Ingantaccen Maganin UlcerGA MASU FAMA, DOMIN AZUMIN WATAN RAMADAN:

Da farko dai muna yi maka fatan alkhairi da fatan Allah ya baka lafiya daga dukkan abinda ke damunka.

Akwai abubuwa da dama a likitancin Musulunci wadanda sukan magance irin wannan ciwon in sha Allahu. Kamar yadda bayanai suka gabata anan Zauren Fiqhu. Ga wasu nan kamar haka :

KAYAN HADI
:

1. Ka samu Garin Kustul Hindi cokali 7, garin Shammar cokali 7, Garin Habbatus sauda cokali 7, garin Kirfa cokali uku. Ka gaurayasu baki daya acikin zuma mai kyau (Farar saqa).

Zaka rika shan cokali uku safe da rana da yamma har tsawon kwanaki 30.

2. Man Tafarnuwa, Man Habbatus sauda, Man Jirjir, Ka hadasu waje guda. Sannan ka samu shayin Na'a-Na'a mai kyau, Ka rika zuba wancan hadadden man cokali 2 acikinsa kullum da safe ka rika shansa da zuma.

LOKACI:

Zaka sha har sati biyar (5 weeks).  in sha Allahu zaka samu waraka daga Matsalar da ta shafi hanji kamar:

- Typhoid Fever (Zazzabin hanji).
- Ulcers (wato Olsa, gyambon ciki).
- Indigestion (wato Magwas).
- Appendicitis (Tsakuwar ciki).
- Majinar Qirji, da Majinar ciki.
- Piles (Basur mai sa kumburin ciki, ko kaikayin dubura).

3. ZAM-ZAM : Kasami Zamzam + Zuma Ka zubata acikin ruwan zam-zam ka rika sha kullum har sati uku.

In sha Allahu zaka samu waraka daga abinda ke damunka ko menene, albarkacin Alqur'ani.

Allah ya sawwake, Allah shi baka lafiya tare da dukkan Musulmai masu jinya.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Ingantaccen Maganin Ulcer "

Post a Comment