Amfanin Kanumfari Wurin Gyaran Gashi



Idan mutum yayi amfani da kowanne bangare na wannan hadin, In Sha ALLAHu gashin shi zai kara tsayi, zai cika, zai daina kaikayi, zai rika kyalli kuma yana kara tsayi DA YARDAR ALLAH.

1- A sanya kanunfari daidai kima kamar a cikin kwalbar Man Zaitun sai a barshi tsawon kwanaki 3, sai a rika shafawa a gashin tun daga kasan gashin har saman gashin.

2- Ko kuma a sanya wani adadi na Kanunfari a cikin roba/gorar ruwa mai kyau tare da ruwa a ciki har tsawon kwanaki 3,  sai a rika wanke kai da shi a kullum tun daga asalin gashi har zuwa saman gashin, idan ya tsane sai mutum yayi amfani da man da yake amfani da shi a gashin.

Duk wanda kayi amfani da shi ya yi kuma za kuga aikinsa da Yardar Allah, mutane da dama sun gwada. Allahu A'alam.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Amfanin Kanumfari Wurin Gyaran Gashi"

Post a Comment