KUNYA ADO RUBUTU NA 6




HADISAN DA SUKA ZO AKAN FALALAN KUNYA:-

HADISI NA HUƊU:-Sahabi Salman Alfarisi Allah ya ƙara masa yarda yake cewa; Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace "Lalle Ubangijin ku mai kunya ne kuma mai karamci, yana jin kunyan bawan sa ya daga hannu ya roƙe shi amma ya bar hannayen su koma zero ba tare da ya amsa masa ba"

سنن أبي داود ١٤٨٨

HADISI NA BIYAR:- Sahabi Ashajji Abdul Qaisi Allah ya ƙara masa yarda yake cewa; Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yacemini "lalle Kana da wasu halaye guda biyu da Allah yake son su" sai nace waɗanne ne ya Manzon Allah? Sai yace mini "juriya da kunya" sai nace ya manzon Allah shin waɗannan halayen sun jima atattare dani ne ko kuma yanzu na same su?? Sai Manzon Allah yace "A'a ka jima da su" sai nace "godiya ta tabbata ga Allah da ya halicceni da halaye da yake so"

سنن ابن ماجه ٤١٨٨

HADISI NA SHIDA:-  Sahabi Anas bin Malik Allah ya ƙara masa yarda yana cewa; Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace "Lalle kowane Addini yana da ɗabi'a, ɗabi'ar musulunci shine kunya".

سنن ابن ماجه ٤١٨١

HADISI NA BAKWAI:-  Sahabi Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda yace; Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace "Imani yana da ɓangarori saba'in da yan kai, mafi ƙololuwa shine faɗin la ilaha illallah, mafi ƙanƙanta kuma shine kawai da abinda zai cutar da mutane akan hanya, kunya wani ɓangare ne na imani".
صحيح مسلم ٣٥

HADISI NA TAKWAS:- Sahabi Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda yake cewa; Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa "Kunya tana daga cikin Imani, shi kuma imani yana kai mutum zuwa ga Aljannah, shi kuma rashin kunya yana daga cikin jafa'i, shi kuma jafa'i yana kai mutum zuwa ga wuta".

سنن الترمذي ٢٠٠٩

Mu haɗu a rubutu na bakwai in Sha Allah

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "KUNYA ADO RUBUTU NA 6"

Post a Comment