AMFANIN MAN KADANYA GUDA UKU 3 (SHEA BUTTER)Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu,yan uwa na barkan mu da warhaka a yau muna dauka da bayani ne akan amfanin man kadanya wanda da dama wasu basu san amfani mn sa ba,gani suke kawai kamar magance kaushin kafa yake.

Eh! Haka ne yana magance kaushin kafa mma amfanin sa ya wuce nan don man kadanya bincike ya nuna ya dauke da Bitamin A da E don haka yana taimakawa fata sosai wajen hana ta kamuwa da kuna warkar da cututtukan da suke fitowa a tare da ita.

YADDA ZAA MAGANCE MAKERO.

1. Man kadanya
2. Man zaitun

Ana hada man kadanya da man zaitun a kwaba sosai a rika shafa shi a duk inda makero ya fito.

YADDA ZAA MAGANCE KYASBI:

1. Man kadanya
2. Man Habbatussauda
3. Nan kwakwa

Duk a hada waje guda a kwaba a rika shafawa a duk inda suka fito sfima wannan yana magance natsalar kyasbi a jikin mutum .

YADDA ZAA MAGANCE KURAJEN ASKI:

1. Man kadanya
2. Man ik'lil jabal (Roseberry)
3. Man kwakwa

Shima a hade su waje guda a rika shafawa a inda kurajen suka fito,bayab kashe su da sinadaran zasuyi har kyau baki da laushi zasu sa gashin wajen yayi.

Wadannan sune kadan daga cikin amfanin man kadanya.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "AMFANIN MAN KADANYA GUDA UKU 3 (SHEA BUTTER)"

Post a Comment