Mecece Kunya Hukuncinta da Amfaninta ga Rayuwar Ɗan AdamKunya wani chanji ne da rauni da yake bijirowa mutum na daga tsoron aikata abinda za'a aibanta shi akai.

 Ibnu Allan, Allah ya masa rahama yake cewa "kunya wata ɗabi'ace da take gadar da barin aikata mummunan abu na magana ko aiki, kuma ɗabi'ace da take hana mutum tauye haƙƙin wani mai haƙƙi".

دليل الفالحين ٣/١٥٨

Fadlullahi Al-jailani Allah ya masa rahama yake cewa "kunya wani chanji ne da yake bijirowa mutum a lokacin da ya ji tsoron azargeshi akan wani abu da yake mummuna ne".

فضل الله الصمد ٢/٥٤

KUNYA NA DAGA CIKIN SIFFOFIN ALLAH

    Yana daga cikin siffofin Allah subhanahu wata'ala kunya, kamar yadda ya zo a cikin hadisi ingantacce Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yake cewa "Lalle Ubangijin ku mai kunya ne kuma mai karamci, yana jin kunyan bawan sa ya daga hannu ya roƙe shi har ya sauƙe bai amsa ba".

Fairuzabadi Allah ya masa rahama yake cewa a ƙarƙashin wannan hadisin "Amma kunyan Allah subhanahu wata'ala wani nau'i ne da hankula basa iya riskarsa kuma ba zasu iya kwatanta ta shi ba, kunya ne na karamci da kyauta, domin shi Ubangiji yana kunyan bawan sa ya ɗaga hannu ya roƙe shi har ya sauƙe hannun bai amsa masa ba, sannan yana kunyan ya azabtar da furfuran da ta samu mutum a musulunci".

بصائر ذوي التمييز ٢/٥١٧

RABE-RABEN KUNYA
  Al-Munawi Allah ya masa rahama yake cewa "kunya ta rabu kashi biyu;-

1. Kunya ta ɗabi'a wacce Allah ya dasata a cikin zuƙatan mutane gaba ɗayan su, misalin ta shine; buɗe al'aura a gaban mutane, duk wani mutum mai cikakken hankali yana kunyan ya bude al'auran sa a gaban mutane, haka saduwa da mace afili.

2. Kunya ta imani wanda shine mutum musulmi ya kame daga aikata abinda Allah ya haramta saboda tsoron sa".

التوقيف على مهمات التعاريف ١٥٠
 
Duka nau'ka guda biyu na kunyan nan an haɗawa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama su, a kunya ta ɗabi'a Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yafi budurwar da take cikin haudajin ta kunya, a kunya kuma na imani Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya kasance shine mafi ƙololuwa awannan ɓangaren.

Mu haɗu a rubutu na biyu in Sha Allah


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Mecece Kunya Hukuncinta da Amfaninta ga Rayuwar Ɗan Adam"

Post a Comment