Jinin Haila: Abubuwan da Yakamata Kisani Dangane da Al'adar ki1- DARASI NA FARFO 01

KAFIN NA FARA BAYANIN JININ HAILA, YAKAMATA NA JA HANKALIN YAN UWANA MATA MUSAMMAN YAN MATA DA IYAYEN SU. DARASI NA 1&2 DUK FADAKARWA CE WADDA ZAI AMFANE KI

Domin an Fi mayar da hankali yanzu akan su Kan komai Matan ne Yan Mata ne wasu har tambaya suke Yi a group Wadda ba su tambayar Wa'azin wani Malami sai Wannan.

Ya Ke Ƴar Uwa Musulma Mai Son Shiga Aljannah, Wadda ta ke son Allah ya Amsa ibadun ta, Wadda ta ke Son Allah ya so ta, Wadda ta ke Son Allah ya Sanya Rahama Zuwa Gare ta, toh Wallahi wallahi ku Ji Tsoron Allah wajen ɗena Ɓata Lokacin ki a Karance-Karancen Banza da ofi na Littafin NOVELS da Littafai na Karya, Kagaggun Labarin Karya wai Domin Nishaɗi Ko Domin Faɗakarwa ga Ƴan Uwa Musulmai. wallahi Babu Inda Littafin Karya ya Zama Shine Littafin Wa'azin da Zai Shiryar da Musulmi. babu Shi inda ace Allah da Manzon Allah ba su Haramta Karya ba, toh da nan ne Kaggaun Labarin Karya zai iya Zama Nasiha Ko Wa'azi. Kuma sa an Yi Annabi Mai kaigo Karya.

Babu Yadda Za'a a Kirkiro Labarin Karya Ace Shine Za'a yi Wa'azi da shi ko Nasiha, Annabi Sallallahu Alahin Wasalam yana Cewa Wallahi ya isa Mutum tashin Hankali, da Azaba Mafi Tsananin Azaba mai Tsanani Mai Raɗaɗi da tsoratarwa a Cikin Qabarin sa, shine a same ki a Ranar Alkiyama ko daga Cikin Qabarin ki a Same ki Ke aikin ki Kenan Wallafa Littatatafai na Novels, a same ki sune abun Sauraron Ki Sune Abunda Kike Karantawa, yadda kika Rike Sunayen Novels Ke ba ki ma Rike Sunayen Annabawa kamar hakan ba ba ki rike sunayen Yaran Manzon Allah ko Sahabban sa Haka ba, yadda kika Rike Sunayen Novels ba ki San Yaya Hukuncin Jinin Hailar ki yake ba, yadda Kike rike Sunan Littafin Novels, ke ba Ki Rike yadda za ki Ɓautawa Ubangijin ki har Allah ya Amsa ibadar ki ba.

Sannan ba ki nema ki sani ba Amma Kullum Tambaya kike yi a Cikin Groups cewa a tura miki Littafi Kaza na Novels za ki Saurara ko zaki Karanta. Ke Kullum ɓata lokacin ki kike yi wajen Sauraron Novels wajen Yin Voice a Groups gurin yin hirar da ba zata amfane ki ba ballatana Rayuwar ki, alhalin ga Babban Aiki tukuru na Jiran ki idan ba ki San su ba Sai Wuta, idan kin San su Sai Aljannah. Domin idan kin San su ne ibadar ki ta gyaru zakiyi su yadda Allah yake so, Amma ba ki San su ba Yaya zakiyi ibadar toh?

Toh Wallahi ki Sani Cewa kina Karanta su Wuta ne, Tamkar Kina Karanta Labarin da zai Sanya ki Cikin Wutar Jahamnama ne. Domin Annabi Muhammad Sallallahu Alahin Wasalam Yace ya isa Mutum Azaba mafi Tsananin Azaba a Same shi yana Karanta Labaran Karya waɗanda aka Kirkiru Domin Nishaɗin Jama'a. Kuma Allah yace Mana idan Kun ga Labari kada ku yada shi sai Kun tabbatar da Sahihin sa, shin Haka kike Yi a novels? Akwai matsala wallahi.

