Hukuncin Mata ta Rage Kudin Cefane Domun Biyan BukataAssalamu alaikum da fatan MALAM yana cikin koshin lafiya, Allah yasa haka. Bayan haka inada tambaya ce, MALAM Dan Allah mijina yaki ya biya mun kuɗi nayi karatun sanin addinina kuma shi bazai iya koya mun ba amma ya yadda nayi, Toh ya halatta in dinga cire wa a kuɗin cafane da yake ban Dan na tara har yakai nabiya kuɗin karatun, Hakan ya halatta akaramakallahu?

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Sata tana daga cikin manyan Zunubai a Musulunci. To amma akwai keɓantattu Hukunci dangane da zamantakewar Ma'aurata.

Misali : Ciyarwa, Shayarwa, Ilimantarwa, samar da sutura, da kuma matsuguni duk Waɗannan suna daga cikin hakkokin da kowacce yarinya take dashi akan iyayenta. Amma daga ranar da aka daura aurenta to hakkokin nan sun koma kan Mijinta.

Wajibi ne akansa ya rika koyar dake addini, ko kuma ya dauko Miki wacce zata koyar dake, ko kuma ya kaiki wajen da zaki koya.

Idan kuma ya gaza wajen sauke wannan hakkin, to kina da Zaɓi guda biyu anan:

1. Ko dai ki sanar ma Waliyyansa kai tsaye, ko kuma Mahaifanki su sanar dasu domin azauna ayi masa nasiha a tunasar dashi akan haka.

2. Ko kuma ki rika rage ɗan wani abu daga cikin kuɗin cefane ɗin. Ki ɗauka bisa Gwargwadon yadda zai isheki ki biya kuɗin Islamiyyar. Amma Kar ki sanya almubazzaranci aciki.

Hujjah anan ita ce  hadisin da Imamul Bukhariy ya ruwaito daga Nana A'isha (ra) tace: "HINDU BINTU UTBAH (RA) TAZO WAJEN MANZON ALLAH ﷺ TACE "YA RASULALLAHI HAKIKA ABU SUFYAN (MIJINTA) MUTUM NE MAI KWAURO (ROWA) BA YA BANI ISASHEN ABINDA ZANCI NI DA YARANA. SAI DAI ƊAN ABINDA NA ƊAUKA BA TARE DA SANINSA BA". Sai Manzon Allah ﷺ Yace "KI ƊAUKI ABINDA ZAI ISHEKI KE DA YARANKI TARE DA ADALCI".
Aduba Sahihul Bukhariy hadisi na 5364).

To anan kin ga Ilimantarwa shima hakki ne na Wajibci kamar yadda Ciyarwa da shayarwa suke.

Acikin Littafinsa mai suna "NAILUL AUTAR" Juzu'i na 6 shafi na 383, Imamush Shaukaniy yayi shigen irin wannan maganar dangane da halascin cirar wani abu daga dukiyar Miji domin riskar da wani hakkin da ya wajabta akansa amma bai sauke ba.

Sai dai Malamai sun ce irin wannan yana halatta ne agun Matar da ba'a tsoron lalacewar tarbiyyarta ta dalilin haka. Don haka idan kin san zaki iya samun matsalar lalacewar tarbiyyah, wato zuciyarki zata zarme to bai halatta gareki ba.

Yana halatta ne kaɗai ga matan da suke da tsantseni da tsoron Allah. Idan kin san kina cikinsu to shikenan.

Kuma ilimin addini muke magana akai. Ba wai Ilimin boko ba. Domin karatun boko ba wajibi bane. Kuma ba ya cikin hakkin mace akan mijinta.

Kuma idan Mace ta rage wani abu domin yin buki, ko sayen kayan kwalliya, ko wasu bukatun kanta, to wannan kai tsaye haramun ne.

WALLAHU A'ALAM.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Hukuncin Mata ta Rage Kudin Cefane Domun Biyan Bukata"

Post a Comment