HUKUNCIN YIN SALLAH DA TUFAFI MAI HOTUNAN MUTANE KO DABBOBI

TAMBAYA TAMBAYA TAMBAYAAssalamu alaikum. Mene ne hukuncin yin sallah da atamfa mai zanen tsuntsu?

           AMSA
Wa'alaikumus Salam. Ba ya halasta mutum ya yi sallah da tufafin da ke ɗauke da hotuna ko zane-zanen abubuwa masu rai, kamar mutane ko tsuntsaye da sauransu, malamai suna kafa hujja da hadisin da Annabi ﷺ ya ce: "Mala'iku ba sa shiga gidan da a cikinsa akwai hoto ko kare". Bukhariy 3226, Muslim 2106.

Idan wanda ya yi sallah da tufafi mai ɗauke da hotunan rayayyun abubuwa bai san hukuncin hakan ba, to babu komai a kansa na laifi, idan kuwa ya sani, to sallarsa ta yi, sai dai yana da zunubi a mafi ingancin ɗaya daga cikin maganganun malamai Allah ya yi masu rahama, amma daga cikin malamai akawi masu cewa sallar sa ɓatacciya ce saboda ya yi sallah a cikin haramtaccen tufafi. Duba Majmu'u Fatáwá na Ibn Uthaimeen, mujallad na 12, shafi na 360.

Harwayau kuma, Nana A'isha ta ruwaito hadisi cewa, Annabi ﷺ ya yi sallah da wani mayafi da ke ɗauke da wasu alamomi, sai ya dubi wannan tufafi ɗin sau ɗaya, lokacin da ya sallame, sai ya yi umurni da a tafi da wannan mayafi nasa zuwa ga Abu Jahmin a karɓo masa mayafin Abu Jahmin, ya kuma ce: "Lallai wannan mayafi shi ne ya ɗauke mani hankali ga sallata". Bukhariy 373, Muslim 556.

Saboda haka ya zama wajibi ga mai sallah ya qaurace wa duk wani nau'in tufafi da zai riqa ɗauke masa hankali a lokacin da yake sallah.

Allah ne mafi sani.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "HUKUNCIN YIN SALLAH DA TUFAFI MAI HOTUNAN MUTANE KO DABBOBI"

Post a Comment