ADDU'A DA MAGANIN SAURIN FUSHI




TAMBAYA TAMBAYA TAMBAYA


Assalamu Alaikum Warahmatallahi Wabarkatahu

Malam Hamisu Allah Ubangiji ya saka maka da alkhairi da gudunmawarka a wannan group Amin

Tambaya ta a nan shine Ni na kasance mai saurin fushi idan akayi min ba daidai ba, wacce addu'a zanyi ko wacce hanya zan bi don rage yawan fushi?

                           AMSA
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Fushi fisgane daka fisgar shaidan, sanadiyar fushi mutum yana fadawa cikin munanan abubuwa, da masifu wanda bawanda yasan iyakarsu sai Allah, saboda haka shari'a tazo dabayani yalwatacce wajan ambaton wanan dabi'a abar zargi, anruwaito acikin sunnar manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam magani na wannan cuta da kuma hanyoyin kubuta daka tasirantuwa da ita, daka ciki.

1- Neman tsarin Allah daka shaidan, ( A UZU BILLAHI MINASH SHAIDAN):

Hadisi ya inganta wanda bukhari da muslim suka ruwaito, wasu mutane suna jayayyah awajan Annabi sallallahu Alaihi wasallam, daya daka cikinsu fuskarsa tayi murtik tai jah saboda fushi jijiyoyin wuyansa sun tattaso, sai Annabi sallallahu Alai wasallam yace: ( Nasan kalmar da inya fadeta abunda yakeji na fushin zaitafi daka gareshi, dazaice " a uzu billahi minash shaidan", dafushin yatafi daka gareshi.
Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace: Idan dayanku yai fushi yace: ( Ina neman tsarin Allah daka shaidan ) fushinsa zai kwanta. sahihul jami'ul sageer ( 695).

2- Yin shiru yayinda kai fushi
: manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Idan dayanku yayi fushi yayi shiru) Imamu Ahmad yaruwaici wannan hadisin acikin musnad nasa ( 1/ 329) da sahihul jami'i ( 693, 4027.
saboda galibi mai fushi yakan fita daka hayyacinsa yayi furuci da kalmomin dawani lokacin ma kafircine, ko tsinuwa, koya furta kalmar saki wanda zai ruguza gidansa, ko zagi dacin mutunci, wanda zai janyo masa kiyayyar wasu mutane, adunkule yin shiru shine maganin fadawa cikin wadannan ababe.

3- Zama: manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace:
idan dayanku yayi fushi yana tsaye toya zauna, idan fushin yatafi shikenan inbai tafi ba, to mutum yakwanta.
fa'idar wannan umarni na Annabi shine lokacinda kake tsaye kana da cikakkiyar damar dazaka iya yiwa wani illah ko mugun aiki, idan ka zauna kuma wannan damar baka da ita sosai, yayinda ka kwanta damar ta kubce maka gaba daya. yanda bazaka aikata abunda zakai nadamar saba.

4- Kiyaye wasiyyar manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam, daka Abu huraira Yardar Allah takara tabbata agareshi yace: wani yazo wajan manzan Allah yace: ya manzan Allah kaimun wasiyyah saiyace: kada kai fushi harsau uku yana mai-maita masa, bukhari fat hul baari ( 10/456).
Awata ruyawar sai mutumin yayi tunani lokacinda Annabi yafadi Abunda yafada, sai naga fushi yatattare sharri baki dayansa, Musnadu Imamu Ahmad ( 5/ 373).

5- Karkayi fushi sakamakonka aljannah, hadisine ingantacce sahihul jami'i ( 7374):

Tuno abunda Allah yatanadarwa masu hakuri na ni'imoni da girman matsayi zai taimaka wajan nisantar abubuwan dasuke kawo fushi din dakuma danne zuciya yayin dayazo.
Wallahu A'lamu.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﻋﻠﻢ ﻟﻨﺎ ﺇﻻ ﻣﺎ ﻋﻠﻤﺘﻨﺎ ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﺤﻜﻴﻢ

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "ADDU'A DA MAGANIN SAURIN FUSHI"

Post a Comment