AMFANIN ZUMA DA QIRFA (HONEY AND CINNAMON) GUDA GOMA SHA BIYAR



Tun azal mutane sun kasance suna amfani da zuma dan ganin muhimmancinta ta fannin kiwon lafiya da magance cutukka,sai dai kuma amfani da kirfa daga bayane ilmin ya samu musamman ma anan Afrika.

To kowane daga ciki,qirfa da zuma din da muke magana akai da irin muhimman sinadiran da yake dauke dasu da kuma irin muhimmiyar rawar da yake takawa ta daqushe wasu qwayoyin cuta da kuma inganta lafiyar jiki.

An dauki shekarru a wasu kasashe ana hada garin qirfa(cinnamon powder) da zuma dan yin maganin wasu cutuka musamman ma a Turai da India da wasu kasashe na Larabawa.Sannu a hankali masana harkar magani sun fadada bincike dan gano ainihin shin ko hada qirfa da zuma ya dace ? Sannan wane irin maganine su ke yi idan aka hadasu ?

Ga wani bincike na musamman da qirfa da zuma ke yi -


1-Arthrities - za a hada cokali daya na garin qirfa da cokali biyu na gangariyar zuma a cikin ruwan dumi cup daya sai a sha safe da yamma tsawon sati biyu.

2.Bladder infection -Mai fama da rashin lafiyar da ta shafi bladder
sai ya nemi garin qirfa cokali biyu sai ya gauraya da cokali daya na zuma ya zuba a cikin cup daya a cikin luke warm water sai ya jira su huce ya sha.zai warkar masa da cutukan mara.

3.Cholesterol  -Cokali biyu na garin qirfa a gauraya da ruwan dumi sai a sha safe da yamma wannan ba sai an saka zuma ba.

4.mura- Sai a gauraya rabin cokali na garin kirfa da rabin cokali qarami na zuma sai a jefa citta a tafasa da kyau a sha idan za a konta ko idan an tashi bacci da asbah.

5.Heart diseases - A gauraya zuma dan qaramin cokali a tareda garin qirfa rabin karamin cokali sai shafa wa biredi marar suga sai a ci fa safe,a karya da shi sai a sha ruwan dumi.A rinka haka tsawon wata daya.
Za a yiman addu 'a.

6.Gas - A sha zuma da garin kirfa cokali daya bayan an karya,yana maganin yawan gas.

7.Boost immunity-karfafa garkuwar jiki- sai a rinka shan kirfa a saka 1/4 na qaramin cokali na cinnamon a cikin ruwan dumi cup daya sai a jefa lemun zaqi daya a ciki.A fara karyawa dasu.

8.qabewar ciki - A sha garin cinnamon a tare da ruwan zafi cup daya bayan an tafasa kirfa sai a tarfa zuma amma sai bayan sun huce.sai a sha.za a warke cutukan ciki.

9.Rashin narkewar abinci
(poor digsetion) sai a sanya rabin cokali na cinnamon powder a cikin ruwa a tafasa da kayu sai a tarfa zuma cokali biyu a sha kamin aci abinci.

10-Choronic fatique-Idan ka jima kana fama da kasala a jiki ko kana jin kamar bakada karfin jiki to sai  ka rinka yin shayin cinnamon kana sha amma arinka matse lemun zaqi aciki kada a saka zuma sai a sha da safe kamin aje exercise.

11.Pimples - kurajen fuska sai a gauraya cinnamon powder da zuma a shafe huska idan za a kwanta washe gari sai a wanke fuska da ruwan dumi.

12-Rage qiba -weight loss- cokali daya na cinnamon sai a tafasa a cikin cup daya na ruwa sai a tarfa cokali biyu na zuma sai a gauraya a sha a sanda za a kwanta haka kuma da safe.

13-Hearing Loss-cokali daya na cinnamon a cikin cup daya na ruwa sai a saka diyan lemu a tafasa ko ayi yi tea a saka cokali daya na zuma a sha.

15.Negative thouht-Idan kana yawan tinani harnba barkata to ka rinka shan kirfa a tare da zuma da kuma cokali daya na ruwan kwakwa.

GARGADI:- Idan za a yi amfani da cinnamon to sai a nemi Organic ceylon cinnamon ita ce mafi kyau da inganci kuma bata haddasa wata matsala duk,haka itama zuma a nemi gangariyar zuma ba mai gauraye da suga ba.

Kada ayiamfani da cinnamon na dogon lokaci dan akoi wasu yan matsalaoli da take ita haddasawa.

Always share and Like.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "AMFANIN ZUMA DA QIRFA (HONEY AND CINNAMON) GUDA GOMA SHA BIYAR"

Post a Comment