Ameen Da Ameena Hausa Novel Part 1 To 64 - Realityloaded

 


1-10

*AZAMANIN MAN,AKW'AI MASU KI'DAN DAMUKE D'AUKOWA LOKACIN BIKUNKUNANMU SUNA NE BIKI NE, DA DAI MAKAMANTANSU AKW'AI WAD'ANSU MASU KI'DA D RAWA A GURIN BIKI WAD'ANDA SUN KASANCE YARAN DJ N*
*SOMETIMES ZAKIGA MASU D'J SUNZO DA Y'AN MATA GURIN BIKI SUNAMUSU RAWA* *TA BURGEWA DAN KAWAI SU BASU ABIN HANNUNSU, DAGANAN WASU* *ZAKIGA SUN LALACE TARBIYYARSU TA TAB'ARB'ARE,* *HARMA KIGA BAASAMU DAMAR YIN AURE BA.*
*SABODA WANNAN SANA'A DA WASU Y'AN MATAN SUKA D'ORAWA KANSU, DUK KUWA INDA* *KIKAGA MUTUM NA RAWA GABAN MAZA DA MATA* *KINSAN BABU* *KUNYA A GURIN.*
   *ALLAH SA* *MUDACE AMEEN*

Tafiya nake akan
titi kamar yadda nasaba dan in samo muku labarai, aikuwa kw'atsam naci karo da wata nuts'atstsiyar yarinya cikin k'atoton hijab, daga gani makaranta zata ko kuma ta taso? oho nidai Foulani haka nayi ta mamaki, da jaka a rataye a kafad'arta, tafiya take cikin kw'anciyar hankali a natse.
Madaidaiciya ce, daga kallon danayi mata daga baya, binta na cigaba dayi a baya har naga ta tsayar da me keke napep(adaidaita sahu)
banji inda tace masa xataje ba amma naga ta sh'iga, nima da saurina na ts'ayar dawani nace yabimin bayan waccen matar,
adai-dai gidan wani party naga ta sauka, tabiya d'an keke napep kud'insa ta fito,.
mamaki na zaro ido ganin da hijab ne ajikinta yanzu kuma naganta tafito da mayafi, hmm
dad'inta d'aya kayan jikinta ba matsatstsu bane, kuma mayafin bawani babba bane can, tayi rolling dash'i ta sh'ige.
Kid'ane ke tash'i sosai,.
Ta sh'iga ga matanan a zazzaune akan fararen kujeru,
daga can kuma gamasu kid'a nan, yana tash'i
wajen naga ta nufa,
tayiwa wani magana yazoko har inda take,
  ahankali naji tana masa magana yace  to ta sh'iga ta ajiye jakarta ,
aka ware kid'a tafito tafara dancing kamar baajikinta ba,
aikuwa nan danan mutanen dake wajen suka dinga zuwa sunayi mata lik'i, kud'i kuwa se zubar mata ake saboda yadda ta iya rawar sosai,
6:00 ta kalli agogon hannunta,
jakarta ta d'auko, wannan wanda naga tayiwa maganar sh'idi'nne ya biyota a baya,
   a d'an wani waje suka samu suka tsaya,
kud'i ya ciro a aljihunsa ya mik'o mata yace"ga kudin ladar rawarki,
"Ok nagode ta karba tana hucewa atake kuma wasu zafafan hawaye suka ziraro mata,
a ranta tace"Allah kazama gatana ka fitardani daga rayuwar danake,.
Tash'are hawayenta ta ts'aida wani me keke napep ya kaita har k'ofar wani madaidaicin gida,
ta fito da hijab d'in d'azu ajikinta t bash'i kud'i ta sh'ige gida da saurinta.
Da sallama ta sh'iga gidan, wata matace a zaune tana tsefewa wata yarinya kai,
"Mama sannu da gida
"yawwa y'ar kirki har kindawo
"eh wlh Haleema ma tana gaish'eki
gash'i tace ma abaki
ta ciro kud'i ajakarta ta mik'a mata
  Mama ta karb'a tana irgawa, ta lissafa dubu biyar ne cif
"duk ita tabaki wannan d'in Ameenah?
"eh ita tabani ta fad'a tana sh'igewa d'aki.
Yarinyar da akewa tsifarce ta juyo ta kalli Mama tace"Mama kinga sai ki biyamana kud'in makaranta nida Asleem
"Insha Allahu Tasleem mugodewa Allah da yakaho mana kud'in nan dan dakinga gobe baki da zuwa makaranta.
A d'aki kuwa Ameenah ce zaune tana ninke kayanta tasa asif
ta fito dawata doguwar riga ta saka sannan tafita tayo alwala tayi sallah,
bayan ta idar ta d'aga hannunta tana rok'on Allah ya kaho musu mafita a rayuwarsu,
Allah ya fitar da'ita daga cikin halin data jefa kanta na zuwa gidan biki tayi rawa dan kawai abata kud'i tasamu na taimakawa Mamanta domin..........


~HOPE DA DAD'I INAJIRAN RA'AYINKU~
Maman triplet ce
[10/24, 7:06 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEENU*
   ®NWA
©FOULANI CERDIYYA
10~40