Don Haka Ki ɗena ɓata lokacin ki, ke ba ki San ibadar ki ba amma kin San Novels, za ki fi mintuna 50 kina Sauraron Novels amma ba za ki iya yin Minti 5 kina Karanta Abunda zai Amfane ki Duniyar ki da Lahirar ki ba, ai ke ko Ba'a gaya miki Ke Ƴar Wuta ba ce ai kin san Kanki Ina za ki je, Domin Allahu Subhanallahu Wata'ala Yana Cewa Ku Sanni Kafin Ku Ɓauta Min, Shin ke Kin San Ubangijin ki ne da kike yi masa ibada? Ki tambayi wata Budurwa menene Hukuncin Jinin Haila in ya Zo da wucewar sa me Allah ya Haramta me Allah ya Halatta shiru zatayi, Amma ki tambaye ta Yan Shirin Film da masu novels sai ta lissafo dukka ko Bata Babu.

Kina Zaune a Matsayin ki na Budurwa wadda ta Balaga Nan gaba kadan kema Uwa ce, Duk Wani Hukunci ya Sauka a Kanki kamar yadda yake a kanki Mahaifiyar ki, amma Na Farko Ke ba ki San Menene Tsrakin Ki ba, Hailar ki ya Zo ba ki iya Bambance ah Ƙwanaki Nawa yake yi ba!  Ke ba ki Iya Sanin Cewa yaya Kalan Jinin ki yake ba!  Ke ba ki San Cewa Wannan Jinin Cuta ne wannan Haila bane, ke ba ki iya sanin Wannan yanayin Chanjawar Zuwan Jinin ki ne ba, ke ba ki San komai ba akan Jinin Hailar ki, ah jinin ya zo yaya zakiyi ba, wanne  ne ake yin ibadah wanne ne ba'a Yi? ba ki san komai ba Kuma a Haka zakiyi Aure ki bayar da Tarbiyya wai, amma kin san Littafin Novels, Shin ke da ba ki San Waɗannan Hukunce-hukuncen Hailarki ba wani ibadar ne zakiyiwa Ubangijin ki har Allah ya Amsa? Kin ga Kenan Shakka babu Tamkar kina ibadah ne amma Allah baya Amsar sa, kenan a Ranar Alkiyama Makomar ki ba Aljannah bane, Sai dai Wutar Jahamnama. Allah ya tsare.

Haka Zalika, Kin Zo Kin Haihuwa ba ki iya Iya Bambance Menene Jinin BIQI Yaya Hukunce-hukuncen Sa yake ba, Sannan ke ba ki San yaya Jinin Ɓari yake ba Idan yana Wata 1 ko 2 ko 3 ko 4 ko 6 ba, ke babu wani Abunda kika sani game da Jinin BIQI, Sannan kuma a Hakan wai Kina Ibadar Allah, Shin yaya Ibadar Allah Zai Amsa miki shi? Domin Ubangijin ki yace Ki San Shi Kafin ki Ɓauta Masa, Shi Ubangijin ki mai Tsarki ne, don haka Ba'a Kusantar sa da Ɓauta face sai kina Cikin Tsarki da Tsarkakewa, toh ke ga shi Ba ki san su ba, amma kuma Kullum kina ibadar, Idan kene kike Amsar ibadar Anya za ki amsa ma mai irin Wannan ibadar da bata san yadda Tsarkin ta yake ba? Kenan ko Ba'a ce da ke Ƴar Wuta ba ce ke za ki iya bawa kanki Amsar hakan Matukar dai ba ki San Tsarkin ki ba Kuma ba ki nemi Hanyar sanin ba. 

