Anfanin Madara Peak Hade da Maltina


A can da a kan sha madarar peak ko maltina ita kadai ba tare da an hada su da juna ba. Daga bisani ilmin kimiya ya gano alfanun hada maltina da peak milk ya kuma bada tabbacin yin haka wanda wannan baida wata illa asali ma zai zamo wani hadi na musamman mai tasirin gaske ga lafiyar jikin dan’Adam duba da irin muhimman sinadirrai da madara da kuma maltina take dauke da su. 
Maltina tana dauke da sinadarai kamarsu carbohydrate, protein, fat, calcium, Bitamin A,bitamin B1, Bit B2, Bit.B3, bit B5, Bit B6, bit C. Haka zalika madara tana dauke da wasu sinadirran dake gina jiki zamanta daga cikin abinci nau’in protein, tana dauke da sinadirran dake karfafa kwakwalwa da saita tunani da kuma karfin kassa da kwarin jiki. A don haka hada su a waje daya na da matukar amfani.

Ga kadan daga cikin dalilan da zai sa a hada maltina a tare da madarar peak:

1.Mai fama da jinya nada bukatar samun wadataccen jini domin ita jinya musamman doguwar jinya takan tafiyar da jini da kuma karfin jiki. Maltina + peak na samar da jini sosai dan haka sai a rinka hada gongoni daya na kowace a cikin kofi sai a sha.

Wanda ya bada gudummuwar jini ga wani majinyaci ko ya bayar a matsayin sadaka ga wadanda wani hatsari ko rashin lafiya ta afkawa to sai ya sha maltina da madara.
Wanda aka yiwa aiki yana bukatar maltina da madara. Sai dai a kula ba sha za a yi har a bake ciki ba musamman ga wanda aka yiwa aiki.

Macen da ta haihu musamman idan ta gamu da zubar jini a yayin haihuwar itama tana bukatar maltina da madara.
Mai fama da basir mai tsiro wanda ke haddasa zubar jini wato wanda kan tafiyar da jinni sai a sha maltina da madara.
Macen da ta yi al’ada ta kare musamman matan dake fama da al’ada mai nauyi itama tana bukatar maltina da madara.

Wanda ke ganin juyuwa da zaran ka tashi ko kana tafiya kanaganin kamar za ka fadi to sai a sha maltina da madara.
Mai fama da karamcin jini a saboda wasu dalillai kona rashin lafiya kona karamcin samun wadataccen abinci mai gina jiki ko wata lalura daban.
Wanda ya ji ciwon da ya kai shi ga zubar jini ko wani rauni sai a sha maltina da madara.

Haka kuma idan ma kana jin jikinka ba karfi ga yawan kasala to za ka iya shan maltina da madara na tsawon sati daya za ka ji banbanci indai ba wata rashin lafiya bace a tare dakai.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "Anfanin Madara Peak Hade da Maltina"

Post a Comment