Maraicin da suke ciki ya jaho musu haka, ga mats'anancin son Ameen datakeyi, wanda besan tanayi ba hasalima gani take kamar ya tsaneta, saboda k'azamar rayuwar data d'aukarwa kanta dan ta taimaki mahaifiyarta, Amma tana tunanin wannan zuwan datayi gidan party Insha Allah sh'ine zuwanta na 'karsh'e, badan komai ba sai dan ta  samu soyayyar Ameen kamar yadda Haleema tash'a gaya mata takance da ita"Friendy kin d'auki rayuwa me wahala gash'i kin fad'a son Yah Ameen kina tunanin zai soki a haka ne?
sh'awarata a gareki itace ki hak'ura da wannan yawace-yawacen gidan rawar.
Hawaye ya k'ara zubowa  a Fuskar Haleema wanda hakan yayi dai-dai da sh'igowar Tasleem k'aninta da gudu,
yana zuwa ya fad'a jikinta yace"Aunty Sayyada sunan da suke kiranta dash'i a dalilin kasancewar sunan Mama ne akasa mata, sh'iyasa k'annen nata ke kiranta da Sayyada
Wacece Ameenah(Sayyada))?
Amina muhd Abdullahi sh'ine asalin sunanta y'ace wurin
Alhaji Muhd
yakasance d'a d'aya agurin iyayensa wato Alhaji Abdullahi
d'an kasuwane na hak'ik'a inda yake ordern kaya daga waje yana turowa nigeria domin a sayar
Alhamdulillah sana'ar ta karfesh'i dan nan danan yafara gini, ana haka ne Allah ya had'ash'i da Ameenah wato Mama
Mama ta kasance itama y'ace d'aya a gurin iyayenta bayanta basu k'ara haihuwa ba
Alhaji Muhd ya auri Mamanta har dai bayan auren nasu basu haihuba sai da suka d'an jima dayin Aure
lokaci d'aya Allah ya basu haihuwar yarinya mace wato Ameenah
Ameenah ta taso cikin kulawa daso da k'auna har makw'aftansu ma suna son Ameenah sakamakon yarinyar ky'akyky'awa ce
data fara hankali kuma ta kasance nutsatstsiya ce bata da hayaniya bata da girman kai duk kuwa dacewar Alokacin Mahaifin nata me kud'i ne
Bayan y'an sh'ekaru sunja har ansa Ameenah a makaranta ta boko da islamiyya,
tunda suna primary take da wata k'awa me suna Haleemah'Haleema irin yaran nanne masu kok'ari a makaranta kamar dai Ameenah itama babu ruwanta hakan ce tasa suka saba da'ita kuma itace k'awarta har yanzu, Mama ta haifi yara biyu bayan Ameenah
wato Asleem da Tasleem sune ma suka samata suna Sayyada wato Aunty Sayyada
Mahaifinta ya rasu; bayan yayi jinya inda tacinye masa rabin dukiyar daya tara.Watarana da daddare bayan mutuwar Mahaifinsu Ameenah b'arayi suka sh'igo musu suka musu satar kaf abinda suke dash'i, kuma Alokacin ne Ameenah ta gama secondary school
daganan rayuwa ta sauya musu,babban gidan dasuke cikima suka sayar dash'i dan asamu na cin abinci da biyawa yara makaranta, Ameenah tana zuwa islamiyyar dake bayan gidansu wacce itama Haleemah tana zuwa,.
Bayan anyi hakane ta yanke sh'awar dayaya xata ringa taimakawa Mamanta?
hardai wata rana taje bikin wata frnd d'inta taga wata tana rawa a gidan biki kuma ta fuskanci kud'i aka biyata sh'inefa taje tayiwa masu Dj mgana
su kuma ganin ky'akyky'awa yasa sukayi saurin amince mata data dinga zuwa tana musu rawar sudinga biyanta,
kullum ran asabar da lahadi zakiga Ameenah baa zuwa Islamiyya, Halema takan tambayeta" wai ke Friendy ina kike zuwa ran weekend ina monitoring d'inki saboda nash'a zuwa idan antash'i Mama tacemin kinje makaranta while ni bakizo ba, ki gayamin ina kike zuwa? kuka ne ya kufcewa Ameenah adalilin yaudarar Mamanta datakeyi,
"Kiyi hak'uri Friendy wallahi ba inda nake zuwa,
but.......sai kuma tayi sh'iru tarasa abin cewa"but what? tell me bekamata ki boyemin ba' nan dai Ameenah ta gaya mata abinda yake faruwa na zuwa gidan party tayi rawa a biyata.
  Salati Haleema tasa tace"talauci haukane Friendy? kinyi Kuskure, yanzu ni bazaki iya gayamin mats'alarki na?
sh'in ni bazan iya taimakonki ba,?
nandai Haleema tayi Fush'i da k'awartata hardai tayi mata alk'awarin baxata k'ara xuwa guri Party tayi rawa ba.
anan nema Haleema take sanar mata bikin Yah Ameen saura sati d'aya,"yaush'e ya dawo ne Friendy, "ya dad'e da daho wa anyi anyi ya futo da mata yak'i to akw'ai wata y'ar k'awar Mumy shine aka had'asu duk da yace sh'i baya sonta ita kuma tana sonsa sosai,
"Allah ya kaimu mush'a biki Ameenah ta fad'a tana faraa a fuskarta.
Yau takama Friday taje wajen Dj khaleed tana tambayarsa koda wani party a week d'in nan?
"Yes akw'ai wani zafaffen Party dazamuje wannan partyn nasan zamu samu kud'i,
murmush'i tayi tace"ok yaush'ene
"gobe ne "aina ne? ya fad'a mata sunan gurin
"Allah ya kaimu ta fad'a tana juyawa tace "sai nazo
a hanya tunani take ga bikin Yayan Haleema ya zatayi?
data tuna jiya basu wani ci abinci ba yasa tace afili" sorry Friendy
bayan ta koma gidane, Haleema tazo, lokacin Ameenah na d'aki tana gogewa su Asleem unifoam d'in school d'insu, Tasleem ce ta sh'igo tace"Aunty sayyada ga Aunty Haleema,
da gudu ta fito tana fadin"oyoyo my Friendy, murmush'i mamatayi tace"saketa karki karyata,
tayi dariya ta sh'ige d'aki itama ta bita,
  Haleema ta dubi Ameenah tace"ke gobe zaa fara bikin Yah Ameen, dummmm gaban Ameenah ya fad'i saboda bazata samu damar attending ba dalilin gobe zataje rawa kuma...... "ke ina miki magana,
karb'i wannan, ash'obenki
"woww yayi ky'au but Friendy ya....Haleema ta rufe mata baki tace"noh karkice komi kedai kizo,
"ok alot of thanks Friendy
harara ta galla mata tace"ke kika san thanks d'in ai
suka tuntsire da dariya.
Ameenah ce taketa sh'irin fita tayi kw'alliya harta gaji, tada yayin bikinta na less golden, dan daga wajan rawarta zata zarce gurin bikin su Haleema,
duk da Haleeman tace ta ts'aya zata biyo ta d'aukets su tafi, itakuwa bata kaho komai ba ta yanke sh'awarar d'aukar wayar Mamanta ta tafi da ita in yaso in tafifo daga can saita kirata ta gaya mata wajen.
"Cab Aminah ta fad'a ganin wajen partyn dabata  ma tab'a zuwansa ba, gaskiya gurinfa yayi ky'au anyi decoration na k'ayatuwa tunda take zuwa party bata taba zuwa irin wannan ba,
Mutane sai sh'igowa suke suma y'an gayu,
sai dai tunda Ameenah ta sh'igo gurin gabanta keta fad'uwa ganin irin kayan dake jikinta, sh'ine na ragowar mutanen dake sh'igowa,
*"Tash'in hankali*Ameenah ta fad'a a fili,
bayan an zazzauna akan chairs dake wurin amarya da ango suka sh'igo
aka bisu da tafi masu camera sai d'aukar photo suke,
itadai jikinta yanata rawa gabanta nata fad'uwa,
bayan anyi wasu jawabe -jawabe,
aka ware Dj kid'a ya fara tash'i, babu yadda zatayi dolenta ta sh'iga tayi musu abinsu ,amma badan haka ba da bazata sh'igaba, tambayarta d'aya wai sh'in bikin nan nasu waye?
itafa jikinta yana bata kodai bikinsu Haleema ne?
"Nash'iga uku idan sh'ine
  hawa tayi kan stage tafara rawa normal, rawarta ta burge kowa da kowa, masu  waya suka fara vedio,
Ango Ameen sani muhd yaji gaba d'aya yarinyar ta burgesh'i,
besan ta akai ya tsinci kansa da kallonta ba har ya tash'i yayi mata lik'i
"woww handsome Ameenah ta fad'a a ranta dan yayi mata mugun ky'au inama mijintane, gaskiya ta burges'hi sai dai daya tuna rash'in kunya ce da fitsara yasata yin rawar sai yaji ta bash'i haushi
zuwa yayi yasanarwa da masu magana cewar a daina d'aukar vedio,
aiko aka sanar gab'a d'aya suka koma suna kallo amma sundena d'aukar vedion,
"wannan familynmu ce? ko kuma yaya?
tambayar dayakewa kansa kenan,
kamar daga sama ta hango Haleema tana tahowa, Innalillshi wa'inna ilaihir rajiun,
na sh'iga uku!!!
can wata dabara ta fad'o mata ta sauko tana tafiya a hankali sh'ikuwa angon kallonta kawai yake taburgesh'i kuma ta bash'i haushi tana isa inda take ta rungumeta tace" nama rugaki zuwa,
"Friendy kinyi bala'in ky'au "kema kinyi ky'au,
Sh'ine kika taho, to aina kika san gurin?
"uh....ai..hm kinga, tun kafin ta k'arasa fad'a Haleema tagane rawa tazoyi,
  tsaki tayi ta jaho hannunta suka hau kan stage d'in, ta rik'o hannunta ,suka fara rawa tare itada Haleeman, nanfa aja k'ara tagi raf rafrafraf, tasowa yayi ya musu lik'i yace ya kamata ku fita daga wajen rawar nan, yana fad'a ya kalli Ameenah data kulash'i ya harareta,
a dai*dai lokacin k'arfe sh'idata nuna, aiko tayi dariya suka fita itada Haleema,
   Me dj ne ya taso yabiyota ya bata wasu uban kud'ad'e wanda bansan adadinsu ba, amma fa sunkai kudan dubu tal..bara dai inyi sh'iru kar ace na zuk'ata.
Bayansu Ameena sun dawo daga dinner ne tazo kw'anciya bacci but baccin yak'i zuwa idonta , ta juya nan ta juya can tarasa mekeyi mata dad'i
abu d'ayane ya ts'aya mata arai hararar da yayan Haleema yayi mata,
murmush'i tasaki ita kad'ai, "dama zaka aureni *Ameenah da Ameen* what a mach!!!
sai kuma ta tuna auren sa akeyi take taji fad'uwar gaba, tayaya ma za'ai ya aureta?
yana da wannan matar? "ze aureki mana Ameenah kina fa da ky'au idan sh'i yakewa
  Ameenah fara ce amma ba k'al ba, doguwace dai-dai misali, k'irjinta cike yake fam, gata da hips , tana fa shape me 8 tana da fuska me ky'au wacce take d'auke da dara-daran idanuwa d'auke da zara-zaran bakin gash'in ido(eyelashes), gata  dawani irin hanci me ky'au bawai dan yana da tsini ba, hancinta yayi ky'au a fuskarta, bakinta me ky'au d'an k'arami, gash'im giratta mara yawa y'ar siririya, gata maabociyar kw'alliya, idan tad'au makeup ke sekace khareena kapoor,
idan tayi murmush'i dimples d'inta su lots'a, idan tana tafiya kese ki rantse tana sani take girgiza jikinta, amma ba haka bane, hasalima itabata so takeyi, woww takoina tayi.
*Ameenah*
Bayan sati d'aya, Ameenah na zaune ita kad'ai, tayi uban tagumi, ga lokacin islamiyya yayi, amma tana zaune tana sana'ar tata wato tunani,
tarasa meyasa idan ta rufe idonta take ganin Ameen a ciki? bata san soba amma dase tace kosh'i ne? hawaye suka gangaro kan fuskarta, dai*dai nan Asleem ya sh'igo ,"Aunty me akayi miki?
"bakomi Asleem i just need your prayer.......
  sallama tajiyo wacce kobaa gaya mataba tasan Friendy c,
  sh'igowa tayi da sallamarta, Ameenah ta goge fuskarta ta amsa,
tun kafin Haleema ta zauna tace"mekuma akayi miki kike kuka?
seko ta fad'a jikinta cikin kuka tace"i don't know Friendy tunani yamin yawa just pray for me pls,
fad'amin abinda ke damunki? da ky'ar ta gaya mata komi,
tana gama fad'a ta ky'al ky'ale da dariya tace" You feel in love, brother na , don't worry Friendy muyita addu'a dan kinsan sh'aamin Yah Ameen sai sh'i, but dole yasoki ai.
Maman triplet
*Wanene *Ameen*?? sh'i irin mutanen nanne miskilai ga zafin kai, da nuna isa gash'i bayada  yawan magana, sh'i i irin chocolate colour d'in nanne fatarsh'i very smooth
yana da ts'ayi da zati, Fuskarsh'i d'auke take da dara-daran  idanuwa
hancinsa dogo, gawani saje daya kewaye Fuskarsa"Wow Ameen kenan wanda  y'an mata suketa kaho masa hari Amma basa burgesh'i saboda sh'i har yanzu bega macen datayi masa ba dan sh'i ya kasance yana son mace me ilimin addini bawai dole sena boko ba, sannan yana son Mace nutsatssiya mai hankali da kamun kai wacce tasan mutuncin kanta.
Yayi aure da matarsa khadeeja wacce ta kasance zab'in mumynsh'ice, dan sh'i bama yasonta , ko gado ne yadda sun had'aba,
Khadeeja irin y'ayan masu kudin nanne wadanda basusan sunemu abu su rasa ba.
Sedai abinda take buri da Ameen ya kw'anta da'ita gash'i sh'ikuma yak'i dan yace jikinsa bame arha bane, yana nan yayiwa macen datasan kanta , wacce bakowani karene yake kallon surarta ba
ita ba irin macen dayake burin samu bace,  yanason nutsatstsiya wacce zata bawa y'ayansh'i tarbiyya me ky'au ba ky'alekyalen abinda wasu mazan suke dubawa ba, yanason mace me dauriya  bame raki ba
wacce bazata iya d'aukarsh'i a sh'infid'a ba, dan sh'i d'in  ingarmane,   totally khadeeja batayi masa ba,
ita sedai ky'au a fuska amma k'irjin a sh'afe yake, har garama hips d'innata ba laifi.

