Amfanin Bawan Kwakwa ga Lafiya



Idan mutum yasha  guba (poison) a rashin sani sai ayi gaggawar hada masa wannan hadin na bawon kwakwa ,  yadda ake hada shi shi ne kamar haka:

Za a samo bawon kwakwar ne sai a kona shi a cikin wuta har yayi baki kamar yadda yake a cikin hoton can, sai a daka shi ayi garin shi yayi laushi sosai sai a rika dibar garin cokali 3 ana zubawa a ruwan dumi kimanin kofi daya kafin a sha a tabbatar an kada shi kuma an gauraya shi da kyau.

Sai a baiwa wanda yasha guba (Poison) din yashanye, IN SHA ALLAHU za kuga ya amayar da gubar da yasha da YARDAR ALLAH.

Kamata yayi a samu garin bawon kwakwar a ajiye shi sbd gudun  ko-ta-kwana ko kuma taimakon gaugawa.

Amma kuma a rika lura da abinda ake ci ko ake sha saboda tsaro kuma duk halin da kake ciki kar ka ksukura ka ki ambatar *BISMILLAH* kafin kaci ko kasha wani abu.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Amfanin Bawan Kwakwa ga Lafiya"

Post a Comment