Hadisin Mu na Yau a Wannan Rana - Hankali da Duniya


(A YI HANKALI DA DUNIYA) 


MANZON ALLAH (SAW) YACE: "KA KASANCE A DUNIYA KAMAR BAƘO, KO MAI ƘETARA HANYA"


ABDULLAHI ƊAN UMAR, YA KASANCE YA NA CEWA:  IDAN KA WAYI GARI KADA KA JITA YAMMA,

IDAN KA YAMMATU KADA KA JIRA SAFIYA, KAYI AMFANI DA LAFIYAR KA KAFIN TA ƘARE, KAYI AMFANI DA RAYUWAR KA KAFIN MUTUWA. 


FA'IDA

WANNAN HADISI YANA KOYA MANA MAHIMMANCIN KULA DA DUNIYA,


KADA MU RUƊU DA ITA,

KADA MU SHAGALA DA ITA,

1.KARDA  KO KADAN MU BAR WANNAN DUNIYA TA RUDEMU  TA ƊAUKE HANKALIN MU,

2. YADDA KA SHIGO HAKA ZAKA FITA. 

2. KADA KA YI WASA DA KWANAKI BIYU RANAR   MUTUWA, DA RANAR ALƘIYAMA.

3. KANA IYA MUTUWA A KOWANNE LOKACI DAGA YANZU.

4. DUK ABIN DA KA TARA NAN ZA KA BARSHI.

A SHIRI DON LAHIRA

5.KA NEMI DUNIYA KAMAR BA ZA KA BARTA BA,

6. KUMA KA NEMI LAHIRA KAMAR GOBE ZA KA MUTU.


ALLAH YA SA MU DACE.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Hadisin Mu na Yau a Wannan Rana - Hankali da Duniya"

Post a Comment