Meke Jawo Gyambon Ciki (ULCER)
Cutar Ulcer shine samuwar kurji ko gyambo acikin daya daga cikin bangarorin hanjin mutum, Sababin haka kuwa shine.
 
1. Damuwa irinta rayuwa.

2. (Gastro intestine) wato yayin da sunadaran da suke diga a cikin hanji don narkewar abinci sukayiwa, suna iya samarda Ulcer.

3 Amfanida tukwane ko kwanukan alminium wayanda ake wankesu da soson karfe, wato birbishin aluminium din dake makalewa ajikin kwanon, shima yana kawo Ulcer
4 Wani likita yana cewa, abinda ake kankarewa ajikin recherge card yana kawo Ulcer idan akaci abinci batareda an wanke hannuba.

5 Yawan amfanida abinci ko abinsha mai tsananin sanyi ko zafi.
6 Rashin tsabtace abinci ko abinsha, domin akwai wasu kwayoyin halittu kanana wayanda suke iya rayuwa ajikin mutum kuma har suyi tasiri a hanjinsa.

Manzon ALLAH S.A.W yana cewa Tsabta tana cikin Imani!!!

Maganin Ulcer mafi shahara da tasiri da yaduwa acikin littattfan likitancin musulunci suka ambata shine.
Ana hada Zuma (Honey) da garin Habbatus Saudah (Negela Sativa) da garin bawon Rumman (Pomgrenate) sai a hadasu a guri guda arika shan cokali 2 sau 3 a kullum.
Idan Ulcer din takai nau'i na karshe daga nau'ukan Ulcer wato (Papetic Ulcer) ana gane wannan nau'i ne yayinda akayi gyatsa sai aji warin jini.
idan Ulcer takai wannan mataki, sai akara garin yayan KUMASARI (Pear) awancan hadin da muka fada.

ALLAH S.W.T yana cewa (Inda zaku kirga ni'imomin Allah to! bazaku iya kididdige su ba)


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Meke Jawo Gyambon Ciki (ULCER)"

Post a Comment