Maganin Basir: Yanda Zakayi Maginin ko Wani Irin Basir


    
Don magance kowacce matsalar basir sai abi daya daga cikin wadannan hanyoyin.

1. MAGANIN BASIR MAI RIKITA CIKI

1-Anemi sassaken baure, da sassaken hararrabi adaka atankade arika Shan cokali daya acikin kunu sau biyu arana zuwa kwana biyar.
2-Anemi sassaken gamji da sassaken taura ajika arika Shan Kofi daya sau biyu arana zuwa kwana biyar.

2. MAGANIN BASIR MAI TSIRO

1-Anemi man ridi arika shafawa sau biyu arana, Kuma ake cin ridin sau biyu arana zuwa kwana bakwai.
2-Anemi kitsen damo mai kyau, ariki shafawa sau biyu arana zuwa kwana bakwai.

3. MAGANIN BASIR MAI FITAR BAYA

1-Anemi sassaken baushe atafasa inya rage zafi arika zama aciki, sau biyu arana har Asamu lafiya.
2-Anemi man kadanya akwaba da garin tafarnuwa ariki shafawa sau biyu arana har Asamu lafiya.

4. MAGANIN BASIR MAI HANA CIN ABINCI

1-Anemi sassaken kadanyar-rafi da ganyen sabara adaka atankade arika Shan cokali daya acikin nono sau biyu arana zuwa kwana bakwai.
2-Anemi 'ya'yan Bagaruwa da ganyen runhu adaka atankade arika Shan cokali daya acikin Madara ko nono sau biyu arana zuwa kwana bakwai.

5. MAGANIN BASIR MAI KARA KARFIN MAZA

1-Asamu saiwar dundu da saiwar kargo(kalgo) atsima arika Shan Kofi daya sau biyu arana zuwa kwana biyar.
2-Anemi saiwar mangoro da saiwar tafashiya da saiwar kirya adaka atankade arika Shan cokali daya acikin shayi ko kunu sau biyu arana zuwa kwana biyar.

 6. MAGANIN BASIR MAI SA ZAFIN JIKI
1-Anemi sassaken faru adaka atankade arika Shan cokali daya acikin madara ko nono sau biyu arana zuwa kwana biyar.
2-Anemi sassaken rawaya da ganyen runhu adaka atankade arika Shan cokali daya acikin madara ko nono sau biyu arana zuwa kwana biyar.

7. MAGANIN BASIR MAI SA YAWAN TUSA

1-Anemi sassaken danya da sassaken dorawa adaka atankade arika Shan cokali daya acikin kunu sau biyu arana zuwa kwana bakwai.
2-Anemi sassaken gawasa adaka atankade arika Shan cokali daya acikin shayi ba Madara sau biyu arana zuwa kwana bakwai.


SHARADI
Matukar Ka fara aiki da maganin mu na Basir kowanne irine,to  ba a Jima i har se angama shan magani. Insha Allah za awaraka cikin hukuncin Allah daga Dukkan matsalulin.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Maganin Basir: Yanda Zakayi Maginin ko Wani Irin Basir"

Post a Comment