~Maman triplet~
[10/24, 7:06 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN*
©FOULANI CERDIYA
®NWA
40~42

Abinda yafisa
Ameena taji gaba d'aya rawar da takeyi tafita daga ranta sh'ine,
Watarana taje gidan party, kamar yadda tasaba takansa kayanda ba matseta sukayi ba,
tayi kw'alliya a fuskarta tunda dama itad'in sarkin kw'alliyace,
bayan tasa hijab d'in makaranta tafito,
Mama ta tarar a ts'akar gidan, tayi mata sallama tace mata ta tafi islamiyya,
anan Mama tayi mata nasiha da cewa"Ameenah ki kula da kanki, kar kiyadda ki biyewa rud'in rayuwa kiyi abinda duk inda kikaje zaa samiki albarka ayabeki,kar kiyi abinda zaayi Allah wadai dake".
"To Mama nayi miki alk'awarin kare mutunci na,insha Allah daganan tasa k'afa ta fice, tana zuwa titi ta tari me keke napep(Adai-daita sahu)
ya kaita gidan party,
ta fito cikin tafiya ta k'asaita wacce dama asalin Ameenah a haka take, jikinta yakan d'anyi rawa kamar tana girgiza sh'i while ba haka bane.
Gurin partyn ya had'u  ga maza da matanan, sunata dancing anata rawar sh'oki.
Tak'arasa gurin y'an uwanta y'an D'j tamusu magana suka gaisa,
alokacin me magana yayi umarni da kowa yakoma gurinsa ya zauna zasu fara nasu programm d'in, wato Mace da namiji su fito suyi rawa kamar yadda akasaba a wajen D'j.
Aka fito aka fara rawa, nanfa Ameenah ta fara zuba rawa iri iri ta 'iya, mutane akafiffito akayi mata lik'i .
Ana cikin rawarne tasamu y'ar uwarta wato y'ar rawa itama ta sh'igo  cikin fili, "Woww rawar nan sun iyata kugunsu kamar ya cire gash'i komi a tare sukeyi, ke kyace zama sukayi aka koyamusu amma ina babu d'aya ballantana k'anwar biyu.
Agogone ya nuna kansa 6:00 tafito,
tana fitowa aka mik'o mata kud'inta ta karb'a, _SHOKI AH SHOKI_
wak'ar data daki kunnenta, amma ta fuske tasakud'inta ajaka, wanda adai-dai lokacin ne y'anmata da samarin gurin suka tash'i suna taya iblis iblish'sh'i
a kw'aso a kuma rufe ido d'aya,
*WA'IYAZUBILLAH*
_SHOKI AH_ tana kaiwa nan tafad'i ak'asa *TUIM*
kallo sai yadawo kanta, da gudu mutanen gun sukayo gurin a dai-dai nan tace ga garinku ne .
Wata gigitacciyar k'ara taji a lokacin da akace bata numfash'i,
"Ni  Ameenatu baiwar Allah, ubangiji na tuba kayafeni"
Ameenah ta fad'a tare da saurin ficewa daga hall d'in,
tana ta jimamin yanzu mofy ta rasu?
agurin rawa,?
yanzu taje tace da Allah me?
"Yasalam
har Ameenah ta dawo gida da jimamin abun aranta,
sukuku tazama, Mama ta tambayeta ko lafiya?
tace da ita bakomi
Abinci ma ta kasa ci, balle wani abu ruwa,
itadai istigfari take yi da salloli tana rok'on Allah ya yafemata.
*Y'AN UWA MUGANE WANI ABU, ITA RAWA BA'ACE HARAM BACE, AMMAADINGA SANIN A'INDA ZAAYI,*
*SABODA YANZU* *DUK BIKUN KUNAN DAMUKEYI ZAKIGA* *MATA DA MAZA AN HAD'U ANCUD'E* *ANA RAWA A GURI D'AYA*.
*IDAN DA'ACE A IYA* *GURINE  WANDA BA MAZA IYA ZALLAN* *MATANE TO BABU WANI ABU,*
*AMMA IDAN KAJI ANCE ZAAYI BIKI BABU D'J*
*SAI KIJI ANA* *FAD'IN AI BIKIN WANCE LAMI BA* *DAD'I WAI SABODA*
*BAAYI D'J BA HMMMMM*
*ESPECIALLY IDAN AKASA* _SHOKI_
*WLH MATA DA MAZANE ZAKIGA SUN CURE GURI D'AYA ANA KW'ASO SHOKI*

      *ALLAH SA MUDACE*
~Maman Triplet~ Ga ha'intar Mama datekeyi, tunda bata san aina take samo kud'inba tana dai cemata Haleema ce ta bata, da farko Mama fad'a tayi mata akan me Haleema zata na bata kud'i ita gaskiya bataso
at the end dai wataran Mamynsu Haleema tazo ta kahomata kayan provision tayi mata godiya, to tundaga lokacin ne Maman take yarda da hakan.
Haleema takan rufawa Ameenah asiri saboda sau tari tash'a zuwa taga Ameenah bata nan koda kuwa Mama tace ai Ameenan tatafi sai kiji tace" May be sab'ani mukeyi Mama bari inje makarantar"
koda wasa bata tab'a nuna mata bata zuwa makaranta ba.
Kuma koda Maman  tayi mata godiya akan wani abu da Ameenan ta kaho tace inji Mamynsu Haleema bata tab'a nuna mata ba itance ta bayar ba,

