SALLAN KASRU (QASRU) DA YANDA TAKE KASANCEWA GA MATAFIYI



Malam Ina son Bayani Akan sallar Qasru?

Amsa
An shar’anta wa matafiyi yin qasarun sallloli masu raka’a hudu (Azzahar, La’asar,Isha)zuwa raka’a biyu,haka kuma zai iya hada sallar azzahar da la’asar,margarita da isha,saboda fadin Allah
Madaukakin Sarki : (Idan kuka yi tafiya a bayan qasa to babu laifi a kanku ku rage (qasaru) sallah,in kuna jin tsoron kada wadanda suka kafirta su fitine ku,haqiqa kafirai maqiyanku ne masu bayyana qiyayya)
An nisa’i aya ta 101
Da abin da ya tabbata daga Anas Dan Malik–Allah ya yarda da shi – ya ce, “Mun fita tare da Manzon Allah (S.A.W) daga Madinah zuwa Makkah,ya kasance yana mana sallah raka’a bibiyu,har muka dawo”
Nasa’i ne ya rawaito shi.
Abin Da Ake Nufi Da Tafiya
”Ita ce duk tafiyar da za a kirawo ta tafiya a al’adance,to wannan tafiya za a yi mata qasaru

 
Malam Minene matsayin Sallar Qasru A matafiyi shin farillah ce ko Sunnah ?

Amsa
An samu sabani tsakanin Malamai akan cewa sallar kasaru Ruksa ce wato mutum na da zabi akan ya yi ta ko kuma ya cika sallah. ko Azima wato dole mutum yayi ta bai da zabi. To anan Imamiyya da Hanafiyya sun tafi akan cewa Azima ce,wato in dai tafiya ta kama mutum,kuma ta cika sharuddan sallar kasaru,to dole kasarun zai yi. Amma a mazhabar malikiyya, shafi’iyya da Hanbaliyya sun tafi akan cewa sallar kasaru Ruksa ce, wato a tafiya a wajensu mutum na da zabi ko yayi kasarun ko ya cika. Amma duka mazahabobin sun yi ittifaki  akan cewa sallah mai raka’a 4 ake ma kasaru wato sallar zuhur,asar da kuma isha’i,sallar magriba da kuma asuba su ba a yi masu kasaru


Malam Mike yanke ma mutun Sallar Qasru?

Amsa
Sallar kasaru tana yankewa a waje uku sune:

1. Mutum yabi ta garinsu,wato idan mutum na tafiya misali ya fito daga wani gari zashi wani gari to idan ya biyo ta garin da yake zaune,to a garin nasu kasaru ta yanke masa har sai ya bar garin ya ci gaba da tafiya.
2. Ko kuma yaje wani gari da niyyar zai kwana goma a garin to shima kasaru ta yenke masa.
3. Taraddudi a waje guda har tsawon kwana 30

Malam Minene hukuncin yin NAfila ga Mae yin sallar Qasru?

Amsa
Sallolin nafilfili na sallar Azahar da La’asar sun fadi kan matafiyi wato ba zai yi su ba,amma na sallar Magariba da Isha’i da kuma Asuba zai yi su,a takaice dai nafilfili na yini ne ba zai yi ba,amma nafilfili na dare kamar sallar Tahajjud duka zai iya yi.Domin ana son ko wace rana in dai mutum ba yana halin tafiya bane ya zamanto yana sallah raka’a 51,kuma lizimtar wadannan raka’oi 51 yana daga cikin alamomin mu’umini,kamar yadda yazo a hadisi daga Imam Hasan al-askari

Allah yasa mu dacee

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "SALLAN KASRU (QASRU) DA YANDA TAKE KASANCEWA GA MATAFIYI"

Post a Comment