Alamun da Suke Nuni da Cewa Aljani ya Shafi Mutum ko Kuma Anmasa Asiri

Daga Littafin 'ASSARIMUL BATTAR' Malamai daga shafin Sunnah Medicine sun tattaro wasu alamomi da za ka iya gane cewa Aljani ya shafi mutum ko kuma an yi masa asiri domin ka taimaka ma sa.


 

1. Mutum ya zama ba ya son karatun Alkur'ani ko saurarensa

2. Rashin son yin ibada kamar sallah, ko a yi ta cikin bacin rai da kasala.

3. Yawan ciwon kai mai tsanani ko 6arin kai ko kuma jiri.

4. Yawan ciwon mara ko baya ko kwankwaso ko kuma ciki wanda ba ya jin magana kuma an rasa me ke kawo shi.

5. Yawan jin tafiyar wani abu a jiki kamar kiyashi ko tsutsa ko kwarkwata tana yawo a kai amma idan an duba ba za a ga komai ba.

6. Yawan mafarke mafarke na abun tsoro ko firgirta da surutai a cikin bacci ko kuma mutum ya ji wani abu mai nauyi ya danne shi ko ya shake masa wuya.

7. Yawan jin tsoro ko faduwar gaba ko wani abu ya dinga yi ma ka gizo ko kuma ka ji kamar ana kiran sunan ki amma ba za ka mai kiran ba.

8. Yawan jin sanyi ko zafi ko rikewar kafa ko wani sashe na jiki ba tare da wani sanannen dalili ba.

9. Rashin iya bacci da daddare ko yawan jin motsin wani abu ko surutai ko kuma takun tafiya.

10. Rashin son yin kitso ko aski kuma a taba m ka/ki kai.

11. Yawan bacin rai ko jin haushin mutane ba tare da wani dalili ba.

12. Rashin son shiga cikin mutane ko yawan zargin su ko kuma yawa rigima da su.

13. Yawan kuka ko dariya ko murmushi ba tare da wani dalili ba.

14. Yawan jin kamar ana yi ma ka rada a kunne ko a ringa raya ma ka zuciya akan ka aikata wani lefin kamar kisan kai ko zina ko kuma sata

15. Rashin son yin Aure ko korar samari ko kasa tsayar da guda daya kwakwara. Haka ma ga namiji abun ya ke.

16. Daukewar Sha'awa ko rashin jin dadin saduwa da muji ko kuma tsanar sa da wulakan tashi ba tare da wani dalili ba. Shi ma namiji haka zai dinga ji.

17. Yawan kallon mudubi ko Sha'awar kallon tsiraici.

18. Yawan son kade-kade da raye-raye.

19. Yawan son dare ko cikin duhu ko yin shuru kamar ba ka gurin.

20. Rikicewar Jinin Al'da ko na Nifasi ga mace.

21. Rashin Haihuwa ko yawan Bari ko Haihuwar dan babu rai ko kuma wasu matsaloli su biyo bayan Haihuwa kamar jijjiga.

22. Aikata wani abu ba a cikin hankalinka ba, sai daga baya ka ringa nadama ko mamakin yadda akayi ka aikata.

23 Yankewar jiki a fadi kasa ba a cikin hayyaci ba ko kuma ihu da rugawa a guje ba tare da ka san inda za ka ba.

24. Yawan wasuwasi ko mantuwa acikin dukkanin Al'amura musamman a lokacin ibada.

25. Tabuwar kwakwalwa ko kasa fahimtar ko wane irin abu.

26. Rashin tsafta da son zama cikin kazanta da dauda.

27. Yawan fita waje mara dalili ko tarewa a wani wuri kamar karkashin bishiya, kan bola, bandaki, jeji, bakin ruwa, da sauran su.

28. Rashin lafiyar da za'a kasa gane kanta.

29. Rashin son Wa'azi ko zama da mutanen kirki.

30. Yawan jin tsoron Rukuya ko masu yinta. Allahu Ta'ala A'alam

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Alamun da Suke Nuni da Cewa Aljani ya Shafi Mutum ko Kuma Anmasa Asiri"

Post a Comment