Kula da Lafiya: Amfanin Yayan Habbatussauda'a Ga Lafiya
Sunday, November 13, 2022
Add Comment
Habbatussuda kamar yadda akafi saninshi a tsakanin musulmai da suka saba da fadanshi wanda ya kasance suna ne na larabci, an fara amfani dashi da kuma sanin dacewarsa tun kimanin karni na goma sha biyar da suka gabata kuma an bayyana shi a matsayin magani ga dukkan cututtuka illa tsufa da mutuwa. Anyi amfani da wannan iri mai ban mamaki tsawon shekaru don warkar da cututtuka daban daban, ana iya fitar da mansa ne daga yayan wato irin, haka kuma ana amfani da man a wajen manshafawa don inganta yanayin fata da gashi.
Amfani da kwayar habbatussauda ko mansa a kai a kai na iya taimakawa wajen hana cigaba da yaduwar kwayoyin cuta na hanji,ana kuma amfani dashi wajen hanawa da kuma magance wasu nauika na cutar kansa, yana taimakawa wajen habaka ayyukan kwayoyin cuta wanda shi ne mafi yawan nau’I jiki, haka zalika habbatussauda na kara samar da kwayar halittar kasusuwa na garkuwan jiki,yana kuma kiyaye kwayoyin al’ada daga lahanin kwayoyoyin cuta. Ana iya watsa yayan habbatussauda ko a abinci ko kuma yayinda ake dafawa ko kuma a kwaba man a salads.
Haka zalika habbatussauda na maganin ciwon suga, yawaita shan man habbatussauda yana taimakawa wajen daidaita matakin sukarin jinni.
Haka zalika Habbatussauda na iya rage yawan kamuwa da cutar farfadiya a cikin mutane, musamman yara wadanda aka gano da cutar farfadiya.
Man habbatussauda na iya taimakawa mutane masu fama da asma, masu karatu suna da’awar cewa habba yafi karfin magani na yau da kullum domin kuwa yana rage tasirin asma a hanyoyin iska,yana taimakawa mutane su yaki mummunan cutar asma da tari.
Kwayoyin habbatussauda maganine mai tasiri wajen kawar da sanyi da mura haka zalika yana sauke lamuran narkewa Kaman jin tashin zuciya ko ciwon ciki.
Haka zalika man habbatussauda na taimakawa wajen rage zubewar gashi, yana taimakawa wajen karfafa kwayoyin gashi wanda ke age asarar gashi.
Zaka iya diban kwayoyin habba ka hada da tafarnuwa kana sha a shayi.
Related Posts
Subscribe Our Newsletter
0 Comments to "Kula da Lafiya: Amfanin Yayan Habbatussauda'a Ga Lafiya"
Post a Comment