Hukuncin Kunya da Amfaninta ga Rayuwar Ɗan Adam Rubutu na Biyu 2

ZUNUBI NA TAFIYAR DA KUNYA

Ibnul Qayyim Allah ya masa rahama yake cewa "Yana daga cikin uqubar aikata zunubi shine tafiyar da kunya wanda kuma kunyan nan itace ruhi na rayuwar zuciya kuma shine ginshikin kowane alkhairi, gushewar sa shine gushewar dukkan alkhairi, ya zo a cikin hadisi Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa "Kunya dukkan sa alkhairi ne"
Abin nufi shine a duk lokacin da mutum ya aikata zunubi za'a rage masa wani ɓangare na kunya har akai matakin da za'a zare kunya gaba ɗaya a cikin zuciyar mutum, sai ya wayi gari baya damuwa don mutane sun san abin da yake aikatawa na saɓo koma su gan shi yana aikatawa, idan har mutum ya kai wannan matakin to lalle shiryuwar sa abu ne mai wuya, irin wannan ne wanda idan shaiɗan ya gan su sai yana cewa "fansa ga wanda ba zai rabauta ba" (shaiɗan da kansa yana masa kirani), haƙiƙa duk wanda ba shi da kunya to tabbas matacce ne a duniya, taɓaɓɓene a lahira, duk wanda ya ji kunyar saɓawa Allah, Allah zai ji kunyar azabtar da shi a ranan da ya koma gare shi, wanda kuma bai ji kunyar Allah ba ya saɓa masa, shima Allah ba zai ji kunyar azabtar da shi ba".

الداء والدواء ١٣١-١٣٣

NAU'UKAN KUNYA

Ibnul Qayyim Allah ya masa rahama yana cewa a cikin littafin sa *_Madarijus salikeen_* "kunya tana da nau'uka guda goma, gasu kamar haka:-

1. Kunya a lokacin da mutum ya aikata laifi, misalin sa shine kamar kunyan da Annabi Adam Alaihissalam yayi a lokacin da ya gudu daga Aljannah bayan ya saɓawa Allah, sai Allah yace masa "Shin gudu na kake ya kai Adam?? Sai yace A'a ya Ubangijina kunyar ka nake ji".

البداية والنهاية ١‏/٧٣

2. Kunya a lokacin da mutum ya gaza akan aikata wani aiki na alkhairi, misali kamar kunya da Mala'iku da suke yiwa Allah tasbihi dare da rana basa gajiyawa ranan ƙiyama zasu ce "tsarki ya tabbata a gare ka bamu bauta maka ba yadda ka cancanta"

السلسلة الصحيحة ٩٤١

3. Kunya ta girmamawa, wanda wannan tana kasancewa ne da ilmi, gwargwadon sanin bawa ga ubangijinsa gwargwadon yadda zai ji kunyar sa.

4. Kunya na karamci, misali kamar kunyan da Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya ji na mutanen da ya gayyato su waliman auren Nana Zainab, bayan an gama cin abinci sai suka zauna anata hira, shi kuma Manzon Allah sai ya ji kunyar yace musu su tafi.

5. Kunya saboda kusanci, misali kamar kunyan da Sahabi Aliyu bin Abi ɗalib Allah ya ƙara masa yarda ya ji game da tambayan Manzon Allah akan Maziyi saboda matsayin yar sa (Nana Fatima) a wurin sa.

Mu haɗu a rubutu na Uku in Sha Allah.Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Hukuncin Kunya da Amfaninta ga Rayuwar Ɗan Adam Rubutu na Biyu 2"

Post a Comment