Mene Ne Ake Nufi da Blogging Kokuma Blogger a Hausance


Assalamu alaikum yan uwa. Barkan mu da wannan lokaci. A yau zamu tattauna akan wasu abubuwa daya kamata ku ƴan uwa kusani. Domun ilimi ne me anfani, kuma ze anfanar da yardar Allah.


Zamu tattauna ne yau dangana da abunda ake kira da Blogging.


Menene Blogging

Ita wannan Blogging ɗin wata abace wacce ake aiwatar da ita a yanar gizo, a inda mutum ze dauki wani bangare na ilimi, musamman abunda yafi kwarewa akai, Yanayin rubutu akan waɗannan ababe domun yasama mabiya waɗan da zasu dinga karanta wannan rubutu nasa.


Abin da blog ya kunsa, yawanci yakanzo ne ta hanyar labarai akan ita shafin yanar gizon wanda mutum ke rubutawa da ake kira blogs posts. Abubuwan da kake karantawa a yanzu haka, shine misalin wannan Blog posts din.


Waye Blogger.

Wanda yake gudanar da shafukan shi ake kira da Blogger. Yanaa rubutu da watsa posts-posts, akai-akai sababbi dakuma gyare gyare na rubutu, da kuma amsa tambayoyin masu tambaya.


Menene Blog

Blog kaface a yanar gizo, inda shi blogger yake amfani da ita wurin yin rubuce rubucen sa yana watsawa a sauran shafukan yaɗa zumun ta. Blog kaman website take, amma ta banbanta da website saboda wasu takai tattun abubuwa da bata dashi wanda website keda shi. Yanzu kaman wannan kafa ta REALITYLOADED ta kuke ciki a yanzu kuna wannan karatun, toh misalin Blog kenan. Amma idan ka kware wurin harkan coding na programming. Sa'annan kana da iliminta sosai, zaka iya design din ta ka ƙawata ta tayi kaman Website.


Meyasa ake Blogging?

- Akwai dalilai da yawa dakesa a fara blogging. Yakan zama don amfanin sirri, kuma kaɗan ne kawai masu ƙarfi, don rubutun ra'ayin kanka a yanar gizo. Yin rubutun ra'ayin kanka a yanar gizo ko kasuwanci, ayyuka, ko wani abu da zai iya kawo maka kuɗi.


- Wani kuma yana Blogging ne kawai saboda ya tara mabiya. Saboda idan yayi rubutu akan wani abu, yasama masu gani su karanta sumara mai baya akan ra'ayin shi dayayi rubutu akai. Shide buƙatarsa a sansa.


- Wasu kuma sukan fara Blogging ne domun koyar da al'umma wani fanni na ilimi ta hanyar rubutu a kafar yanar gizo.


Takaitaccen Kammalawa

  • Rubucen rubucen ra'ayin kanka a yanar gizo taqaitaccen sigar "weblog," wanda ake farashi kaman a matsayin diary mai kama da masu amfani da intanet na farko.
  • Rubutun ra'ayoyi na kanka a yanar gizo na zamani hanya ce mai fa'ida wacce ta ƙunshi rubutattun kalmomi, daukar hoto, bidiyo, da kowane nau'in batutuwa.
  • Haka harkan  Kasuwanci na iya amfani da shafukan yanar gizo don fitar da abokan cinikai zuwa gidan yanar gizon su, tareda haɓaka aikin SEO, ko samar da madadin hanyoyin samun kuɗi.
  • Shafukan yanar gizo (Blog) sun bambanta da gidajen yanar gizo na gargajiya (Website) saboda ana sabunta su akai-akai, kuma suna sauƙaƙa wa masu bibiyanta damar yin hulɗa da juna da masu ƙirƙirar abun cikin Blog din.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Mene Ne Ake Nufi da Blogging Kokuma Blogger a Hausance"

Post a Comment