HUKUNCIN WANDA YAYI ZINA DA MATAR DA ZAI AURA

TAMBAYA TAMBAYA TAMBAYA
Assalamu alekum algafarta malam barka da war hakah. Tambaya daga dalibinka daga danko wasagu L. G na kasance inada wadda xamuyi aure da itah amma nabiya sadaki saidai muna saduwa da junanmu amma ban bari maniyina yaxuba daga naga zaizo sai incire, bana bari yaxuba kuma nagaji dayin haka gashi aure yakusa minene hukuncina?
Allah yabada ikon amsa tambaya nagode asha ruwa lafiya.

             AMSA
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Hukuncinka daidai kake da kowanne mazinaci. Sai dai kai naka laifin yafi muni tunda aciki har da cin amana wato zamba cikon aminci.
Iyayenta sun amince dakai, sun yarda zasu baka aurenta har an dauki rana, amma ka biyewa shaidan ka yaudari 'yar mutane kana zina da ita.
Zina dabi'a ce ta marassa cikakken imani. Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace "Mazinaci ba zaiyi zina alhali yana mumini ba".
Rashin zuba maniyyinka acikin mahaifarta bai zaisa ka samu wani sassauci acikin girman laifin ba. Don haka nake jan hankalinka cewa kaji tsoron Allah ka tuba ka dena wannan zinar da kukeyi. Amma ka sani cewa wajibi ne tayi istibra'i kafin a daura muku aure. (wato zata zauna agida har sai tayi jini uku). Amma wasu Maluman sun ce koda jini guda ne ya wadatar.

 GARGADI : Anan nake jan hankalin iyaye cewa kada ku rika barin 'yarku tana kebancewa da saurayi koda bayan ya biya sadakin nata ne. Kada ku amince da irin wannan barnar.
Biyan sadaqi 'daya ne kawai daga cikin sharudan aure amma ba shine auren ba. Don ya biya sadaqinta bata zama matarsa ba. Ko mutuwa yayi babu gado atsakaninsu.
Don haka idan zaizo hira ya rika zuwa da yamma, ido na ganin ido. Kuma ku samo wata Qanwarta mai wayo ku zaunar da ita tare dasu.
Mutukar Baligi ya kebance da baligah, to shaidan fa shine na ukunsu. Zai rika chusa musu sha'awar junansu har sai sun fara ta'ba jikin juna, daga nan kuma sai zina. (Allah shi kiyayemu ya kiyaye mana zuriyarmu).

WALLAHU A'ALAMU

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "HUKUNCIN WANDA YAYI ZINA DA MATAR DA ZAI AURA"

Post a Comment