AMFANIN KUNYA RUBUTU NA 7





HADISAN DA SUKA ZO AKAN FALALAN KUNYA:- 3

HADISI NA TARA:-Sahabi Abdullahi bin Umar Allah ya ƙara masa yarda yake cewa; Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa "Kunya da Imani an hada su ne a tare, idan aka ɗauke ɗaya to ɗayan ma zai tafi".

مستدرك حاكم ١/٢٢

HADISI NA GOMA:-Sahabi Abu Umama Allah ya ƙara masa yarda yake cewa; Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa "Kunya da ƙarancin surutu halaye ne da suke cikin Imani, amma rashin kunya da kuma yawan surutu halaye ne da suke cikin munafurci".

سنن الترمذي ٢٠٢٧

HADISI NA GOMA SHA ƊAYA:- Sahabi Imran Bin Hussein Allah ya ƙara masa yarda yake cewa; Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace "Kunya bata zuwa face sai da alkhairi" sai bushair bin ka'ab yake cewa "ai ya zo ma a cikin hikima cewa; lalle a cikin kunya akwai nutsuwa da kwanciyar hankali, sai Imran Bin Hussein yake ce masa "ina ce maka Manzon Allah yace kai kuma kana kawomin abin da ke cikin sahifar ka??".

صحيح البخاري ٦١١٧

HADISI NA SHA BIYU:Sahabi Anas Allah ya ƙara masa yarda yake cewa; Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa "Rashin kunya ba zata kasance a cikin wani abu ba face ta ɓata abun, haka kuma kunya ba zata kasance a cikin wani abu ba face ta ƙawata wannan abun".

سنن الترمذي ١٩٧٤

HADISI NA SHA UKU: Sahabi Abdullahi bin Umar Allah ya ƙara masa yarda yake cewa; wata rana Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya wuce ta wani mutum sai ya ji yana yiwa ɗan uwan sa wa'azi akan kunya (kunyar sa tayi yawa ya rage) sai Manzon Allah yace masa "ƙyale shi domin kunya tana cikin imani".

صحيح البخاري ٦١١٨

Mu haɗu a rubutu na takwas in Sha Allah

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "AMFANIN KUNYA RUBUTU NA 7"

Post a Comment