Hanyoyi Biyar Da Zasu Taimakamuku Wurin Rage Kiba da Tumbi

Tunbi da kiba

 Assalmu Alaikum yan uwa, barkan da wannan Lokaci. Dafatan wannan karan ma mun sameku cikin koshin lafiya hade da farin ciki me yawan gaske. 

Ayau zamuyi magana ne akan kiba. Ita Kiba wata halittace wanda Allah ya ke halittan muntun da ita. Wanda zakuga mutum yayi fadi dakuma tara kitse a jikinshi. Amma kuma wasu basasan wannan yanayi da Allahbyavhaliccesu da ita. Duk da hakan yakasance baiwane a garesu daga Uban gijinsu. 

Wannan Kiba da dai akwai hanyoyi da dama domun a rageta a cikin jiki. Amma banyi Alkawari idan kabi wadannan hanyoyi zaka rabu da kiba gaba daya ba. Ammade Allah ze taimaka ka rage wani abu daga ciki,  kuma zakaji dadin jikinka.  Domun jin wadannan hanyoyi kubiyomu. 

HANYA TA FARKO

A raje yawan cin abinci, musammam abimci masu maiko irinsu gyada. Sa'annan kuma a yawaita motsa jiki akai akai. 

Kuma yanada kyau a dinga cin gayan itatuwa sosai musamman ganyanyaki irinsu Lansir, Kabeji dakuma Latas. 

HANYA TA BIYU:

Man zaitun hade da shayi shima yana taimakawa sosai. Idan kasama Zaitun mai kyau sai kadinga sashi a cikin shayi cokali daya kacal ba madara. Kasha sau kaman biyu a rana na kwana 30. Insha Allahu za'a a ga canji. 

HANYA TA UKU: 

Asama lemun zaki hade da albasa, a matse ruwansu.  Asaka albasan a cikin ruwan lemun kofi daya acigaba dasha har na tsahon wata biyu. Za'a ga aiki insha Allah. 

HANYA TA HUDU:

 khal tuffa cokali guda a cikin shayi kada asa madara asha sau biyu wuni har na tsahon kwanaki 60. Idankuma kanada Olsa to kada kayi amfani da wannan. 

HANYA TA BIYAR

Ganyen na'ana'a da kuma dakakken garin goruba za'a samu anayin shayi dashi. Se a zuba zuma cokali daya anasha, asha sau biyu a rana. 


CONCLUSION

Lemun Tsami yana matukar taimakawa wurin rage kiba amma inde kasan kana Olsa to ka gujeshi. 

Kuma cin ayaba da safe kafin aci komai shima yana matukar taimakawa. Idan mai Olsa yayi haka to Olsan nashi ma ze nemeta ya rasa da yardan Allah. 


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Hanyoyi Biyar Da Zasu Taimakamuku Wurin Rage Kiba da Tumbi"

Post a Comment