Hukuncin Wankan Tsarki da SabuluAssalamu alaikum bark da safiya malan inada tambaya kamarhaka nine nikeso nayi waikan. Juma a kuma inaso nayi waika da sabilu to yaya waikan zankasan.cene malan na gode Allah ya sakada mafificin alkairi malan Allah yayi jagoranci

         AMSA
Walaikum sallam warahmatahi wabarkatahu

Alhamdu-lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Musulmin da yayi wakan juma'a sannan yayi wakan sabulu, wankansa ya yi, kuma babu laifi yayi Sallah kai tsayi, idan yayi alwala kuma bai shafi azzakarinsa ba lokacin wankan sabulun. Shafan zakari da cikin tafin hannu yana warware alwala. Domin haka, sai maza su kiyaye. Idan sun shafi al-aura, to sai sun sake alwala.

Babu laifi mutum yayi wankan tsarki bayan yayi wakan sabulu, kamar yadda zai iya yin wankan tsarki sannan yayi wakan sabulu. Wakan tsarki
ana yinsa ne da ruwa mai tsarki kuma mai tsarkakewa, wato ruwan da dandanonsa bai canza ba, launinsa bai canza ba kuma kamshinsa bai
canza ba.

Idan mai wanka zai fara wankan ibada kafin na sabulu, to babu wani khaufi dangane da ruwansa, saidai yakiyaye kar yashafi azzakarinsa bayan alwala. Amma idan mai wanka zai fara na sabulu ne, to ya kiyaye ruwansa kar ya gurbata da kumfar sabulu har ya canza launinsa, ko
kamshinsa, ko dandanonsa.

Allah ya tsare-mana ibadar mu kuma ya karba mana. Amin.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Hukuncin Wankan Tsarki da Sabulu"

Post a Comment