Famili Planning: Hukuncin Yin Tazarar Haihuwa


Shin ko akwai dalilai na shariah da suke halatta mace ta juyar da mahaifarta ko kuma ta samu tazarar haihuwa?

𝐀𝐌𝐒𝐀
To ɗan'uwa amfani da abin da zai kayyade iyali, ya kasu kashi biyu:

1. Ya zama zai hana ɗaukar cikin kwata-kwata, a nan bai halatta ba, saboda ya saɓawa manufar shari'a na yawaita al’uma, kuma ‘ya’yan da take da su za su iya mutuwa sai ta koma mai wabi.

2. ya zama an tsayar da shi ne na dan wani lokaci, kamar mace ta zama tana yawan haihuwa kuma cikin yana wahalar da ita, sai ta yi nufin ta tsara haihuwarta ta yadda za ta haihu duk bayan shekara biyu ko makamancin haka, to wannan ya halatta in dai miji ya bada izini kuma ba zai cutar da matar ba, dalili akan haka shi ne sahabbai sun kasance suna AZALU a zamanin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam don kar matansu su ɗauki ciki, kuma ba’a hana su ba, kamar yadda Bukari ya rawaito daga hadisin Jabir mai lamba ta: 4911.

Abin da ake nufi da AZALU shi ne idan namiji yana saduwa da matarsa idan ya ji maniyyi zai fito sai ya fitar da azzakarinsa ya zubar da maniyyin a wajen farji.

Duba Dima'uddabi'iyya na Ibnu Uthaimin shafi na 57.

Sannan kuma an haramta: *VASECTOMY* wato kashewa 'ya'yan maniyyin namiji. Idan akayi ma namiji irin wannan aikin, to zai iya yin Jima'i amma har abada ba zai haihu ba.

TUBECTOMY shima haramun ne. (Daurewa bakin mahaifar mace, ta yadda Qoyin halitta ba zai samu damar shiga ba). Idan aka yiwa mace irin wannan aikin, to har abada ba zata sake haihuwa ba. Domin kuwa Qwan halitta ba zai samu damar shiga ba, ballantana har maniyyi yayi fertilizing ɗinsa.

Ba'ayi sai dai idan matar ta kasance anyi mata operation sau da dama, kuma likitoci sun bada tabbacin cewar ba zata iya rayuwa ba idan aka sake yi mata wani operation ɗin.

Hakanan irin allurar da ake yiwa mata domin kashewa Qoyin halittar ɗan adam (gaba ɗaya) daga cikin mahaifarsu. Itama haramun ce.

Abinda ya kamata kayi, in har matarka tana da larurar da addini ya amince ayi *family planning* saboda ita, sai kaje ka tuntubi kwararren likita, musulmi wanda kuma yake da fahimta irinta addini domin ku tattauna, ya baka shawarar da ta dace.

Amma kafin nan ya kamata ka san cewar duk waɗannan kwayoyin da alluran tsarin iyali ɗin, suna da mummunan SIDE EFFECT ga ita matar taka. Musamman ma idan tsufa yazo.

Babu mamaki ta samu mental problem (hauka) ko mummunar mantuwa. Ko shanyewar jiki, ko kuma jijjigar gaɓoɓin jiki. Ko kuma sankarar mahaifa, ko cancer acikin bladder ɗinta.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Famili Planning: Hukuncin Yin Tazarar Haihuwa "

Post a Comment