dan wani lokacin idan taje ta dawo kud'in da'aka bata takan sayo kayan Abinci da kayan dazaa nema ta kaho mata azuwan Mamyn Haleema ce ta bayar.
Koda tafad'a mata cewar Ameen takeso Haleema tayi murna da farin ciki sai dai ta k'ara gargad'inta da dole ne ta sauya halinta, ta dawo Ameenarta data sauya kanta da wannan banzar rayuwar.
Ta zuwa gidan biki yin rawa,
hirarsu ta k'arshe da Haleema ranar dataje gidan party ta dawo tayi sallah tana addu'ar Allah ya kaho musu d'auki cikin rayuwarsu,
Sallama tayi ta sh'igo suka gaisa da Mama, ananne Maman take mata godiyar kud'in data bayar akaho mata.
Murmush'i kawai tayi tace"ai Mama yiwa kaine,"
"kish'iga tana ciki"
"to Mama Haleema ta fad'a tana sh'igewa cikin d'akin.
tunani take ita kad'ai ta tuno hararar da Ameen yayi mata a farkon ganinta dash'i face to face,
dan bata tab'a ganinsa a fili ba sai a hoto,
afili ma yafi ky'au.......
"sannunki juliet sarkin soyayya kinwani kish'ingid'e da alama tunanin romieo n kike ko?"
Haleema ta fad'a cike da zolaya
"Eh yason ranki y'ar sa eyes?"
"Wai hmmm wai wayaga kuma fa ko kundace wallahi,"
But Friendy kinsan Yah  Ameen d'an uwana ne,
dole tilas ki gy'ara halinki ki dena zuwa gidan rawar nan dan Allah badanni  ba"
"kina tunanin wani zai aureki ne idan yasan cewar kina zuwa gidan biki yin rawa?
sam-sam baze yuhuba, bawai akan Yah Ameen ba, kinsan kowanne uba burinsa samawa y'ayansa uwa tagari?
why not bazaki zama haka ba?,
ko kinaso nan gaba y'ayanki su taso ace Uwarsu kafin tayi rawa y'ar D'j ce?
bafa haka kike ba Friendy
You have to change your bad behaviours, pls
  You know har baiko akaiwa Benazir an kusa bikin but da saurayin yaji tana yimawa y'an D'j rawa ya fasa aurenta?
pls nd pls Friendy ki sauya.
Tana kaiwa nan tayi sh'iru
"Insha Allah bazan k'ara koda rawa a gidan biki ba har indai ba iya y'an uwana mata ne zalla ba."
"Yawwa k'awas har naji dad'i, nagode da k'arba'ar sh'awarata da kikayi"
"nice da godiya ai"Ameenah ta fad'a da faraa a fuskarta.
"ina romieo na??"
"Hahhhhhh yana gurin matarsa daga aure wata d'aya hartafara kaho k'ara, sh'i yace mafa ya gaji da ita, dan halinta be masa ba.
Itama kuma Mamy ta gaji da kaho k'arar da Aunty khadeejan ke kahowa,.
danfa rash'in kunya wai ta iya cewa Mamy wai betab'a kw'anciyar aure da ita ba
Mamy taji haush'i ranar nan wallahi.
Haleema ta k'arasa maganar da bacin rai
"Allah yasa mudace Ameen, Ameena ta fad'a tana mik'ewa ta kahowa K'awarta ta abin sh'a.

~Maman triplet~
[10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN*
©FOULANI CERDIYA
®NWA
43~45

Ranar asabar da misalin k'arfe hud'u ta sh'irya zataje gidansu Haleema kw'alliya tayi tak'in k'arawa tasaka riga da skirt na atamfa ta d'auko hijabinta har k'asa tasaka ta fito tayiwa Mama sallama tafita.
Ak'ofar sh'iga falon gidan taci k'aro dash'i gabanta ne ya yanke ya fad'i ta dafe k'irjinta, "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun "
ta fad'a tare da cigaba da tafiya cikin  nuts'uwa,
sanye yake cikin skyblue d'in sh'adda taji aiki, ga hular sa _zanna bukar_ ya kafa itama me rats'i rats'in skyblue,
sanye yake da agogo a jikin hannunsa, ga gash'in nan ya kw'anta da alama ansh'afa masa man k'ara fito da ky'an gash'i na maza.
Tana zuwa daf dash'i tad'an russuna tace cikin rawar murya"in.........ina..yini...?
d'ago da idonsa yayi ya mata wani kallon sh'ek'ek'e ya amsa da "klau"
  hanjin cikintane ya kad'a rugugugu da wannan kallon dayayi mata sonsa ya k'ara dira a cikin birnin zuciyarta ta sh'ige ciki. Haka ta lallab'a ta sh'iga ciki kamar wacce kw'ai ya fash'ewa a ciki.
bakowa a falon dan haka ta nufi d'akin Friendy, tana kw'ance tana sana'ar tata wato karanta _Hausa novel_
Hadeeza Deeza Dije take karantawa littafin ;U Fadeela Foulani Cerdiya nd hauwa'u damary.
D'ala mata duka tayi, firgigit Haleema tasaki wayar hannunta ta kw'alla k'ara saboda ta tsorata ainun. [8:32AM, 8/12/2016] Foulani Cerdiya: Hatta nima Foulani da nike rubutoo muku labarin sai da wayar hannuna ta subuce saboda razana.
"Gaskiya badan kebace da nace Allah ya......kafin ta k'arasa Ameena tasa hannu ta tosh'e mata baki
"sorry Baby herly kinsh'iga shauki ko"Allah dai ya sh'iryamin ke Friendy,
"Lah yanzu Yah Ameen yafita
"Ai nagansh'i sarkin miskilanci kinga wani kallo dayamin?
"hmmm ki dad'a hak'uri"
"wai ina Mamyne?banjita ba
"tana sama tash'i muje 
"ok
"kinsan Yah Ameen fa girki yasani in masa wai baze iya cin abincin aunty khadeeja,
bayan sungaisa ne suka fito, suka nufi kitchen suka fara had'a masa delicious food
Haleema sai zolayarta take wai dayake girkin Yah ameen ne ta dage sai fama take.
Dai-dai sh'ida da rabi suka gama suka fito da ga kitchen sun gama girkin,
suna fitowa falo sukaci karo dash'i zaune akan kujerar dake zagaye da falon,
"cab lallai wannan 'yan gayu ne sh'i, yanzu daga fitarsa daga gidan har ya sauya kaya, yanzun sanye yake cikin k'ananun kaya sun amsh'i jikinsa,
gash'in nan ataje luf-luf.
"Sannu da hutawa Yah ameen," Ameenah da Haleema suka fad'a suna had'a baki
  "sannu"
kawai yace ya cigaba da kallon Tv.
Toh bayan Ameenah tayi sallar maghrba ne ta fito zata tafi gida, Mamy na falon ita da Yah ameen suna magana banaisan me suke cewa ba,
ganin fitowar Ameenah yasa Mamy ta tash'i tana fad'in
" badai tafiya zakiyi ba ko?
"wallahi Mamy tafiya zanyi,
"toh tsaya ina zuwa
Mamy ta fad'a tana hayewa bene,
sh'iko gwanin kallo d'aya yayi mata ya 'dauki remote yakamo tash'ar _Music plus_ga d'an kwando na kayan marmari yana d'auka yanaci.
sa
kin baki tayi tana kallonsa yadda yake taunarma abin burgewa ne, wayyo jitakeyi kamar tafad'a jikinsa ta rungumesh'i ta fad'a masa cewar tana sonsa sedai hakan bazata yuhuba, dan ita d'in mecece me aji.
Mamy ce ta sakko da leda a hannunta ta bata,
"aa Mamy kibarsh'i dan Allah
"noh bazamuyi haka ba karb'i a matsayin y'a kike gurina.
Hannu tasa biyu ta russuna ta karb'a tace"Nagode Mamy
daga nan tayi mata sallama ta fice.
"Dama yarinyar nan tana da nutsuwa?
"gata dai a haka kamar ta Allah
"nan kuwa ko dujal nan yaganta ya ky'ale saboda rawa. "Mtswww yayi ts'aki a fili dan sh'i a ganinsa Mace ta sh'iga filin biki tayi rawa gurinda maza da matan suka gauraya gani yake kamar rash'in _class ne_
"lafiyarka kuwa Son naji kana tsaki?
sosa gash'in kansa yayi yace"Noh bakomi Mamy.
"Yawwa Mamy wai wannan y'ar waye?(Littafin granny khairat up"
"Kawar Haleema ce tana da kirki sosai ga nutsuwa da hankali wallahi yarinyar ba ruwanta.
"Hmmmmm
ya d'an k'ara girman idonsa alamar mamaki , yarinyar dabata kunya ina wani hankali.