Sannan Ke Kin Zo Kin Haihu, Kema Kin Zama Uwa ga Ɗiyar ki ta Girma kema ba Ki San yaya Jinin Hailar ki ya ke ba, Ba ki san Yaya Hukunce-hukuncen BIQIN ki yake ba, Sai ga Ɗiyar ki ta zo tana Tambayar ki kuma ba ki San komai ba, amma Kin san Littafin Novels sama da 50 amma ba ki San Hailar ki ba, Shin me za ki gaya mata?? Sannan me Makomar ki a Wajen Ubangijin ki? Domin Allahu Subhanallahu Wata'ala Yana Cewa Dukkan Ku Makiyaya ne Kowanne sai Allah ya Tayar da shi an Tambaye shi Kiwon da Allah ya ba sa, Kenan Kin Shiga Ukku Ƴar Uwa Matukar ba ki tashi kin Nemi Sanin Addinin ki ba amma kin Karkakata ga Duniyar Novels.
 
Mijin Ki ya Zo Yayi Jima'i da ke, Ba Ki San yaya ake Yin Wankan Janaba Ba, Ke Ba Ki San Menene Maniyyi Ba, Ba Ki San Menene Maziyyi Ba, Ba Ki San Menene Wadiyyi ba, babu wani Hukunce-hukuncen da kika sani akan Waɗannan Abubuwan, Shin kina ganin Zakiyi ibadar da Allah zai Amsa Kuwa? Domin ba ki San Ubangijin ki ba kin je kina yin ibadar ki babu Tsarki a Jikin ki, Alhalin ke kina ganin Cewa ai kin yi wanka Kin Tsarkaka, ba ki iya Wankan Ɗaukewar Jinin Haila ba, ke ba Ki iya Na Janaba ba kuma ba ki nema ki sani ba kuma ga shi Kullum sai an yi Jima'i da ke. Amma Rayuwar ki kab ya Karkakata ga Littatafan Novels. Shin ke Ƴar Aljannah ce ko Ƴar Wuta Ce? Shin Yakamata ace an Samu Mace Musulma wadda ta Balaga a Jiya ace wai bata San Waɗannan Abubuwan da muka Lissafa dukka ba? Shin tayiwa Kanta Adalci kenan? Shin idan kin yi ibadar ki a hakan anya Allah zai Amsa kuwa? Wallahi babu Yadda Ubangijin ki zai Taɓa Amsar ibadar ki kai tsaye in ba dai Kin yi ilmi ga Hakan ba. Ku biyo a Hadisai da zamu kawo akan Tsarki da Waɗanda ba su yin sa me yake samun su. 

1- DARASI NA BIYU

KISSAR "HAMZALA R.A"

MUHIMMANCIN YIN TSARKI, MATA MASU YIN FITSARI A TSAYE

👉🏽A Yanzun haka wata tana Ganin Godon Rubutun nan zata ce ba za ta Ɓata Lokacin ta wajen Karanta shi ba domin na Addini ne, amma zata fi Awa tana Karance-Karance  Littafin Novels wadda zata Karanta su kuma ta Ɓata Lokacin ta  ba tare da Sanin Addinin ki kike yi ba, kuma ba ta san komai ba game da Addinin ta akan Tsarkin ta ma, amma ta karkata a aikin Banza na Karanta Labarin Karya. Azaba Ce gare ki a Ranar Alkiyama matukar ba'a tuba an Dena ba. Allah ya Shirya Ameen.

Ya Tabbata a Cikin Hadisi Annabi Muhammad Sallallahu Alahin Wasalam Yana Ce Wa *BILAL* ya Bilal Shin Wani Irin Aiki ne Kake Aikatawa har na ji Takun Takalmar ka a Cikin Gidan Aljannah?  Sai Bilal R.A yace, Shi ya Kasance Duk Alwalar da Yayi Sa, toh fa Sai Yayi Sallar Nafila Raka'a Biyu, Muhallin Sha'id anan Shine, Yin Alwala Da Shi Bilal yake Yi Shine Allah yayi masa Sakamako da da Wannan Babbar Ƙyautar.

Shin ke a Yanzu inda Za'a Bincika Alwalar ki da Sai an Samu Kurakurai Sosai wata Kila ma a Samu ba ki Iya Alwalar ba Shin yaya Ibadar ki kuma yake toh?  Ga shi Annabi Sallallahu Alahin Wasalam yana Cewa Babu Sallah ga Wadda ya zo Yin Alwala Amma bai yayi Bisimillah ba wato bai Ambaci Sunan Allah ba, Shin Sau nawa ne kike yin Alwalar babu Bisimillah?  Kuma ba ki san Hukuncin ba. Amma kin iya Sanin Komai na iskanci Kala-kala kin iya ɓata lokacin ki wajen Chatting amma ba ki iya Ɓata Lokacin ki wajen sanin Addinin ki ba.

