Falalar Kunya a Rayuwar Dan Adam Rubutu na 4

DAGA INA AKE SAMUN KUNYA


Junaidu Allah ya kara masa rahama yake cewa "Kunya shine dubi zuwa ga Ni'ima da kuma dubi zuwa ga gazawa sai a samu kunya a tsakanin su"

رياض الصالحين ٢٤٦

Ma'anar wannan magana tashi shine "mutum yayi dubi zuwa ga girman Ni'imar da akayi masa, sai kuma yayi dubi zuwa ga gazawa da yayi wurin bada haƙƙin wanda ya masa wannan Ni'imar, to anan ake samun kunya.

    Abul Fida, Isma'il Alharawi Allah ya masa rahama yake cewa "ana samun kunya ne a cikin girmamawan da yake chakuɗe da soyayya"

مدارج السالكين ٢/٢٧٤

Ibnul Qayyim Allah ya masa rahama yake cewa a ƙarƙashin wannan magana ta Abul Fida; babu cin karo tsakanin maganganun duka domin ita kunya tanada sabubba da yawa, kowane ɗaya daga cikin su yayi nuni ne akan wani sashi nata".

مدارج السالكين ٢/٢٧٤

KUNYA TUSHENE NA DUKKAN ALKHAIRI

Ibnul Qayyim Allah ya masa rahama yana cewa "Kunya ɗabi'ace da tafi kowacce ɗabi'a alkhairi da falala da girma, kuma tafi kowacce ɗabi'a yawan amfani, bal ma itace ɗan a damtaka na mutum, a lokacin da mutum ya rasa kunya to ya kasance shi ba komai bane face tsoka da jini kawai abisa tsarin mutum, kamar yadda kuma ya kasance ba shi da wani alkhairi atattare da shi, da badan kunya ba da ba'a aikata wani aiki na alkhairi ba, ba za'a cika alkawari ba, ba za'a mayar da amana ba, ba za'a nisanci alfasha ba.

  Ɗan adam yana da masu ba shi umarni da tsawatar masa guda biyu, na farko shine mai masa umarni da tsawatarwa ta ɓangaren kunya, idan ya masa biyayya sai yakame daga aikata abinda yake ya saɓawa muru'a.

    Na biyu kuma mai masa umarni da tsawatarwa shine ta ɓangaren son zuciya da ɗabi'a, dan haka duk wanda ya bijirewa umarni na kunya to ba makawa zai bi umarnin son zuciyarsa".

مفتاح دار السعادة ٢٧٧

Mu haɗu a rubutu na biyar, in Sha Allah

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Falalar Kunya a Rayuwar Dan Adam Rubutu na 4"

Post a Comment