~Maman triplet~
[10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN*
©FOULANI CERDIYA
®NWA
45~50

BAYAN SATI D'AYA
Anyi hutun islamiyya ya kama yanzu su Ameenah suna gida hutu.
Idan Haleema batazo gidansu Ameenah ba to ita Ameenah zataje, suna sh'irya planing ta yadda zaa jaho hankalinsa, but duk ta inda suka bu'lllo sai suga da akw'ai matsala.
Yau takama Alhamis, Haleemace tazo gidansu Ameenah,
lokacinma Mama tana kitchen tana dafa musu abinci,
ita kuma Ameenah tana d'aki tana yiwa Asleem da Tasleem home work d'in da'aka basu a school.
Haleema ta sh'igo ta sallamarta bayaj sun gaisa da Mama ta ciro kud'i a jaka ta bata tace inji Mamyn su,
godiya Mama tayi mata sosai, Naso in gano muku ko nawane amma Mama ta soke a zaninta lol, ganin Ameenah na aiki yasa ta fita tsakar gida tana taya Mama aikin datake.
Bayan duk sungama aikinne Mama tazubo musu abinci dama _dambu_ sukayi ita dama masoyiyar sace sukacinye abinci bayan sungama Haleema ta kalli Ameenah tace"Friendy kinsan dame nace"
"aa ta fad'a tare da girgiza kanta
"kizo muje gidan Yah ameen pls kirakani bawai dan wani abu ba kema ai kya gansh'i ko? Haleema ta fad'a tana d'aga mata gira,
ba musu tace"to bari na sanarwa Mama,
  bayan ta fad'a matane tace "sai kun dawo ku kula da kanku banda kula kowa a hanya _pls_
"Insha Allah ta fad'a tana sh'igewa d'aki tasanja kaya sanan suka tafi.
Tash'in hankali wanda baasa masa rana suna zuwa gidan kafin su sh'iga parlour sukajiyo ihun kukan mutum, kuma daga ji na mace ne sai dai in ka k'ara sa kunnenka sai kaji kamar harda namiji ma ke kukan,
kallon-kallo sukayi ts'akanin Ameenah da Haleema
"Friendy meke faruwa ne? anya kuwa mush'iga?, bamu sani ba ko wasu ne suka sh'iga gidan"
Ameenah ta fad'a tana narai-narai da ido.
"Ah no kizo mu sh'iga, karkiji tsoro bakomai"
Haleema taja hannunta suka sh'iga ciki , zazzaro ido sukayi  waje ganin Aunty khadeeja(Matar Ameen) ce ke kukan Yah Ameen sai jibgart yakeyi ita da wani, ya had'a kansu ya gwara har jini ke fitowa ta bakinta,
   "
_kije ki tafi ki tash'i ki barmin gidana ki tafi gidanku  ki cigaba da neman maza da bin mazan da kika fara yanzu kin matsa kince bana kw'anciya dake, bakisan rufa miki asiri nayi ba ,mahaifita kinje kin gayaa mata bana saduwa dake duk meyayi zafi, ko duk saboda masifarki sai kin kahomin kw'arto cikin gidana kitash'i nace na sakeki, ya jahota ya danganata da waje inda damatuni kwarton nata ya d'ibi kafafuwansa ya arci na kare sai dai ya kw'afsa dan tuni y'an sanda suka kama s'hi suka fice dash'i station_
"Friendy dan Allah ki taho mutafi kinga kar ya had'a daku jibifa yadda yake kallonmu," kus-kus ta fad'i mata
"aa tsaya dai"
"muts'aya muyi me?
juyowa yayi yaga mutane abayansa,
huci yake kamr tsohon zaki yakallesu yace" ku kumafa?" Haleemace tayi kok'arin bash'i amsa da cewa
"uhm dam...ma cemukayi bari muzo mugaisa da Aunty khadeeja kuma.......kuma......mhmm
"kuma me?
"go out munafukan banza.
Aiko da gudu -gudu sukayo waje, fitsarine kawai ya ragewa Ameenah bata saki na, amma ta tsorata ainun.
Gidansu Haleema suka huce, suna zuwa suka baje a parlour suna numfash'i Haleema dariya kawai takeyi, tana tuna yadda suka tsorata.
Jiyo dariya yasa Mamy ta sauko" ku kuma lafiya dan Allah?
"Mamy daga gidan Yah ameen muke wallahi ya zane Aunty khadeeja, ita dawani,
"duka fa kikace Haleema?,
"eh kamar dai kwarto ya kama a gidan,
"Innalillahi wainnailaihirrajiun!!!
Abinda yarinyar tayi kenan?,
"yamace yasaketa,
sukadai kwashe kaf labarin suka gaya mata,.
Baa dade'ba sukajiyo sh'igowar mota koba'a fadamusu ba sunsan shi ne ai da y'ar rige-rige suka tsere d'aga tayi kitchen d'aya tayi d'aki.
Bayan yash'igo ne kuma yama Mamy bayani tayi masa fad'an akanme zedaki y'ar mutane?
ai haku'ri akeyi ta lallab'ash'i nan da nan ya dawo normal,
"ni zan k'ara nema maka wata macen,
"what Mamy Ameen ya fad'a yana zare ido,
inda Ameenah dake kitchen  itama d'in ta zaro ido tare da cewar"what na sh'iga uku,
kqmar zeyi kuka ya marai-raice ya sakko k'asa ya tsugunna a gabanta, ya had'a hannu biyu yana rok'onta.
"Mamy pls ki barni wallahi Mamy mata basada gaskiya, ki barni in zab'o wata me mutunci da hankali y'ar tarbiyya, Mamy ba cikin y'ayan k'awayenki ba wad'anda aka sangarta ba, ba irin wad'anda basu san ilimin addininmu ba sai na yahudu, Mamy masu qualities danakeso , ba wad'anda basa cikin tsarina ba, Mamy wacce zata haifamin y'an biyu , ta basu tarbiyya me ky'au ba ky'ale- kyalen zamani ba Mamy,
hawaye ne ya zub'owa da Ameenah yadda Ameen yayi ya matuk'ar bata tausayi,
"Son duk wad'annan qualities d'in yarinyar ta had'a, sedai tunda bakaso anfasa sh'ikenan ko?
"ohhh sweet kill me ooooo that's why i proud of you Mammy, "da akw'ai abinci Mamy?
"eh jeka kitchen da akw'ai"
da murnarsa ya nufi kitchen dan samun abinda zesa a cikinsa,  turus yayi ganin mutum a tsugunne yana hawaye, ...."keee..... Ameen ya kirata.

~Maman triplet~‍‍
[10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [1:56PM, 8/15/2016] Foulani Cerdiya: *AMEENA DA AMEEN*
©FOULANI CERDIYA
®NWA
50~52

In'ina Ameenah ta fara, dacewa"Uhm bakomi.......bah....abinda nake......yi"
"tambayarki me kike yi?
"munafuka dallah fice kibani guri,"
ai tun kafin yakai k'arsh'e ta kw'asa da gudu ita wallahi kw'arjini yake mata tarasa meyasa,?
  _hm ai dole yayi miki kw'arjini dan Ameen ko baki sansh'i ba kika gansh'i sai kinji sh'ayin yi masa wani abu_.
"Au kece kika sh'iga kitchen dama?
Mamy ta tambayeta
"eh Mamy nice wallahi, tana fad'a ta sh'ige d'akin Haleema,
dariya Haleema keta ky'akyatawa saboda taga k'awartata ta sh'igo a kid'ime kuma duk abinda suka tattauna tsakanin Mamy da Yah ameen duk taji.
"Friendy romeo ne ya tsoratar da juliet d'insa"?
"kefa muguwa ce wa billahillazi ko? ina tausayin randa kema zaki fad'a tarkon son wani"....
Tv suka kunna suka kamo tash'ar _Mazzika_ kid'a yafara tash'i, mussaman da Ameenah taji wak'ar datayi matane, ta d'au remote ta k'ara volume,
ta tash'i ta cire hijab d'in jikinta, ganin kid'an zai wuceta yasa ta tash'i ta fara rausayawa tana karkad'a k'irji k'ugu da kai rawar larabawa kenan wani lokacin. Haleema kuma itace me temaka mata da tafi"woww woo wannan rawar sai ranar bikinku keda Yah Amee......
     "Kuwai bakuji ana muku magana kun mayar mana da gida sai kace gidan biki?, kun cikamana kunne da wak'a?... duk wannan maganar Ameen ne ke yinta but kawayen nawa basusan yanayi ba saboda sh'auk'in dasuka sh'iga.
Bugo k'ofar da akayine da k'arfi yasa suka zuba ido ga bakin k'ofar dan ganin wake sh'igowa,
"Inye????? lallai tayi muku ky'au, inata muku magana kun karad'e gida da kid'a hmmmm."
Ameen ya fad'a cikin masifa,
mutuwar tsaye Haleema tayi, tace
"yi...hak'uri..bamuji bane,
"kedai wannan, ya nuna Ameena da yatsa yacigaba da cewa"in baki wasa ba akan wannan Raye-rayen da kike sai kinje kin kw'asowa kanki jinnu.
  "Ke kuma Haleema, itama ya kira sunanta "kici gaba da biyemata kuna zama d'aya banzaye ku fito  kumin girki kuma kala biyar nakeso, a cikin minti 30 juice kala uku, aciki zan zab'i  d'aya inci, ragowar kunyi asarar hannunku da lokacin da zaku b'ata, wannan shi ne punishing naku"
kuma a ciki idan d'aya bemin ba sai kunsake.
Cab Kallon kallo akayi tsakanin Ameena da Haleema,
"munsh'iga uku suka had'a baki su ka fad'i a tare.
"ai Allah gida zantafi Friendy,
"kut....ke kinma isa? wallahi baki isaba.
[5:32PM, 8/15/2016] Foulani Cerdiya: "Bake ce kika jaho mana ba?
"to ke in bandake da abunki tayaya zakice zaki tafi ki barni ni kad'ai? sai kace me hannun Gizo-gizo?, Haleema tayi maganar cikin tsiwa.
"to mu computer ne dazamuyi masa girki kala biyar? me zamu dafa masa? ga juice har kala uku, dan Allah ya zamuyi,
Ameenah ta fada da tunanin nemo mafita,
zaman bori sukayi suka zub'e a k'asa, Ameenah tayi facing Haleemah kowacce tayi uban tagumi suna tunanin mafita,
lokaci d'aya suka had'a baki da cewar"Menene Mafita? me zamu girka masa acikin 30minute????.
  Jin sun tafi tunani ne yasa  nima Foulani na d'anyi plugging wayata kafinsu dawo daga tunanin.
*Toh Masu karatu, ko zaku iya basu sh'awarar abinda zasu girka a cikin 30minutes? inkece ko in kune mezaku girka masa,? me zakiyi??.*