Annabi Muhamma Sallallahu Alahin Wasalam wata Rana Suna tafiya a Bayan Gari akan Hanya kusa da Wani MAQABARTA da Sahabbai, Sai Annabi ya tsaya Sahabbai suka Ji Annabi yayi Shiru ya Tsaya, Sai Suka ga Annabi ya Cire wani itace Ɗanye ya Ajiye ya Da sa Shi akan Qabarin Mutane guda 2, Sai Sahabbai Suka tambayi Annabi Ya Manzon Allah, Shin meyasa ka Tsaya anan Sa'annan me yafaru da Waɗannan Bayin Allahn da aka da sa musu itace a Qabarin su??  Sai Annabi Muhammad Sallallahu Alahin Wasalam Yace da su, Dalilin da yasa na Tsaya Waɗannan Bayin Allahn Azaba ce Ake yi Musu a Cikin Qabarin Su, Wannan itace da na Cire na Sanya musu Shine zai sa su ɗan Samu Rahama idan ya Ɓuce Azabar ta dawo Sabo.

Sai Sahabbai Suke Tambayar Annabi Muhammad Sallallahu Alahin Wasalam Shin toh Wanne Irin Aiki ne Suke Aikatawa har Ubangiji yake Musu  irin wannan Azabar a Qabarin Su?  Sai Annabi yace da su,  Ɗaya daga Cikin su ya Kasance Idan yana Tsarki baya yin sa yadda Yakamata, a Wani Ruwayar ai ya Kasance idan yana Fitsari yana Barin Fitsarin yana Wasewa har Digadigin Kafafun sa, Fitsarin yana Watsewa Sannan a hakan yake ibadar sa, Wannan ne ya sa Allah yake yi masa Azaba a Cikin Qabarin sa har Ranar Alkiyama. To Ina Mata masu Fitsari a Tsaye? A ji tsoron Allah.

Kenan ya isa mutum Azaba a Cikin Qabarin sa a Samu Fitsarin ki yana Watsewa akan Kafafun ki ga shi kuma ke ba ki San hukuncin hakan ba, Shin idan Allah ya Ɗauki Rayuwar ki a Hakan wani Hali kema za ki Kasance a Cikin Qabarin ki?

Annabi Sai sake cewa da Su Ɗayan Kuma ya Kasance bai da Aikin Komai Sai Yin Annamimanci, Aikin Sa kenan ya Haɗa Ƴan Uwa Faɗa ya Rikitar anan ya haɗa a wancann.

Ƴar Uwa ki duba Mahimmancin Yin Tsarki Fa, Ɗaya daga Cikin Sahabbai Mai Suna *HAMZALA* yayi Sabon Aure, sai Wata Rana Kawai Yayi Jima'i da Matar Sa, irin da dare ga shi Goshin Asuba ne, Kawai Sai Annabi yayi Kira yace kowa ya fito a Fita Yin Jihadi.

Yanzu dai inda kene Farko za ki Fara Hana Mijin ki Tafiya Domin za ki ce daga yin Auren sa sai fita zuwa Jihadi idan ya je ya Mutu a Can fah kenan kin dawo Bazaura!  Ah hakan Sai ki hana shi, kai shima zai ce ba zai je ba domin yayi Sabon Aure. Amma da yake Sahabbai ba Rayuwar Duniyar ce a gaban su ba Lahirar ita ce komai, HAMZALA R.A ya mike ya tashi Suka tafi yin Jihadi ya bar Amaryar sa da ya Auro Jiya-Jiya, Ya tafi Yin Jihadi a Can Fagen Yaƙi haka aka Kashe HAMZALA.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Jinin Haila: Abubuwan da Yakamata Kisani Dangane da Al'adar ki"

Post a Comment