FALALAR ƘWANAKI GOMAN NA WATAN (ZHUL-HIJJA)        DARASI NA 001

Hakika Falalar Waɗannan Ƙwanaki Goma Na Watan ZHUL-HIJJA ya Zo a Cikin Al Qur'ani Mai Girma, da Kuma a Cikin Hadisin Manzon Allah Sallallahu Alaihin Wasallama Ingantaccen Hadisai, Za Mu Kawo Kaɗan Daga Cikin Waɗanda Suka Zo a Cikin Al Qur'ani Mai Girma:

Allah Maɗaukakin Sarki Yana Cewa a Cikin (Surah ta 22 a Cikin Suratul Hajji), ((Kayi Shela Wa Mutane Gameda Aikin Hajji, Za Su Zo Maka Suna Masu Tafiyar Kafa da Kuma Akan Abin Hawa, Za Su Zo Daga Kowanne Lungu Da Tsako Ko Sako Domin Su Halarci Amfani Nasu Sannan Kuma Su Ambaci Allah a Cikin Ƙwanaki Sanannu))._ _Sahabi Abdullahi ɗan Abbas Yake Cewa a Karkashin Wannan Ayar Ƙwanaki Sanannu Sune Ƙwanaki Goma na Farko na Cikin Watan ZHUL-HIJJA.

Allah Maɗaukakin Sarki Yana Cewa ((Allah Yana Rantsuwa da Alfijir, Sannan Yana Rantsuwa da ɗarare Goma)) Imam Ɗabari yake Cewa a Karkashin Tafsirin Wannan Ayar, Ɗarare Goman Sune na Farkon Watan ZHUL-HIJJA, Sabida Ijma'in Malaman Tafsirin Akan Haka Suka tsaya, Hakanan Shima Imam ibn Kathir ya Faɗa a Tafsirin sa na Wannan Ayar Cewa Sune Ɗararen Farkon na Cikin Watan ZHUL-HIJJA, Kamar Yadda Aka Ruwaito Hakan daga Abdullahi ɗan Abbas da Zubairbda Mujahid da ma Sauran Salaf da Ƙhalaf.

Daga Nan Zamu Iya Fahimtar Cewa Ƙwanaki Farko na Watan ZHUL-HIJJA Suna da Falala Wadda take a Bayyane Daga Cikin Ayoyin Al Qur'ani Mai Girma ta Yadda Allahu SWT ya Kira Su da Ƙwanaki Sanannu, Don Girman Falalar Su da Matsayin Su a Wajen Allah.

Sannan Kuma Akwai Hadisai Masu tarin Yawa da Suka Zo Daga Manzon Allah Sallallahu Alaihin Wasallama Game da Falalar Waɗannan Ƙwanaki Goma na Farko na Cikin Watan ZHUL-HIJJA.

Mu Haɗu a Rubutu Na Gaba Insha Allahu.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "FALALAR ƘWANAKI GOMAN NA WATAN (ZHUL-HIJJA)"

Post a Comment