YIN "ANNIVERSARY WEDDING" MA'ANA MURNAR ZAGAYOWAR RANAR AURE YANA HALATTA A MUSULUNCI?
Assalamu Alaikum
Barka da yamma Mal Muhammad.

Dan Allah menene hukuncin wedding anniversary a musulunci?

Shin Yana daukar hukuncin birthday celebration?

Shin Yana halasta tsakanin mata da miji suyi Dan karamin liyafa a tsakanin su kawai ranar zagayowar aurensu tare da addua ki azumi Koko fita aje wajen cikin abinci a wannan ranar ba tare da anyi Wani Abu makaruhi bakamar daukar hoto a yada a social media Koko wani Abu daya saba wa Allah?
Koko yin abun ya haramta kwata kwata?

       AMSA
Wa AlaikisSalaam:- Toh wannan dai ba ya Halatta ga Musulmin Kwairai yayi wani Abu da ake Kira ANNIVERSARY WEDDING, Domin Koyi ne da Arna Ma'ana Yahudawa da Nasara sune suke yin wannan, wasu Lalatattun Musulmai Kuma suka ganin Suna Amfani da shi.

Lura da Cewa ta kowacce Fuska Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam yace mu Sabawa Yahudawa da Nasara ko da a gurin yin ibadar mu ne, dalilin hakane Annabi ya sa ayi Azumin TASU'A DA ASHURA, a maimakon ayi guda 1. Kenan ta kowanne Fuska shi musulmi Bai kamata ace Yana koyi da Yahudawa da Nasara ba Musamman irin wannan biki-bikin. Sabida a gurin ibadar ki ma Annabi yace ki Sabawa Yahudawa da Nasara, sai a yanzu Kuma ke Kika ga wani Abu na Bikin su ANNIVERSARY WEDDING ya Burge ku ya ba ku Sha'awa yayi muku kyau ku ma kuke CE zakuyi me matsayin ku?

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam yayi Aure ko Bai Yi ba? Matan Annabi 11 Kuma Dukkan su Babu wadda Za'a Ce ai Bai Yi Shekara 1 da su ba dai Mace 1, Shin Manzon Allah ya taba shirya Matan sa yace yau ne ranar ZAGAYOWAR Auren mu mu zauna muyi girki a ci Abinci ayi Addu'a?? Ko Kuma ya ware wani Dandali ya Tara jama'a aka Yi hakan? Ina Sahabban Manzon Allah su ma ai sun Yi Aure, Matan su da Mazan su shin sun Yi Haka? Ina Tabi'ai sun Yi hakan? Duk a Lokacin wato su Kansu Bai waye ba ba su more Rayuwar su ba, yanzu ne Kai ya Waye a more Rayuwa an Gane Sabon ilmi Koh?

Mu dawo kusa Nan Ina Manyan Malaman ku na Addinin, Shin wanne Babban Malami ne Muka taba ji ko gani Cewa Yau Auren sa ya Cika Shekara 1 ya Tara Iyalan sa a Cikin Gidan sa ko ya Kama hotel akayi shagali da sunan ANNIVERSARY WEDDING? Kenan idan ma wani Malami yace Eh ya Halatta to a tambaye shi, shin meyasa shi baya Yi da Iyalan sa ko Yaran sa meyasa baya barin su suyi? Kuma an ce muyi koyi da su waye?

Sabida Haka Rayuwar Arna ne wannan bawai rayuwar Musulmai ba, Kuma Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasalam yace duk Wadda ya dubi wasu yayi koyi da su Ma'ana ki dubi wasu Arna Kika ce abun da Suke Yi ya Burge ki Bari kema kiyi irin Bikin su komai nasu da Sanya suturar, toh Manzon Allah yace a Ranar Alkiyama tare Za'a tayar da ku, Ke ba ki layin inda Manzon Allah yake kina tare da Wadda suke Burge ki Arna.

Sa'annan mu dawo Akan Iyayen mu, ki tambaye Iyayen ki shin su Zamanin su sun Yi irin hakan? Ko Kuma su Kansu, ki tambaye su a Zamanin Iyayen su, sun Yi irin wannan Bikin?? Ko dai a nasu Zamanin Babu Al Qur'ani da Hadisai da Za'a iya gano Cewa ayi irin wannan ANNIVERSARY WEDDING din ne? Ko Kuma babu masu ilmin da zasu iya gone gurin ne? Sai a yanzu ne ilmi ya yawaita aka gano su? Kenan su Kansu Bai waye ba Namu ne ya Waye kawai a more Rayuwa?

Toh wallahi Yana Daya daga Cikin abun da ya sa Auren mu a yanzu ko Yaya akayi ba zai  yi Albarka har a samu Jin dadi da Natsuwa da Farin Ciki Kamar na Iyayen mu ba. Domin su da muke dauka kansu Bai wayen ba, ba su Yi Auren su akan Sabawa Allah ba da ake Yi a Yanzu ba, shin Zamantakewar Auren su Yake da naku?

