Hukuncin Barin Farce (Kumba)
Saturday, November 11, 2023
Add Comment
Assalamu alaikum Malam shin ya halatta barin farce?
𝐀𝐌𝐒𝐀
Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh
Yanke farce yana cikin sunnoni na dabi'a da'aka dabi'antar da mutum akansu saboda faɗin
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ( Abubuwa biyar suna daga dabi'ar da'aka halicci mutum dasu, kaciya, da aske gashin gaba, da rage gashin baki ga ( maza) da yanke farata, da tsige gashin hammata) Bukhari da Muslim.
Ya Tabbata awasu hadisai sunnonin fidra guda goma ne daga ciki akwai yanke farce, yazo ahadisin Anas dan malik Allah yakara yarda dashi yace: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya iyakance mana lokacin yanke gashin baki da yanke farce da aske gashin gaba da tsige gashin hammata kada mu barshi yahaura kwana arba'in bamu kawar dasu ba). Ahmd, Bukhari, Nisa'i
Wanda bai yanke farcensa ba ya saɓawa sunnah, hikimar hakan shine tsafta da kuma fitar da abunda ke karkashinsu na dauda da datti, da dauke kamanceceniya da wanda basa hakan cikin kafirai, da kuma kama da dabbobi, Fatawa lajnatul da'imah ( 5/173).
Mafiya yawan mata ayau sun faɗa cikin kamanceceniya da dabobi da kafirai wajan tara farce, sannan sai su rinashi da jan farce baki ko jah, wannan yakai makura wajan muni, da abun kyama acikin zukata, ga duk wani mai hankali mai dabi'a kubutacciya.
Haka yana daka cikin mummunar dabi'a wajan wasu mutane saisu bar wani sashi nafarcen yayi tsawo bakyan gani, dukkan waɗannan sun saɓawa sunnah da kuma fidira ta ɗan adam, saboda haka bashi halatta tara farce gabaɗayansa ko barin wani daka cikin faratan domin kamace dakafirai kama dakafirai kuma haramunne acikin dukkan komai na al'adunsu.
Muna rokon Allah kubuta daka waɗannan munanan halaye, Allah yashiryar damu hanyar madai-daiciya.
Related Posts
Subscribe Our Newsletter
0 Comments to "Hukuncin Barin Farce (Kumba) "
Post a Comment