Hukuncin Kallon Fina-Finai Na Rashin Da'a a Musulunci

TambayaMalam Ni inada Mata amma idan ban Kalli bad firm bah banajin sha'awa bare na iya biyama matata buqatar ta, malam minene hukuncin kallon dana keyi ?

Amsa

Baya hallata ga musulumi kallon fina-finan da ake nuna tsiraici, ko hutunan da ke baiyyana tsiraici, ko kallon tsiraicin a zahiri, mutum shi kadai ne ko tare da matarsa ta Sunnah. Al-kur’ani mai Girma yana cewa a cikin suratun-nur: ‘ Ka fadama muminai maza su rintse idanuwansu kuma su tsare farjinsu. Wannan shi ne yafi tsarki agaresu, kuma Allah mai bada labarin abin da suke aikatawa ne. Kuma ka fadawa muminai mata su ruitse idanuwansu kuma su tsare farjinsu…’

(قل للمؤمنين يغضوا من أبصارهم ويحفظوا فروجهم ذلك أزكى لهم إن الله خبير
بما يصنعون* وقل للمؤمنات يغضضن من أبصارهن ويحفظن فروجهن…) [النور:
30/31].
Wannan umurnin Allah ne ga duk wani mumini, don haka musulmin kwarai ya rintse idon sa daga kallon tsiraici wajibi ne. Babu sabani acikin haka agorin magabata.

Kallon tsiraici yana kekasar da zuciyar mutum, kuma yasa shi yazama raukananne ga barin Allah da ambatonsa. Kamar yadda yake gadar da ciwukan zuciya da na ruhin dan-adam, sannan kuma ya nisantar dashi daga halal kuma ya kusantar da shi zuwa ga haram da muyagon ayyuka.

Ya ku ‘yan-uwa magidanta, Annabi (SAW) ya yi umurni da suturta tsiraici kuma ya yi hani da bayyana tsiraici ko kallon tsiraicin. Sabo da bala’in da dake cikin hakan.

Ba ya hallata ga wani yaga tsiraicin wani saidai ma’aurata, ko akan matsananciyar lalura. Amma abinda magidanta ke fakewa da shi na kallon fina-finan batsa da tsiraici- wai cewa suna koyon salon jima’i da hanyoyinsa ko kuma su ce, yana mutsar da sha’awarsu- to wannan ba zai taba zama hujja a gorin Allah ba, domin sabawa umurninsa ne.

Kallon fina-finan batsa da tsiraici tafarkin shedan ne, yana amfani da shi don halakar da magidanta. Al’hali kuma Allah da Manzon sa, sun yi umurni da rintse ido daga kallon tsiraici.

Duk wasu magidanta da ke kallon fina-finan batsa da tsiraici, to su tuba zuwa ga Allah, kuma su bari, tun kafin mutuwa ta riske su.

Allah yasa mu dacee


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Hukuncin Kallon Fina-Finai Na Rashin Da'a a Musulunci"

Post a Comment