      Maman triplet

[10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN*
©FOULANI CERDIYA
®NWA
52~54

"Ki tash'i muje muyi masa white rice nd spaghetti with soup, sai muyi masa pineapple nd coconut juice , sai mu bash'i hak'uri Ameenah ce me wannan maganar
"Cab duk acikin 30minute d'in?"ni aganina mu soya masa indomie da k'wai sai kuyi masa fara mu zuba mai, sai muyi masa jallop d'inta kinga hud'u kenan, sannan sai muyi masa d'an wake ko? Ameenah ta fad'a
"sai muyi masa pineapple juice dana watermeloon, mu markad'eta musa madara da sugar sai musa a fridge dan yayi sanyi, biyu ko?
"wai ke Haleema bazaki bada taki idea ba kinwani kafeni da ido kina kallo?,
"Dalla ni gyalen......
Bazaku fito ba? kunacin time d'inku fa,
Yah ameen ne yayi maganar yana daga falo, atare suka fito suna zuwa suka zub'e akan centre carpet dake d'akin,
"Dan Allah Yah Ameen kayi hak'uri bazamu sake ba, ko Haleema ko Ameenah? suka fad'a a tare suna kallon juna, dariya suka so bash'i amma sai ya k'ara had'e rai yace"oya maza-maza kutash'i kumin abinda nasaku ko yanzu ranku ya ba'ci,
Mamy tana sama dan haka batasan wainar da ake toyawa tasauko da niyyar d'aukar abu a k'asan ta tarar da y'ara a durk'ush'e duna bada hak'uri.
"Meyake faruwa kuma?
ka dawo gidan zaka takurawa yara, da ita k'anwar taka da wacce ba k'anwartaka ba,? sedai dan mutunci da zumunci ta zama k'anwarka, amma ai bahaka ake rayuwa ba mesuka maka?
"Mamy ina musu magana sunmin banza, sun ware kid'a, suna rawa"
"to sh'ine me?
"punishment na basu,
"name?
"sumin girki,
"au girkin ne ku kuma bazaku iyaba kuka zube kuna bash'i hak'uri?
da kun tash'i kunyi da kun huta ai ko?
Mami ta fad'a tana kallonsu sunyi wani zuru zuru da ido.
Haleema ce me kok'arin cewa"Kal...kala biyarfa yace muyi masa kuma wai da juice kala uku a cikin 30minute .
Hangame baki Mamy tai tana kallonsa tace"kala biyar kuma duk zaka cinye a cikinka?
"zasuyi maka amma fa kaima duk sai ka cinyesh'i ku tash'i kuje babban kitchen ku d'ora masa duk abinda kuka so.
Damurnarsu suka tash'i , Halema tayi niyyar dariya amma tak'i saboda tsaro.
Suna zuwa daya ta d'ora ruwan zafi, tayi masa tea ta juye a plask, d'aya ta soya indomie da k'wai, sannan suka yi masa d'anwake, suka yi masa white sphagetti nd soup,
bayan sh'i suka fara juice kamar yadda Ameenah ta fad'a haka sukayi, kuma duk yafi k'arfin cikinsa.
D'auke da tire suka sh'igo suka ajemasa kan dining "Food is ready romeo,
Haleema ta fad'a cikin siririyar murya daky'ar ma inyaji abinda tace, tunda be d'auki wani action ba.
Ameenah ce ta kalli Haleemah tace
"Nidai Friendy gida zantafi wallahi,
"driver ne ze kaiki, coz ban yadda adinga kallemin matar yaya baa, eyye Haleema tafad'a tana d'aga mata gira,
duk
a ta da'ala mata tace"ke dallah rabu dani, wannan yayan naki yana wahalar dani ni bazan iya jurar wannan wulak'ancin ba, in mukayi aurenma haka ze dinga sani girki kala goma.
Ta fad'a da fuskar tausayi .
Har gida driver ya kaita, tash'iga da sallamarta, Mama ta amsa mata, Asleem da Tasleem suka rugo da gudu sula rungumeta"We miss you big sis" Missing you more ta musu peck, suma sukayi mata ta sh'ige d'aki.
Mama tana alfahari da y'arta saboda kasancewar bata tab'a jahomata magana ba, gash'i tana taimakawa k'annenta wajen karatunsu,
sai dai tace"Masha Allah.

~Maman triplet~
[10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [8:52AM, 8/19/2016] Foulani Cerdiya: *AMEENA DA AMEEN*
©FOULANI CERDIYA
®NWA
54~55

BAYAN WATA D'AYA.
Yanzu in kaga Ameenah gaba d'aya ta sauya, ko hira ake sedai tayi sh'iru saboda tunanine yake addabarta, kai ko a hanya ta  taho zata iya bigeka ma bata sani ba.
Agida kuwa su Asleem da Tasleem suyi ta damunta da"Ya sayyada wai meyake damunki?
yanzu baki mana tatsuniya, kindena zama kiyi hira da Mama, meyasa? takance tasu
"bakomai Twins d'in Mama.
Mamar matayi tambayar har tagaji, takaita asibiti a duba ko bata da lafiya ne? amma lafiyarta k'alau dan haka da tagaji sai kawai ta kyaleta.
Acan gidansu Ameen kuwa, kullum Mamy zatayi masa  zancen yarinyar nan, seyayi kamar zemata kuka ita kuma tasan had'in dazatayi masa bana sh'arri bane dan ta yadda da tarbiyyar yarinyar da zata bash'in,
Haleema y'ar sa ido, sedai kiji ta lallab'o tace"Mamy wai wacece wannan d'in ne?
kigayamin inji mana.
Haleema tanayin hakan ne dan kar k'awarta ta rasa zab'in ranta, tanaso taji wacece dan tasan hanyar dazata bullowa da abun, but Mamy tak'i gaya mata.
Yau Alkhamis da misalin k'arfe takw'as na dare, Ameena ce zaune ita da Twins d'in Mama, tana k'aramusu karatun Alqur'ani sakamokan an basu hadda a islamiyya.
Yaro ne ya sh'igo da sallama yace"wai ana sallama da Ameenah,
"What??, Me?, Ameena ta fad'a tana nuna kanta da hannunta,
da sauri tace
"kace batanan."
"kace tana zuwa"
Mama fad'aa tana kallonta, kitash'i ki fita, jik'aki zamuyi mush'a koyaya?
sai ayita zuwa gurinki fira amma sai kik'i fita, to yau sai kinfita.
Tash'i tayi taja hijab d'inta Fuuuuu ta fita.
Tana zuwa ta taddash'i tsaye jikin motarsa ash, cikin sh'adda milk, ya kafa hularsa _Zanna bukar_
sai tash'in k'amsh'in turare yake.
Tsayawa tayi k'ik'am bata masa sallama ba.
"Barkanki da fitowa yake gimbiyar mata"
"barkanka" abinda ta iya cemasa kenan ta d'inke bakinta tayi masa sh'iru
"To dafari nidai sunana Haruna ina zaune a garin abuja inda anan nake aikina,
nazo biki nan kano naganki, kuma naji kin burgeni har nayi
sh'aawar mu had'a halak'a ta soyayya fatan zaki karb'a?."
tunani ta tafiyi a gidan biki wajen rawa anan yaganta kuma yace yana sonta? Anya??
katse mata tunanin yayi da cewar"Haba yadai naji kinyi sh’iru ne,? kobanyi miki ba?
"Aa bakomi
hira yadinga yimata sedai ta bish'i da uhm  eh aa.
daga k'arsh'e dayaga ba wata hira kawai yayi mata sallama tare da mik'o mata kud'i tak'i karb'a,
se cayayi ba abinda zakiyi min wanda zesa im nakoma gida in dunga tunaninki?
"mezan maka?
Ameenah ta tambaya,
"Haba baby Meenah ko d'an irin hugging da kissing ai nasamu ko,?
ya fad'a yana k'ok'arin kami hannunta, sauri tayi ta janye tace"ya haka Malam??
"mekake tunani?
ni y'ar iskace? ko kuka me? mtswww to kasanja tsar...."ke dalla saurara kina y'ar rawar D'j dan nazo namace inasonki sh'ine zakimin shauting?
"Kaicona!!! ta fad'a da gudu tayi cikin gida.
[5:11PM, 8/19/2016] Foulani Cerdiya: Kafin ta k'arasa cikin d'akin tasaita kanta dan kar su Mama sugane wani abu.
Koda ta sh'iga bata musu magana ba ta sh'ige d'akinta tayi kw'anci tana tunanin halin
Wash'egari
Mama tana zaune tana yanka salad taji tsayuwar mota a k'ofar gida.
Sallama tayi tayi ta sh'igo "Lah Mamyn Haleema? sannu da zuwa
Mama ta fad'a da mamakin ganinta dan ta dad'e batazo gidan ba.
Ameenah
Dafara'arta tafito tana "oyoyo Mamynmu
Mama ta dafata suka sh'ige d'aki bayan an gaggaisa Mama take cewa"kin d'auke k'afarki daga gidanmu ko Daughter?
"aa wallahi Mama ba haka bane"
"To aini gani nabiyoki "
Ameenah ta sunkuyar da kanta alamar kunya.
ta tash'i ta aiki Asleem ta sayo mata lemo me sanyi ya kahomata, taji yaron ya burgeta sosai.
Bayan tash'ane suka fara hira da Mama ganin haka yasa Ameena ta fita tabar musu d'akin domin bedace tasasu a gaba tana kallo ba.
Bayan tafita ne Mamy ta kalli Mama tace
"dama nazo miki da wata magana ne, kuma inafatan zakiyimin alfarma,
Gaban Mama ya fad'i dajin wannan  abu amma sai tace "menene Mamyn Haleema?
Mama tafara da cewa dama............
Ayya wayata ba charge sorry Fans

