Sarkan Kafa: Hukuncin Wancce take Saka Sarka a KafantaAssalamu alaikum malam barka safiya
Malam Allah ubangiji yasa muku da alkhairi da irin wannan tunasarwa da gudummawa da kuke kokarin bamu Allah yasaka da mafificin alkhari. Malam "yar uwa ta ma,ana yayata tana sanya sarka a kafar ta idan anyi mata magana sai tace wai addini ya yarda da saka sarka a kafa ita babu ruwanta da abinda mutane zasu fada akanta har status take da wannan hoton

           AMSA
Wa Alaikis Salaam:-

Eh lallai Addini ya yarda Mace ta sanya Sarka a Kafar ta, Addinin Allah ya da shi ko a Zamanin Annabi ma mata suna Saka Sarka a Kafar Su.

Toh amma ba za'a kafa hujja da shi ba ace bari a saka ba tunda Addini ya yarda da shi, ai Addinin Musulunci ba Addinin Wawaye bane, Akwai Abunda Addinin yake dubawa kafin tayi Hukunci akan abu, shi Addinin Musulunci a kullum yana duba A Zamani ne da Abunda Zamani yake tafiya da shi, Matukar Addinin Allah ya samu Cewa ai Wannan Abun mutanen Banza ne suke Ƙwalliya da shi, toh Wajibi ne Addini ya hana Saka shi Saboda Hadisin Annabi da yayi Magana Cewa duk Wadda ya Siffantu da wasu Mutanen Banza toh Shima yana Cikin su a Ranar Alkiyama, Shin Sarkar Kafa a Yanzu Mutanen Ƙwarai ne Suke Sakawa Ko Ƴan Maɗigo ne? Idan mutanen Banza ne Kenan ya Haramta ga Mutumiyar Kirki ta Saka, amma idan Mutumiyar Kirki ne Suke Sakawa Kenan sai a bi Hadisin Zamanin Annabi a lokacin da Mata Suke Sakawa amma Annabi bai hana su ba.

Saboda Haka a Yanzu ya zama Cewa ƴan iska ne masu sawa, don haka ke Mutumiyar Kirki me zai kai ki, ki saka abun Mutanen Banza ƴan Maɗigo??  Kin ga Kenan duk Mutumiyar Kirki ba zata so ace yau an kamantata da Mutanen Banza ba, Yanzu ke ba ki Karuwanci, sai wata Qawar ki ko mijin ki yace miki Karuwa, don Allah me za ki ji a Ranki?? 

Sannan kuma Annabi ne yace ma duk Wadda ya Siffantu da wasu Mutanen Banza a wajen sanya sutura ce ko a wani abu daban, toh yana Cikin su, kuma a Ranar Alkiyama Za'a tashe su tare, toh shin ya zatayi da Wannan Maganar Annabi?  Tunda ga shi dai Ƴan Maɗigo sune masu Amfani da Sarkar Kafa, itama kuma tace ai Addini ya yarda da shi don haka zata saka babu ruwan ta da Maganar mutane, kenan itama tana Cikin su, Sannan ga Hadisi ya zo daga Annabi a Ranar Alkiyama zasu tashi tare.

Shin ta san Ranar mutuwar ta ne?  Idan tana Cikin sakawa sai Allah ya Ɗauki Rayuwar ta fah?  Me zata gayawa Ubangijin ta? Kin ga Kenan a Ranar Alkiyama tana layin Waɗancan Ƴan Maɗigo masu Saka Sarka a Kafar Su Domin da suke take koyi bata koyi da Mutanen Ƙwarai waɗanda suka ji an ce bai dace ba suka ɗena sakawa ita tace A'a. Idan kuma tana yin Maɗigon toh nan kuma Azabar yafi Haka.

Saboda Haka ba hujja bane cewa don Addini ya yarda da shi Sannan kuma a rika Sakawa, ai Addinin ma yana duba zamani ne da kuma Abunda yake tafiya a Cikin zamani sannan sai yayi Hukunci akai. Dafatan kin gane koh?  Ki tura musu su karanta dakyau ba Burgewa bane ba kuma ƙwalliya ba ce, Wajibi a ji Tsoron Allah a Siffantu da Siffar mutanen Kirki ba mutanen Banza ba.

Wallahu A'alamu.


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Sarkan Kafa: Hukuncin Wancce take Saka Sarka a Kafanta"

Post a Comment