan kunne malam" Ameen ya fad'a da y'ar tsawa.

"Kai Yah ameen wallahi kasauya hali, nifa inkayimin nayi hak'uri ita kuma fa?,"

" itawa?" Ameen ya tambayesh'i.

"Amarya mana," Habeeb ya bash'i amsa.

Nakusa dawowa fa Yah, i think on friday zandawo saboda I can't wait to see........Bye bye Yah .

Habeeb ya katse wayar.

Ai sai Yah ameen ya sh'iga tunanin maganar k'aninnasa Habeeb, " Yah mu in kayi mana mun hak'ura.....itafa wa?.....Amarya....

can't wai to see.........What??

"Mmtswww ya doka tsaki tare da jaho d'an fruit d'in gabansa yasomaci yana ta tunanin abubuwa da yawa.

Sai da dare yayi bayan anyi sallar maghriba sannan yafita yayo wanka ya sh'irya cikin wata sh'adda dakakkiya tayi masa ky'au, am mata d'inkin boda.

[19:07, 8/30/2016] "Yar Fara: Hula ya kafa abunsa, ya fesh'e jikinsa da turare me d'an karan k'amsh'i sannan ya fito.

Direct parking space ya nufa yad'auki motarsa har ya kunna ta ya tuna aiken da Mamy tayi masa "Mtsww yaja tsaki, sannan ya kash'e motar ya koma ya d'auko ledar, aransa yana mitar kamar sh'i wai zaa aikesh'i gurin k'anwarsa? yanzu inda zaice bazai jeba Mamy tayi fush'i, itakuma y'ar sa ido Haleema ta zuga"Mtsww ya k'ara jan tsakin, adai dainan ya hau motarsh'i yayi gidansu Ameenah.

Kodayaje layin bakowa kuma babu yaron da zai aika, kawai sai yayi zamansa cikin motar, giftawar yaro yagani kamar ya huce, da sauri ya fito yana magana "Hi boy"

"Hello" yaron ya amsa masa tare da mik'o masa hannu suyi musabiha, mamaki ne ya cika Ameen yaro k'arami kamar wannan yasan yayi musabuha da d'an uwansa musulmi lallai.

"Yadai Yaya naji kayi sh'iru?" D'an yaron ya tambayesh'i cikin siririyar muryarsa.

  Murmush'i Ameen yayi najin dad'in ganin yaro k'arami me tarbiyya haka yakeson sh'ima ace yana da y'ay'a masu tarbiyya da hankali sh'iyasa yakeson yasamu y'ar mutunci da tarbiyya domin rayuwar y'ayansu ta inganta.

"Dama aikenka zanyi nan gidan," Ameen ya fad'a yana nuna masa gidan.

Dariya yaron yayi sannan yace"Ok gidanmu ne ai menene?, da mamaki Ameen yace

"Gidanku?"

"Lah eh mana"

yaron ya bash'i amsa. Hmmm

  "Karb'i wannan ka kaima yayarka kace Mamy tace a kaho mata"

Ameen ya fad'a yana mik'o masa ledar .

Karb'a yayi sannan yace"Sunana Asleem"

kaifa?,

"Ameenullah" Ameen ya bash'i amsa fuska asake.

Sh'iga gidan Asleem yayi yabata tare da gayamata yadda sukayi, tash'i tayi da sauri tayo waje dai dai zai sh'iga mota ta k'araso.

  Magana tafara cikin sark'ewar murya tace"Ka....cema..Mammyn. Nagode"

  Kallonta kawai yake yadda tayi wani haske gash'i jikinta sai wani sh'ek'in kyau yake, ga wani sihirtaccen k'amsh'i daya bugi hancinsa, k'amsh'in me sanyi sanyi, me dad'i, yakasa tantance wannan wami irin k'amsh'ine.

   Basarwa yayi yakalleta yawani yatsina hanci yace" Nid'an aikenki ne?,. "dan ita ta aiken kema cemiki akai kin isa ki aiken?............

Kuyi hak'urin rash'in typing wlh mun fara hidimar bikin sister ta.Shiyasa zaku dinga jina sh'iru.



~Maman triplet~

[10/24, 7:08 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [08:34, 9/1/2016] Foulani Cerdiya: *AMEENA DA AMEEN*

        _BY_

FOULANI CERDIYA

®NWA

69~70



Ameen yacigaba da magana da cewar"Koma wane ya gayyatoki nan gurin,? oho.

Ya kad'a kansa ya sh'ige motarsa yabarta kamar statue.

Itadai tana ganin ikon Allah, yanzu ace a haka za'ayi rayuwa?

Mijin tanefa idan Allah yanufa, tunda baa d'aura auren ba.

Amma yake mata haka. Gash'ita kuma kasa cemasa uffan take, saboda sh'e like the way dayake accting, yana matuk'ar burgeta sosai sh'iyasa sai dai tasaki baki, tana kallonsa.

Murmush'i kawai tayi a lokacin dayaja motarsa yayi gaba.

Gida ta sh'iga, taga turarene guda uku aciki kamfanin

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Ameen Da Ameena Part 65 To 95 - Hausa Novels - RealityLoaded"

Post a Comment