[10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [8:05AM, 8/21/2016] Foulani Cerdiya: *AMEENA DA AMEEN*
©FOULANI CERDIYA
®NWA
56~57

"Dan Allah Maman Ameenah kimin alfarma, "
"wace abune wannan Mamyn Haleema? kifad'amin mana, kinfi k'arfin komi a gurina".
"Dama so nake kibani y'arki, so nake ki yadda in had'a *AMEENA DA AMEEN* aure,
ammafa sai in kin amince kin yadda tunda kece mahaifiyarta."
Gumine yake ketowa Maman, dan maganar tazo mata a bazata, coz batayi expecting hakan ba but why?,
tayaya zata had'a y'arta da yaron da taji Haleeman da Ameenan suna cewa yafiye fad'a da miskilanci,
  Mamy ce ta katseta daga tunanin datake tace"Maman Ameena yanaji kinyi sh'iru ne?
ko kin bayar da ita ne?
"Sh'in Ameen yana son Ameenah?
sh'i yace miki ki nemo masa aurenta?
inke kika zab'a masa ya amince?"Mama ta tambayi duka dantaji amsar da Mamyn zata bata.
To itama Mamyn ta tafi tunanin amsar bawa Mama,
"ki kwantar da hankalinki na isa da Ameen , bash'i yace in nemo masa ba, ni na duba dacewar hakan, ina ganin Aurensu zai kaho sauyi a rayuwarsa, ki yadda in had'auren *Ameena da Ameen* pls Maman Ameenah,
Tayaya? babbar mace kamar wannan tazo ta nemi abu agunta ta hanata? matar da take taimakonsu a rayuwa, sai dai abinda ta nema d'inne kamar da wuyar bayarwa, Y'afa?....
"Maman Ameenah in kinga bazaki iyaba sh'ikenan
Mamy ta fad'a cikin fuskar tausayi,
"yaron nan matar dana bash'i a farko bata masa adalci ba, bata juri duk abinda yake mata ba, bata rufa masa asiri akomai ba,
Hankali da nutsuwar Ameenah da tarbiyyarta su suka jani suka saminsh'aawar had'a *Ameena da Ameen* itace dai-dai sh'i". Amma idan kinga bazaki bayar da itaba s'hikenan.
Maganar ta sh'igi Mama sosai kuma taji tausayinsa tunda beyi dacen mata ba.
"sh'ikenan Mamyn Haleema Allah yasa hakane yafi alkhairi.
[8:40AM, 8/21/2016] Foulani Cerdiya: Da sauri Mamy tajuyo cikin farin ciki tace"da gaske? da gaske kin yadda Maman Ameenah?
"eh na yadda mu had'asu, "
"Insha Allah zamuga alkhairi tunda da niyyar hakan mukayi Allah sa albarka acikin auren *Ameena da Ameen*"
"Ameen ya rabb" suka fad'a a tare.
Kowanne da tsantsar farin ciki a zuciyarsa.
Bayan Mamy tafuto zata tafi ne, take cewa Ameenah" yaush'e zaki zo? kink'i gidanmu yanzu,
"aa Mamy ba haka bane zanzo soon"
"Allah yasa.
Daganan sukayi sallama da cewar sai Abbansu Ameen d'in yadawo zasu tsaida magana dan baya gari.

[10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [13:56, 8/23/2016] Foulani Cerdiya: *AMEENA DA AMEEN*
©FOULANI CERDIYA
®NWA
58~59

