Fa'idar Kunya ga Rayuwar Dan Adam Rubutu na Uku 3



Ci gaba da bayani akan nau'ukan kunya guda goma da ibnul Qayyim Allah ya masa rahama ya kawo, a darasi na biyu mun kawo guda biyar, wanda yanzu zamu ɗora in Sha Allah.

6. Kunya na ƙanƙan da kai, misalin irin wannan kunya shine mutum ya ji kunyar rokon Allah buƙatun sa, wanda irin wannan kunyan abubuwa biyu ke haifar da shi;-

A. Bawa ya ƙanƙantar da kansa saboda girman zunuban sa.

B. Ganin girman wanda zai roƙa, wanda shine Allah mai girma da ɗaukaka.

7. Kunya ta soyayya, wanda wannan shine mutum ya ji kunyar wanda yake so.

8. Kunya ta bauta, wanda wannan kunyar tana ƙunshe ne da soyayya da kuma tsoro, bawa a lokacin da yake bautar Ubangijin sa zai kasance yana jin kunyan Ubangiji domin girman Ubangijin ya wuce wannan bautar da yake, sannan yana kunyan shin yana mai yin bautar yadda zata burge Ubangijin.

9. Kunya ta daukaka da sharaf  shine mutum ya ji kunyar yin abin da bai kai martabar sa,

10. Kunya ta kai da kai,  shine mutum ya ji kunyar kansa a lokacin da ya aikata wani abu na kasƙanci .

مدارج السالكين ٢/٢٧٢

KUNYA BATA HANA DA'AWA (WA'AZI)


   Kunya ta gaskiya bata taɓa hana yin umarni da kyakkyawan aiki ko hani da mummunan aiki.

  Fadlullahi Al-jailani Allah ya masa rahama yake cewa "Idan aka ce mutum mai kunya zai ji kunyar fuskantar gaskiya hakan yasa ya bar umarni da kyakkyawan aiki da hani da mummunan aiki, kuma kunya zata sa ya tauye wasu haƙƙoƙin,
Ni kuma sai in ce musu; lalle wannan ba kunya bane, ragwantaka ne da tsoro, kawai sun gagara banbance tsakanin ragwantaka ne da kunya yasa suke kira wannan da kunya.

Kunya ta gaskiya itace munin abinda ake jin kunyar sa haƙiƙatan, don haka abinda mutane suke ƙyamata idan mai kyau ne ba zai shiga wannan babin ba, misalin wannan shine kamar macece kwarto ya shigo mata gida, sai tace tana jin kunya ba zata yi ihu ba saboda kada mutane su ce wacce ai kwarto ya shiga mata gida, idan da zata hankalta zata ga cewa ihun da zata yi ba wani abun kunya bane idan akayi muƙaranan sa da kuma barin kwarton da zata yi ya keta mata haddi, don haka anan kunya ta gaskiya shine tayi ihu yan uwa su zo su kawo mata ɗauki.

   Ya tabbata cewa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yafi budurwa da take cikin haudajinta kunya, wanda kuma shine abun koyi a gare mu amma duk da haka ransa baya ɓaci har sai ya ga an saɓawa Allah, wanda wannan ke nuna mana cewa kunya bata hana da'awa".

فضل الله الصمد ٢/٦٩٢

Mu haɗu a rubutu na huɗu in Sha Allah

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Fa'idar Kunya ga Rayuwar Dan Adam Rubutu na Uku 3"

Post a Comment