Iddar Matar da Aka Saketa Kafin Saduwa Bayan Aure


As-Salaam Alaikum. Mutum ne auri mace watanni uku kenan da ɗaura musu aure amma ba ta yarda da shi ba, wai tsoro yake ba ta. Yanzu dai ya aiko mata da takardar saki zuwa gida. Shi ne suke tambaya: Yaya maganar iddarta?


Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Abin da Allaah Ta’aala ya ce dai shi ne:
یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوۤا۟ إِذَا نَكَحۡتُمُ ٱلۡمُؤۡمِنَـٰتِ ثُمَّ طَلَّقۡتُمُوهُنَّ مِن قَبۡلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ فَمَا لَكُمۡ عَلَیۡهِنَّ مِنۡ عِدَّةࣲ تَعۡتَدُّونَهَاۖ فَمَتِّعُوهُنَّ وَسَرِّحُوهُنَّ سَرَاحࣰا جَمِیلࣰا
Ya ku waɗanda suka yi Imani! Idan kuka auri muminai mata sannan kuma kuka sake su tun kafin ku shafe su, to babu wata idda da kuke da ita a kansu. Ku ba su mutu’a na saki, kuma ku sake su saki mai kyau. (Surah Al-Ahzaab: 49).

Sannan a wurin tafsirin wannan ayar Sahabi Abdullaah Bn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa)_ya ce:

فَهَذَا الرَّجُلُ يَتَزَوَّجُ الْمَرْأَةَ ، ثُمَّ يُطَلِّقُهُا مِنْ قَبْلِ أَنْ يَمَسَّهَا ، فَإِذَا طَلَّقَهَا وَاحِدَةً بَانَتْ مِنْهُ ، وَلَا عِدَّةَ عَلَيْهَا أَنْ تَتَزَوَّجَ مَنْ شَاءَتْ
Wannan a kan mutumin da ya auri mace ne, sai kuma ya sake ta tun kafin ya sadu da ita. Idan ya sake ta saki ɗaya, to ta yanke daga gare shi kenan, kuma babu idda a kanta. Tana iya auren duk wanda ta so.

Game da ɓangaren farko na ayar kenan.

Amma a kan sashen ƙarshenta sai ya ce:
إِنْ كَانَ سَمَّى لَهَا صَدَاقًا ، فَلَيْسَ لَهَا إِلَّا النِّصْفُ ، إِنْ لَمْ يَكُنْ سَمَّى لَهَا صَدَاقًا مَتَّعَهَا عَلَى قَدْرِ عُسْرِهِ وَيُسْرِهِ ، وَهُوَ السَّرَاحُ الْجَمِيلُ
Idan ya riga ya yanka mata sadaki kafin sakin, to ba za ta samu komai ba sai dai rabin sadakin kawai. Idan kuma bai riga ya yanka mata sadaki ba, sai ya ba ta mutu’ar saki da gwargwadon talauci ko wadatarsa. Wannan kuma shi ne ma’anar: ‘Saki mai kyau.’ _(At-Tafseerus Saheeh: 4/134)._

Wannan ya nuna:
1. Babu idda a kan macen da aka sake ta matuƙar dai an tabbatar cewa mijin bai yi kwanciyar aure (watau, bai sadu) da matar ba.

2. Idan a lokacin sakin mijin ya riga ya ambata mata sadakin da zai ba ta, to rabin sadakin kawai shi ne haƙƙinta.

3. Idan kuwa bai riga ya yanka mata sadaki ba, to babu wani abu na sadaki a kansa sai dai mutu’a (alherin) saki kawai, da gwargwadon ƙarfinsa.

4. Mijin da ya sake ta kafin tarewa ba shi da ikon yin kome (komo da ita), sai dai da sake sabon ɗaurin aure, idan ta amince.

5. Idan kuma ba ta amince ba, to tana iya ƙulla aure da duk wanda take sonsa, ko da kuwa ranar da mijin ya sake ta ne.

6. Idan miji ya saɓa wa wannan ƙa’idar, to bai bi umurnin Allaah Ta’aala ba na cewa, ya sake ta saki kyakkyawa.

7. Idda tana zama wajiba ce a kan mace ta dalilin rabuwa da mijin ko dai ta hanyar mutuwar auren ko kuma mutuwar mijin.

8. Babu bambanci a nan ko sakin a bayan sahihin ƙullin aure ne ko kuma a bayan lalataccen ƙullin aure ne.

9. Idda a kan mace da aka saki tana zama Wajiba ce ko da sakin na-farko ne, ko na-biyu ne, ko kuma na-uku ne.

10. Amma idan rabuwar auren ta zama saboda mutuwar miji ne, to a nan wajibi ne ta yi idda na tsawon watanni huɗu da kwanaki goma ko mijin ya sadu da ita ko bai sadu da ita ba. (Tamaamul Minnah: 3/219-220)

Allaah ya ƙara mana ilimi mai amfani.

WALLAHU A'ALAM


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Iddar Matar da Aka Saketa Kafin Saduwa Bayan Aure"

Post a Comment