Hira Tsakanin Miji da Mata: Hiranda be Dace Kima Mijin Ki Ba





Maza da dama suna gudun yin hira da matansu ne saboda rashin iya amfani da kalamai a wajen wasu matan. Hakan yasa za kaga magidanci ya bar matarsa a cikin gida ya fito majalisa yana hira da abokai. Ga wasu irin hirarrakin da duk dadin zancenki kada ki yiwa mijinki su.


1πŸ’•: Duk yadda 'yan uwan mijinki da abokansa suka tsaneki. Kada ki taba furtawa mijinki kin tsanesu.

A kullum kada ya taba jin wasu mugayen kalamai daga bakinki zuwa garesu koda kuwa a bayan idanuwansa kina fada.

2πŸ’ž: Duk yadda mijinki zai yi dake kada ki taba yiwa mijinki labarin zinar da kika yi da wasu mazan kamin ki aureshi.
Koda yasan kina zina ko kin tana zina, kada yaji cikenken hira daga gareki na yadda kikayi zina da wasu a baya.

Amsa mafi sauki da duk wata macen da take son nonuwa namiji ta taba zina shine ta sanar da shi budurcinta an kawar. Daga nan kuma babu wani karin bayani.

3πŸ’•: Koda giya kike sha kada ki nunawa mijinki gazawarsa kai tsaye. Idan akwai ta inda ya gaza samu wasu hanyoyin da zaki iya fahimtar da shi ya gane cikin sauki amma ba ki fito karara ki fadamasa gazawarsa ba.

5πŸ’ž: Kada ki taba nunawa mijinki bacin ranki akan wani al'amari na kudi da ya hanaki ko bai baki a wadace ba.
Maza sukan iya daina yiwa mace kyauta ma gaba daya idan ta cika mita akan a bata ko an bata ba yawa.

6πŸ’•; A kul dinki kika furtawa mijinki tsana da wasu 'yan uwanki ko iyayenki suke masa.
Dauki wannan lamarin tsakanin kedasu ne, amma kada ki sake ki yiwa mijinki hiran hakan.

7πŸ’ž: Mata da dama suna da halin taso da abunda ya riga ya wuce a lokacin da suke hira da mazansu.
Kada ki sake ki dauko hiran wani matsala da kuka taba samu a baya, koda kuwa hiran da kuke yi ya shafe hakan.

8πŸ’•: Ki kiyaye kokarin nunawa mijinki so kike ya kasance yadda kikeso.
Maza akwai kifadi. Wani daga ranar da ya fahimci so kike ki rika juyashi yadda kike so, daga wannan lokacin zai daina miki duk wani abunda yasan kina so.

9πŸ’ž: Ki guji yiwa mijinki hiran wani abunda ya hanaki amma daga baya kika aikata abun.
Da zaran kinyi karambani fadamasa wannan abun, daga lokacin ya daina yarda dake.

10πŸ’•: Ki tabbatar da sai lokacinda mijinki ya nemi shawara akan abokansa ko 'yan uwansa kamin ki masa maganansu.
Kada sabar iyaye da neman waje kice zaki nunawa mijinki yadda zai kula da 'yan uwansa ko kuma abokansa. Muddin suka fahimci kina da ruwa a wasu abubuwan da ake musu. Har wanda ba a musu ma zasu ce kece kika hana ayi musu.

Ba wai maza basa son zama hira ne da matansu a gida ba. Matan ne basu iya zaben kalaman da zasu yiwa mazansu hira dasu ba. Mata da dama banda lissafowa mazansu babu, shine suka fi kwarewa idan suna hira dasu. Wasu kuwa banda kawo kara da korafi basu iya hira ba. Muddin zaki kasance macen da ta iya hira da mijinta, to ko majalisa ya kama dole sai ya leka, tare zaku saboda kada ma yaje ya dade bai dawo miki ba.

Da fatan mata zasu koyi yadda ake hira da miji.


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Hira Tsakanin Miji da Mata: Hiranda be Dace Kima Mijin Ki Ba"

Post a Comment