Karin Lafiya: Kadan Daga Cikin Anfanin Kwallon Dabino


 

Abune sananne cewar: Naman wasu dabbobin ko na tsohuwar dabba suna da wahalar dafuwa, wani yakan kai wajan awa ɗaya da rabi kafin ya dafu, amma idan mutum yayi amfani da  ƙwallon dabino ba lallaine ya iya kaiwa mintuna 30 ba.

Yadda ake amfani da shi shine: Bayan an tsaftace kwallon dabinon sai a sanya kamar  guda 3 ko 4 a cikin tukunya tare da naman, sai a rufe da murfi abarshi a wuta har tsawon mintuna 15 ko 20 ya danganta da yawan naman sai a bude In sha ALLAH za aga abin mamaki, domin naman zaiyi dafu, yayi kyau kuma yayi dadi.

Shi kuma naman Kaza ko kuma duk wani abinci nau'in kwaya mai wahalar dafuwa idan aka sanya masa ƙwallon dabino guda 2 ma ya wadatar da Yardar Allah zai dacikin kankanin lokaci mintuna 10 ko kasa da haka sai a bude za aga abin mamaki.

Baya ga wadan nan kuma Kwallon dabino yana da matuƙar amfani sosai a jikkunan mutane idan aka sanya shi a abinci yayi dafa abincin amfanin da Allah ne kadai yasan iyakarsu. Wannan kadan kenan daga cikin amfaninsa idan Allah ya kaimu wani lokaci za mu kara ambato sauran amfanin nasa.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Karin Lafiya: Kadan Daga Cikin Anfanin Kwallon Dabino"

Post a Comment