FALALAN ADHKAR: FALALAR YIN ZIKIRI DA AMFANIN SA



1. Yawan zikri yana korar sheɗan
2. Yawan zikri yana jawo samun yardar Allah
3. Yawan zikri yana gusar da damuwa da baƙin ciki daga zuciya
4. Yawan zikiri yana jawo farin ciki da annushuwa da nasaɗi a zuciya
5. Yawan zikiri yana ƙarfafa zuciya da jiki.
5. Yawan zikiri yana haskaka fuska da zuciya
7. Yawan zikri yana jawo arziki
8. Yawan zikri yana jawo samun kwarjini da jin dadi da farin jini
9. Yawan yana jawo samun ƙaunar Allah ta'ala, samun ƙaunar Allah shine babban buri.
10. Yawan zikri yana jawo kusanci da Allah, har a wayi gari mutum ya samu matsayin ihsani.
11. Yawan zikri yana jawo komawa zuwa ga Allah ta'ala, cikin farin ciki
12. Yawan zikri yana buɗewa mutum kofa ta samun yarda, da kusanci (Alƙurbiyya) tsakanin sa da Allah ta'ala.
13.. Yawan zikri yana buɗewa mai yinsa babun ilmi, duk sanda ya yawaita ambaton Allah, zai ƙara sanin Allah ta'ala.
14. Yawan zikri yana buɗewa mutum matsayin ganin buwayar Allah ta'ala, da isar sa.
15. Yawan zikri zai sa Allah ya ambaci mai yawan yi, duk sanda ya Ambani Allah, shima zai ambace shi.
16. Yawan zikri yana raya zuciya domin zikri ga zuciya kamar kifi ne a cikin ruwa, yaya kifi yake kasancewa idan aka raba shi da ruwa? Haka mutum zai kasance idan baya ambaton Allah ta'ala.
17. Yawan ambaton Allah yana zama kamar abinci ga zuciya da rai.
18. Yawan zikri yana washe zuciya ya goge tsatsa daga cikin zuciya.
19. Yawan zikri yana kankare zunubi
20. Yawan zikri yana kare mutum daga ɗimuwa da gafala.
21. Yawan zikri idan yana tuna Allah a cikin yalwa da wadata , Allah zai fidda shi daga cikin halin tsanani.
22. Yawan zikri yana tsaratarwa daga saukar azaba.
23. Yawan zikri yana jawo saukar nutsuwa da saukar rahma, da lulluɓewar Mala'iku,
24. Yawan zikri yana shagaltar da harshe ga barin giba da gulma da ƙarya Annamimanci, da ashariya.
25. Majalisin da ake zikri, sheɗan baya zama a wajan
Albarka tana sauka a Majalisin da ake zikiri.
26. Yin zikri yana kare mutum daga hasarar lokaci, da tashi da warin mushen jaki daga majalisi.
27. Duk wanda ya ambaci Allah a ɓoye, har ya yi hawaye don ganin girman Allah, zai shiga inuwar al'arshi ranar Alƙiyama.
28. Idan yawan zikri ya ɗaukewa mutum hankali, har ya zama baya rokon wata bukata, Allah zai bashi fiye da dukkan masu roƙo suka roƙa.
29. Zikri shine mafi saukin ibada mara wahala kuma ga yawan lada.
30. Daga cikin falalar zikiri, yana jawo a dasawa mutum bishiya a gidan Aljanna, kamar yadda yazo a hadisi, Duk wanda ya ce Subhanallahil azeem wa bihamdihi.
31. Daga cikin falalar zikri, Kalmomi guda biyu masu saukin faɗa akan harshe masu nauyi akan sikeli, abin ƙauna a wajan Allah, Subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil azeem.
32. Dawwama a cikin zikiri yana ƙare mutum daga taɓewa.
33. Zikri yana zama a kowane hali, babu sharaɗin sai da Alwala ko tsarki.
34. Yawan zikri haske ne, a duniya da ƙabari da makoma da siraɗi.
35. Yawan ambaton Allah shine tushen komai, idan ka sami arziƙin yawan sa ka gama sumun dukkan komai daga Allah.
36. Zikri yana kusanta abinda yake nesa, na buƙatu kuma yana nisanta abinda yake kusa, na damuwa da baƙin ciki.
37. Zikri yana tashin zuciya daga baccin gafala.
38. Yawan zikri yana jawo samun ɗanɗano mai faranta rai.
39. Mai yawan ambaton Allah, kada ka damu domin Allah yana tare da kai.
40. Yawan zikri yayi daidai da fita yaƙi da ciwar da dukiya mai yawa.
41.. Ambaton Allah shine tushen nuna godiya ga Allah, domin duk wanda baya zikri baya godiya.
42. Zikri yana jawo samun ni'ima daga Allah kuma yana tunkuɗe Sakar fushin Allah. Mafi darajar mutane a wajan Allah shine wanda harshen sa ya zamo ɗanye a wajan ambaton Allah ta'ala.
43. Allah ta'ala da Mala'ikun sa suna yin salati ga mai yawan ambaton Allah.
44. Yin zikri shine Asalin samun soyayyar Allah da tsira daga faɗawa cikin maƙiya Allah ta'ala.
45. Yawan zikri yana jawo a sami katon dausayi a cikin aljanna.
46. Majalisin zikri wajan zaman Mala'ikun Allah ne.
47. Dukkan ibadu da Allah ya yi umarni a yi babbar Manufar su shine yawan ambaton Allah.
48. Dukkan ibadar da ake ambaton Allah da yawa a ciknsa tafi dukkan sauran ibadu kamar sallah bayan Tauhidi.
49. Yin zikri yana tsayawa a matsayin Sadaƙa da Aiyukan lada da ake yi da dukiya.
50. Ambaton Allah yana ƙara ƙarfin imani.
51. Yawan zikri yana sauƙaƙewa mutum duk wani abu mai wahala.
52. Yawan zikri yana jawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.
53. Zirki yana zama kariya daga sharrin magauta da maƙiya, musamman zikirin safe da yamma, da lokacin bacci.
54. Yawan zikri yana ƙare mutun daga munafunci domin munafukai basa ambaton Allah da yawa.

Misalin zikri,لااله الاالله وحده لا شريك له له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير
duk wanda ya karanta wannan zikri ƙafa 100, da safe zai sami abubuwa guda biyar:
Kamar ya ƴanta bayi goma, sai lada 100, za a kankare masa zunubi 100, zai zame masa tsari daga sheɗan a wannan rana har zuwa yamma, babu kuma wanda yazo da wani abu da yafi nasa a wannan rana. Bukhari da Muslim.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "FALALAN ADHKAR: FALALAR YIN ZIKIRI DA AMFANIN SA"

Post a Comment