Amfanin Hulba: Man Hulba, Garin Hulba, da yayan Hulaba
1)Ana maganin ulser da garin hulba, idan ake hada hulba cokali daya na hulba, cokali daya na zuma mara hadi asha, duk bayan awa 8.

2)Tana taimakawa akan ciwan tari Mai tsanani wanda bayajin magani, ko yaki warkewa, da kuma bangaren matsalolin ciwan kunhu,ko asama inda zaa rika tafasa hulba, ko azuba arwan dumi abar shi minti 10-15 sannan asha, zaayi hakan sau uku arana.

3)Hulba tana karama hanjin mutum karfi tafuskar narkar da abinci, da kuma sauki wajen tafiyar sa.

4)Tana taimakawa mazaje wajen basu nishadi, da kuma karin kuzari, musamman tafuskar maza, idan andaka yayan habba, tare da yayan hulba sai azuba aruwan dumi ,abar shi minti 10-15 ko sama sannan asha indai sunada kya babu algush, kuma basu lalace ba kwana biyu zuwa uku ne zaka sakamakon aikin akan abinda nafada insha Allah.

5)Hulba tana magance rashin bayan gida wanda yake faruwa sakamakon cin abinci mara tsafta, da sauran rashin bayan gida wanda wasu matsalolin suke haddasawa.

6)Tana karfafa mahaifha, tare da nishadar ta da ita ga mata shi yasa mata kanyi amfani da ita awatan 9 domin samun sauki wajen haihuwa.Bayan haka wajen karbar haihuwa amfani da man zaitun yana saukaka wa, kuma yataimaka wajen haihuwa Lafiya, batare da mace tasamu Kari ba, koda kuwa haihuwar farko ce, wannan kam abune da aka jarraba, ko aka tabbatar insha Allah.

7)Hulba tana saukaka radadi ciwan mahaifha, ko ciwan mara tahanyar dafata ana shiga cikin ruwan na mintina 10.
Bayan ahada hulba da habbatusauda da Kisdul hind anayin shayin sa tare da zuma ana sha.

8)Hulba tana baiwa gool blader nishadi, tana  Kara sinadari insulin acikin jini, wanda hakan akarshe zata iya saukaka ciwan suga ga masu fama da ciwan suga, zaa yi wannan ta hanyar shan cokali daya na garin hulba mai kya arana sau uku.

9)Tana rage yawan kitse ajiki wanda yake karuwa, don haka akarshe idan ana sha zatayi reduced na cholostrol na cikin jini wanda yake cutar da jiki, tare da dagowa na cholostrol Mai amfani.

(10)Hulba tana Kara bubbgowa da ruwan no-no musamman ga mata masu shayarwa,shi yasa likitoci sukan bayar da shawara arika shan man hulba sau uku arana.


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Amfanin Hulba: Man Hulba, Garin Hulba, da yayan Hulaba"

Post a Comment