Amma a yanzu kafin a Daura Auren an Sabawa Allah Party ba irin wadda ba za'a Yi ba, Kauyawa Dance na Yaren ki, ku ce sai an Yi sa duk wani fitsara sai an Yi sa, Amarya ta Sanya sutura irin na Arna suke Sakawa Wedding Gown kina iya ganin duk jikin ta Kai inda ace Za'a Yi iska Mai Karfi zai yare wannan rigar ya bar ta tsirara, su fito suyi Rawa a idon duniya a tashi ayi posting a duk wasu Social media Wai ana Murnar Bikin Aure Za'a Yi Auren wata ne, Amaryar Rawa Miji Rawa Iyayen ta Rawa, ayi ta Sabawa Allah kuma Wai Kuma ana son a Zo a samu Zaman Lafiya da Yara Nagari ta Yaya? Ko Allahn a gidan su yake ai Dole ya Tsalleke su.

Sa'annan a Zo Tsakiyar Auren an Shekara 1 Wai a Zo ana Bikin ANNIVERSARY WEDDING, Nan ma wasu su Kama hotel a je a Kashe kudi a iska a Banza Wai ana Murna ana Taya su Addu'a, Yaro yayi Shekara 1 Wai Suna Bikin birthday nashi Hotunan su ko Ina Yana yawo. Kuma masu Cewa MAULIDI BIDI'A CE su ba su yin Maulidin Amma sune Kuma suke shirya irin wannan abun Sabawa Allah din, shin da yin Maulidin Annabi, da yin Bikin Murnar Ranar Auren ku, da yin Bikin birthday naki ko na Yaran ki, don Allah na waye yakamata ace an dauka ana Yi? Kin ga na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam Bidi'a ce wannan Haramun ne, Amma naku ya Halatta sabida Wai Al'ada ce?

Toh ku ji tsoron Allah, wannan Rayuwar Arna ne yin ANNIVERSARY WEDDING duk wani da koyi da su da ake Yi Bai halatta ba, inda ace kudin da za ku Kashe ko da ace ku biyu ne daga ke Mijin ki misalin ace kuyi shi a Cikin Gidan ku, toh wannan kudin da Zaku Kashe a iska da Makwabtan ku ko wasu mabukata ko ku Kai Masallaci Sadaka da su kuka samu kuka ba su kudin Suka Siya Abinci suka ci da Kun samu Lada Mai tarin yawa, Kuma sai Allah ya Kara muku Budi ya Kara Sanya Albarka ga Rayuwar ku. Ballatana ace Wai kudin da Za'a dauka a je a Kashe su a iska a Kama hotel a dafa Abinci Kala-kala ka ga kayan shaye-Shaye Wai ai ana Murnar ZAGAYOWAR Auren ku Kuma ana Taya su Addu'a. Haka ake yin Addu'a kuyi Azumi Mana ku godewa Allah ga ni'imar da ya ba ku.

Toh maimakon ki samu Lada Tarin Zunubi Za'a Debo, maimakon a samu Yara masu Albarka Kun Riga haifo Yan iska kenan da wadanda ba su Jin Maganar ku, Kai karshe ku gagara iya rike su ko ba su Tarbiyya, ku dawo ku ce Bari ku yi planning domin kada suyi Yawa, Alhalin Sabawa Allah da akayi a baya Sakamakon ku ne ya fito Allah yake nuna muku shi, Amma wallahi ko Yara 100 ne Allah ya ba ku su kuka Haife su, matukar kun Tsara Rayuwar Auren ku daga Farkon nema har Zuwa yin Auren irin Yadda Allah da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam Suka ce ayi, wallahi Allah zai muku hanyar da za ku iya kula da su ko su nawa ne, za ku iya ba su Tarbiyya ku iya Ciyar da su ku iya Biyawa kowa bukatar sa.

Amma wallahi ku Tsara Rayuwar Auren ku irin yadda kuke Yi a Yanzu da yadda Muka Yi bayani ake Yi a Yanzu, to ko Yara 2 ne Allah ya bar ku da su, sai Kun gagara ba su Tarbiyya sai Kun gagara iya kula da su kullum suna yawo a layi. Ai abun ba wayo bane akeyiwa Allah, ki Gama yin family Planning naki Yaro 1 sai ya gagare ki rikewa. Allah ya shirya. A ji tsoron Allah Yan uwa. Fatan kin Gane Koh??

Wallahu A'alamu.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YIN "ANNIVERSARY WEDDING" MA'ANA MURNAR ZAGAYOWAR RANAR AURE YANA HALATTA A MUSULUNCI? "

Post a Comment