Amfanin Aikata Alkhairi a Rayuwan Duniya

Assalamu Alaikum Warahmatullah, ƴan uwa barkan mu da sake saduwa a wanna kafa ta yanar gizo me albarka. 

A yau zamu danyi jawabi ne ko kuma ince taƙai tacciyar nasiha ga ƴan uwa mabiya.

 Ku kalli wannan hoto dake a kasan wannan rubutu.


Wannan hoton da kuke gani, wata ma'aikaciyar a sibiti ce tadaukeshi,
tayi rubutu kamar haka:

Kwanaki 23 kenan da wannan majiyyaci yake asibiti. Kuma a cikin wadannan kwanaki 23 babu wanda ya zo ganinsa a cikin iyalansa. Amma wannan Tattabara takan zo kowace safiya ta kwanta a kirjinsa.

Tattabarar takan zauna ne na wasu ƴan sa'o'i sai ta tashi ta tafi.

Daga baya na gano cewa wannan mutumin, ya kasance yana zama a wurin shakatawan da ke kusa dasu, sannan yana ciyar da Tantabaru a wurin shakatawar.

Wannan na  nuna mana cewa ko Tantabaru suna jin dadi kuma ba sa mantawa da mutanen da suka kula da su, dakuma yi musu Alkairi.

To dan Haka ƴan uwana, mukasance masu kyautata ma ƴan uwan mu dakuma Al'umma gaba ɗaya. Insha Allahu zamu alfanan hakan. Muhuta lafiya.


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Amfanin Aikata Alkhairi a Rayuwan Duniya"

Post a Comment