MAGANIN MATSALAR FADUWAR GABA

TAMBAYA TAMBAYA TAMBAYA


Assalamu alaikum. Malam sannu da kokarin ilmantar damu da kake awannan zaure mai albarka mun gode Allah ya saka maka da mafificin alkhairi nan duniya da kuma gobe kiyama.

Malam don Allah ina so ataimaka min da wasu addu'o'i ko magani. malam ina fama da matsalar faduwar gaba ako da yaushe.. Malam har makarantar kwana aka kaini wlh malam sbd wannan faduwar gaba na kasa zama a makarantar.
Da zarar na dauko litattafaina da nufin karatu gabana ya rika faduwa sosai. Sai na fada agidanmu aka fiddani..
Sannan kuma bayan haka ni artist ne idan aka dauke ni domin yin wani rubutu ko kuma symbol gabana ya rika faduwa har rubutun ko kuma symbol din ya lalace. malam dan Allah Ataimaka min nagode wslm.

         AMSA
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Dukkan godiya ta tabbbata ga Allah, Tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah, da iyalansa da Sahabbansa da dukkan salihan Bayin Allah.
Akwai wasu nau'in Shaitanun Aljanu wadanda idan sun shafi mutum sukan sanya masa fargaba da kuma Waswasi acikin dukkan ibadarsa da Mu'amalolinsa. Musamman ma Muhimman abubuwa.

Amma ga wasu hanyoyin da zaka bi domin samun lafiya:-

1. Kulawa da Sallolin farillah acikin jam'i.
2. Yawaita karatun Alqur'ani kullum.
3. Yawaita zikirin Allah akoda yaushe.
4. Kulawa da zikirin safe da yamma da kuma na kwanciyar barci.

Duk lokacin da kaji alamar irin wannan matsalar zata taso maka, ka karanta wannan addu'ar :

" ﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﻜَﻠِﻤَﺎﺕِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟﺘَّﺎﻣَّﺎﺕِ ﻣِﻦْ ﻏَﻀَﺒِﻪ ﻭَﻋِﻘَﺎﺑِﻪِ، ﻭَﺷَﺮِّ ﻋِﺒَﺎﺩِﻩِ، ﻭَﻣِﻦْ ﻫَﻤَﺰَﺍﺕِ ﺍﻟﺸَّﻴَﺎﻃِﻴﻦِ ﻭَﺃَﻥْ ﻳَﺤْﻀُﺮُﻭﻥِ*

"A'udhu bi kalimaatil Laahit Tammaati Min Ghadhabihi wa 'Iqaabihi wa Min sharri 'Ibaadihi wa min Hamazaatish Shayaateen Wa an Yahdhurooni".

MA'ANA: ina neman Tsari da albarkar Kalmomin Allah cikakku, daga Fushinsa da Ukubarsa, kuma daga sharrin bayinsa, kuma daga sharrin Fizge-Fizgen Shaitanu, (Kuma ina neman tsarinka Ya Allah) Kar su halarto inda nake".

Zaka karanta wannan addu'ar sau uku kullum safe da yamma. Da kuma duk lokacin da kaji alamar fargaba ko faduwar gabar. Sannan kuma ka yawaita LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BIL-LAAH.

Bayan Haka kaje ayi maka Rukyah. In sha Allahu lafiya zata samu gareka da yardar Allah.
Allah ya sawwake. Allah shi baka lafiya.

WALLAHU A'ALAM.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "MAGANIN MATSALAR FADUWAR GABA "

Post a Comment