MIJINTA YA HANATA SHIGA ISLAMIYYA

:


As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah

Ina son mijina ya sa ni a Islamiyyah, amma sai ya ce ba ya son a fita a bar masa gida babu kowa! To, malam wai a cikin haƙƙoƙin aure babu neman ilimin addini ne? Kuma shin dole ne in yi masa biyayya a kan hakan?

          AMSA
Wa Alaikis Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Wajibi ne a kan mace ta yi wa mijinta biyayya a kan duk abin da bai saɓa wa dokokin Allaah Ubangijin Halittu ba.

Idan miji ko wani shugaba ya yi umurni da wani abin da ya saɓa wa dokokin Ubangiji, to ba za a yi masa biyayya ba.

Amma ko hana mace zuwa makarantar Islamiyyah yana daga cikin saɓon da mace za ta ce ba za ta yi wa mijinta biyayya a kan hakan ba?

Malamai sun yi ƙarin bayani:

(i)  Idan har mace tana da ilimin sanin abin da addininta ba ya tsayuwa sai da shi, kamar ilimin sanin haƙƙoƙin Allaah da Manzonsa _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam),_ da ilimin sanin sauran Rukunnan Imani da Rukunnan Musulunci da sauran nau’ukan Zikirori tare da yadda ake yin dukkan ayyukan aqida da ibada a sunnace. Haka kuma idan tana da ilimin sanin yadda ake gudanar da wasu mu’amalolin da suka shafe ta a tsakaninta da sauran jama’a, da sauran ladubban da shari’a ta tsara a kan al’amuran rayuwanta na yau da kullum, da kuma yadda ake zama da miji da kishiya ko kishiyoyi da maƙwabta, da yadda ake gyara gidan aure, da yadda ake tarbiyyar ’ya’ya a ciki da wajen gidan aure, da sauran abubuwa dai makamantan wannan. Idan har mace ta san waɗannan, to ba dole ne sai ta fita zuwa wata makarantar Islamiyyah a kusa ko a nesa ba.

(ii) Idan kuma ba ta sani ba, amma kuma mijin nata malami ne masani, wanda kuma ya ke da lokaci ko hali ko ikon karantar da ita duk irin waɗannan abubuwan, to a nan ma ba lallai ne sai macen ta fita zuwa makarantar Islamiyyah ba.

(iii) Idan kuma ya zama mijin ba shi da sani, ko kuma ba shi da lokaci ko hali ko ikon karantar da ita, to a nan wajibi ne ya samo mata wanda zai karantar da ita daga cikin muharramanta, waɗanda keɓancewa da su bai zama mai haifar da wani abin da shari’a ta yi hani ba.

(iv) Idan kuwa wannan ɗin ma ba zai samu ba, to wajibi ne miji ya yi wa matarsa izini ta shiga nagartacciyar makarantar Islamiyyah, domin a koya mata irin waɗannan abubuwan da ba ta sani ba. Amma abu ne mai kyau ya bincika ya tabbatar makarantar tana daga cikin waɗanda ake kulawa da tsari da dokoki, tare da bin ladubba na shari’a a cikinta daidai gwargwado. Kuma ya san cewa samun waɗansu ’yan matsaloli a makarantu kar ya hana shi barinta zuwa makarantar, domin babu sharri ko ɓarnar da ta fi jahilci.

(v) Idan kuma duk da samuwar irin wannan makarantar mijin ya yi ƙememe ya hana matar zuwa Islamiyyah, to a nan wasu malamai suna ganin ya halatta ta fita ko da ba da yardarsa ba, kuma ba ta yi laifi ba. Amma duk gudun buɗe ƙofar fitina muna ba da shawarar ta fara sanar da manyansa sannan manyanta kafin ta ɗauki wannan matakin.

Malamai sun ciro duk waɗannan bayanai ne a ƙarƙashin maganar Allaah Ta’aala mai cewa:

يآ أيها الذين ءامنوا قوا أنفسكم وأهليكم نارا وقودها الناس والحجارة
Ya ku waɗanda suka yi Imani! Ku kare wa kanku da iyalanku wata Wuta: Makamashinta mutane ne da duwatsu.
(Surah At-Tahreem: 6).

Abu ne sananne kuwa cewa tsare kai ko kare kai daga Wutar Lahira ba ya yiwuwa sai da bin dokokin Allaah _(Subhaanahu Wa Ta’aala)_ ta yadda ya tsara. Kuma bin dokokinsa daidai wa daidai ba da sakaci ba, kuma ba da zaƙewa ba, ba ya yiwuwa sai da ilimi.

Shiyasa da na janyo wannan ayar a cikin ayoyin da suke bayani a kan Haƙƙoƙin Ma’aurata, sai kuma na ambaci cewa:

Wannan ya nuna abubuwa kamar haka:

(1) Haƙƙin miji da mata ne su tabbata a kan bin dokokin Ubangiji Ta’aala a cikin komai, domin su kare kansu daga Wutar Lahira.

(2) Haƙƙin miji ne ya karantar da matarsa kuma ɗora ta a kan bin dokokin Ubangiji Ta’aala ta yadda zai gyara rayuwarta a duniya da Lahira, kuma ya kare ta daga shiga Wuta a Lahira.

(3) Haƙƙinsa ne na wajibi, idan ba zai iya ba saboda rashin sani ko rashin iko, ya yi mata izini ta tafi makaranta, inda za a koya mata hakan.

(4) Haƙƙin mata ne ta yi wa mijinta biyayya a cikin duk abin da ba saɓon Allaah ko Manzonsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba ne.

(5) Haƙƙin miji da mata ne su san cewa: Aikin Imani ne su yi tsayin-daka wurin hana kansu da iyalansu aikata duk abin da zai kai su ga zama makamashin Wuta a Lahira.

Allaah Ta’aala ya ƙara mana fahimta.

Wal Laahu A’lam

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "MIJINTA YA HANATA SHIGA ISLAMIYYA"

Post a Comment