Bayan fitar Mamy ne Mama tayi kiran Ameenah, take cemata"Ameenah Mamyn Haleema tazomin dawata Magana.Daganan ta kw'ash'e duk yadda sukayi da Mamyn amma bata gayamata cewar da Ameen zaa had'asu ba.
Tunani sosai ta sh'igayi saboda zancen yazo mata a bazata, ita dawani d'an nata Mamy zata had'asu?,
ya zatayi,
ita datake son Ameen yanzu idan bash'i bane fa? idan k'aninsa ne shi'kenan an mata yankan k'auna da abin son zuciyarta, sai dai data tuna hirar Mamyn da Ameen, sai take tunanin to kodai shi'ne? Allah yasa haka to.
D'aki tash'iga jiki asalub'e, ta haye gadonta tafara tunanin yadda za'ai a had'ata aure dawani wanda baya sonta cab jink'iri mak'ari.
"Yah Ameen "Yah Ameen ka tash'i Daddy yadawo yana ta kiranka kazonan sai sh'ar bar bacci kake".
   Haleema ketash'insa, amma saboda jiya ya d'auko Abbansu daga airport kuma cikin dare ne dan Haleeman ma tayi bacci a lokacin, shi'yasa batasan ya dawo ba sai da safe data ganshi' sh'i ne har take tuna masa yataa'shi.
Bargonsa ta janye, ta jaho d'an yatsan k'afarsa "ka tash'i.Tafa'da da k'arfi, tafice da gudu, dan dole ya tash'i ya sh'iga toilet yayi brush,wanka da alwala saboda besamu sallah asuba ba.
Bayan yagama yayi addua sosai sannan ya tash'i, yayi cikin gida.
kodash'igarsa cikin gidan a dining ya taddasu sunfarayin breakfast, sallama yayi sannan ya nemi guri yazauna.
Gaida iyayen nasa yayi,suka amsa ckin sakin fuska, daga nan ya jaho flat d'in abinci yayi serving kansh'i.
Bayan sungama cine Abbansu yayi gy'aran murya, sannan yafara magana kamar haka
"My son! kaga dai be kamata mubarka haka ba, duk ka tsufa sh'ekara tafiya take, kwara ka amfani kurciyarka,
kai yanzu ba yaro bane, kana da y'an uwa k'anne kuma suna koyi da abunda kakeyi ne, inso samune inaso kayi aure, kuma nasa Mahaifiyarka tayi maka zab'i na hak'ik'a, ba irin wancen ba."Inafatan zaka amince da duk wacce aka kaho maka amatsayin mata".
Shi'ru falon yayi, kasancewar kowa yayi tsit yana saurar Abban.
Duk kansu inka kalli fuskokinsu da farinciki, banda Yah Ameen wanda yake ta faman had'a uban gumi dukko da sanyin Ac dake ratsasu. Tunani yake sh'idai yanason matar daxai aura ta kasance dawasu  qualities wanda yake burin samun mace dasu, yanzu idan ba haka take ba yaya zaiyi, wallahi aure ze k'ara.Haka yaketa tunani kafin Abban ya katseshi da cewa"nasan kana da biyayya da hak'uri, kayi hak'uri ka tallafi kowacece insha Allah zakaga Alkhairi."
"toh Abba insha Allah zanmaka biyayya domin farantawa MAHAIFINA zan auri koma wacece"
"Allah yayi maka albarka"Mamy ta fad'a tana faraa.
"Allah yabaku zaman lafiya" Abba ya fad'a. A'inda ba abar Haleema y'ar sa eyes ba sai da tace"Allah yasa ku haifo y'an uku masu kama dani da Abba da Mamy ko?.
Duka aka tuntsire dariya amma banda Yah ameen wanda ya kad'a bujensa yafita.
Abba ne ya kalli Mamy yace"
"Aise akahomin Y'artawa in ganta ko? duk da dai naaganta a photo inason naganta; dan intabbatar da banyiwa d'ana zab'in banza ba,
duk da nasan Haleema bazatayi k'awar da bata kirki ba."
"Abba k'awata kuma?
Haleema ce tayi tambayar tara da k'arawa eyes d'inta girma.
[14:13, 8/23/2016] Foulani Cerdiya: Mamy ce ta tare ta da fad'in "eh k'awarki Ameenah saura ki bari yaji yasan kowace ranki zai ba'....."Wayyo Allah sweet kill me woooo,"Mamy
Haleema tayi gunta da murna ta rungume ta ta k'ara kallon Mamyn tace"Mamy are you serious?
kafin ma Mamy ta bata amsa tayi gun Abba sh'ima ta rik'e masa hannu tace"Abbana da gaske *Ameen da Ameena* kuka had'a?
sh'ima be bata amsa ba  sai murmush'i kawai dayayi ganin y'ar autar Mata na farinciki ,ta mik'e tana tsallen murna" Dole inyi murna da celebration, kunsan daga jin sunan ma Abba couples d'im sun had'u? aiko? kuma sun dace da juna? ko? *Ameenah da Ameen* woww perfect match wayy.... Bata k'arasa Mamy wacce Haleema ta cika mata kunne da ihu tace
"Ke dallla kincika mana kunne dawannan sh'ash'ancin naki, sh'iyasa tunda wuri nak'i gayamata dan nasan sh'irme zatayi mana.
"Aaa Mamyn yara banson fad'a yazakice bazatayi murna ba? barta tayi, yayanta take tayawa murna.
"Autar mata(sunan da Abba yafi kiranta dashi) tash'i kije ki sh'irya kije gidansu y'artawa ki tahomin da ita".
"Yee ok Abbana.Da gudu tafita daga parlon tayi d'akinta, tana mejin dad'in wannan abu burin k'awarta Aminiyarta, Sister ta zai cika.
         
   By; ~Maman triplet~
[10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN*
BY;FOULANI CERDIYA
   ®NWA
62~64

Ameen ne ya juyo yana hararar Haleema yace"
"Mamy ga driver nan a zaune, aikin meyake?".
Haleema ce tayi saurin cafe zancen ta k'irkiro k'arya tace.
"Uhmm, ai sh'i driver aikensa za'ayi," Mamy koma kin aikesh'insa?
"Aa dai yanzu nake sh'irin kiransa,".
Ameen ne ya kalli inda Haleema ke zaune yace
"Hmmmmmm!! zan kama yarinya ne duk randa Abba ya tafi,
  yasa kai ya fice,"
Sai kina hak'uri fa y'ata, d'annawa akwai kirki"
"uhm" murmush'i kawai tayi, itadai so take sud'an bar parloun sukoma d'akin Haleema dan takasa sakewa, duk kuwa da yanda su duk suka sake da ita, musamman Abba dayake jin kamar 'yar daya haiface.
Yarinyar ta burges'hi saboda nutsuwarta da kunyarta.
Kiran sallar maghriba aka fara, sh'ine dalilin dayasa suka tash'i Abba yayi masallaci, Ameenah da Haleema ma sukayi d'akin Haleeman,
suka d'auro alwala suka fito sukayi sallah kowacce ta roki' ubangiji buk'atunta.
Tv dake parloun suka kunna suka fara kallon Mbc bollywood, suna wani film ne wanda Ameenah ke mugun so, wato *vivah*
murmush'i ne d'auke a fuskarta, dan intana kallon, sai taga Ameen yayi yanayi da jarumin film d'in _Shaheed kapoor_
sai dai ya nuna masa hasken fata, amma gani take ma yafi _Shaheed kapoor_ d'in ky'au.
Masoyan sun burgeta, dan tana kallonne ma, Haleema taga tension d'in Ameena baya kanta dan haka ta kalleta da tsokana tace"Ah su juliet tunanin romeo akene?
  "hmmmmm" Ameenah ta harareta batace mata uffan ba.
Mamy ce ta kira Haleema tace ta kira Yah ameen, ai tana zuwa d'akinsa ta sh'iga a bud'e amma bayanan,
ta sh'iga bedroom, bata gansh'iba,. Bata kuma ji motsin ruwa ba bale ta lek'a toilet d'insa.
Dan haka kawai ta fita.
Ashe sh'ikuma yana ciki, Haleemah na fita, ya d'auko Key d'in motarsa zai fita.
Haleemah na sh'iga ta sh'aidawa Mamy bayanan,
ganin dare na k'arayi tace"jeki kira driver yazo ya maidata,
"Daughter bari nazo ko? Mamy ta fad'a tana d'an dafe da kafad'ar Ameenah,
stair d'inta ta hau,
Haleemah ta dawo tace ma Ameenah tazo ga driver nan zai kaita.
Mamy ce ta sauko dawata bag me ky'au,
daga gani kayan kw'alliya ne a ciki dasu turare dan naji k'amsh'i sosai.
Haleema ce ta ruk'omata ledar da Abba ya bata ta tsaraba, da bag d'in da Mamy ta bata.
Tayiwa Mamy godiya, tayi mata sallama
inda Mamy tace"kicewa Mamanki sai nazo ina gai'sheta"
"to"
sannan suka fito.
Karaf idon Ameenah cikin na Ameen ya fito sai uban k'amshi yake, ya sauya kaya zuwa dark blue sh'adda taji aiki,.
K'amsh'i kawai yake bugawa,
Ameenah ce ta tab'o Haleema "ke ina zash'i?
da daddaren nan,! yawani ci wanka?,
"oho masa, koma ina zash'i ki barni dash'i, kar kice masa uffan ki tsaya kiyi kallo.
"Toh" kawai tace da ita.
"Yah ameen so kake Mamy tai fush'i dakai ne?
cataifa ka kai Friendy gida sh'ine zaka fita,
Hararta yayi tukun kafin yace"Baga driver can ba nifa unguwa zani,
"Driver Mmy aikensa zatayi gidansu Aunty khadeeja,(Tsohuwar matarsa idan baku manta ba).
Sai dai in drivern yakaita gida kai kuma kaje aiken da drivern, gidansu Aunty khadej. ................"Shut up,
muje, abinda kawai ya isa cewa kenan, dan bayason ya tuna da khadeeja taci amanarsa sai dai Allah ya isa .
Hannu ta d'aga Jinjina Ameenah tayi mata, kin iya suburbud'o k'arya. Sukayi dariya
tabud'e mata mazaunin me zaman banza, ta zauna,
kallo kawai yabisu dash'i, danya fuskanci yaran halinsu yafi k'arfinsh'i.
S'higa ya kunna mota, zai juya yafita, Haleema tace"Au Yah Ameen, Mamy tace ka sh'igar mata da wannan", ta mik'o masa Ledar nan da bag,
"wai daganan sai ku gaisa da Mamanta.
Karb'a kawai yayi yako d'orasu asaman cinyar Ameenah,
yaja motar yabar gida,.
Har ya fita titi, besan inane gidansu ba, besan wacce unguwa take ba,
yanason ya tambayeta amma baison yimata magana,.
Dan haka kawai ya zaro phone nash'i ya kira Haleema, yana tambayarta inda zai kaita,.
"Ah yah Ameen ka tambayeta mana".
Abinda tace kenan ta katse wayar.
"Mtsww"
Parking yayi kawai yaci gaba da danna wayarsa, tanason yimasa magana amma tanajin tsoro, gash'i har anfara kiran ish'ai.


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

2 Comments to " Ameen Da Ameena Hausa Novel Part 1 To 64 - Realityloaded"