Hukuncin Yin Sallah a Zaune
Wednesday, November 1, 2023
Add Comment
Assalammu Alaikum, dan Allah menene hukuncin me yin sallah a zaune, kuma tana yawo ko ina amma idan ta zo yin sallah sai kafan ya fara zafi sai ta yi a zaune?
AMSA
Wa'alaikumus Salamu:- sallar farilla wajibi ne a yi ta a tsaye, saboda yin sallah a tsaye rukuni ne daga cikin rukunnan sallah, ba makawa sai mutum ya yi ta, amma yin sallah a zaune ga wanda ba shi da lafiya, ko ba shi da ikon yin tsayuwar, wannan babu laifi idan ya yi sallah a zaune, saboda ya tabbata daga sahabin Annabi ﷺ Imrana ɗan Husaini Allah ya qara masa yarda ya ce:
Na kasance ina fama da basir, sai na tambayi Annabi ﷺ game da yadda zan yi sallah, sai ya ce mani: "Ka yi sallah a tsaye, idan ba za ka iya ba ka yi a zaune, idan ma ba za ka iya ba ka yi a kan ɓarin jikinka (wato a kwance)". Bukhariy 1117.
Wannan dalili ne a kan yin sallah a zaune ga mara lafiyan da ba zai iya yin ta a tsaye ba, ko kuma ga wanda tsayuwar take masa tsananin wahala kamar wanda ya tsufa tukuf da makamantan haka. Amma lafiyayyen mutum, wanda yake da ikon yin sallah a tsaye, idan ya yi ta a zaune sallarsa ba ta inganta ba.
Related Posts
Subscribe Our Newsletter
0 Comments to "Hukuncin Yin Sallah a Zaune"
Post a Comment