YaYan Kankana: Amfanin Shan Kwallon Kankana ga Lafiya



Idan ka sha kankana to ka daina yada qwallan,maimakon haka sai ka tarasu a waje daya ka wanke ka shanya a rana har su bushe, ko ka siyo wadanda ake siyarwa a herbal medicine store.
Zaka dauki qwara 20 zuwa 30  sai ka niqe su,har sai sun koma gari (powder).
sai ka nemi ruwa misalin liter daya da rabi ka zuba garin ka tafasa sai ruwan sun tafasa.
Shikenan hadin ya kammala.

Zaka sha sau daya a kullum amma zaka dakata a duk bayan kwana uku.Idan ka sha na kwana biyu to a ran na uku ba zaka sha ba,sai washe gari.A haka zaka rinka yi har zuwa wani lokaci ya danganci ciwon da ake son magancewa da kuma jimawar matsalar a jiki.

πŸ‘‰ Domin samun zuciya mai koshin lafiya da rage yawan wasu wasi.

πŸ‘‰ Maganin yawan batun zuci.

πŸ‘‰ Karawa garkuwar jiki karfi da kuzari.

πŸ‘‰ Samun maniyi mai rai da maganin karamcin haihuwa ga namiji.

πŸ‘‰ Gyaran ciki da hanji da wankin dattin ciki.

πŸ‘‰ Yana haskaka fatar jiki

πŸ‘‰ Domin saurin  warkarda gyambo ko wani rauni a jiki.

πŸ‘‰ kariya daga barazanar kamuwa da ciwon Sugar.Idan kana fuskantar wannan barazanar to ka jarraba wannan maganin.

πŸ‘‰ Rage nauyin jiki da qiba.

πŸ‘‰  Maganine ga masu fama da anemia.

πŸ‘‰ Yana maganin basir mai tsiro.

πŸ‘‰ Rage kumburin hanji,kumburin ciki,kumburin jiki da sauransu.

πŸ‘‰ Samun karfi da kuzarin kasusuwan jiki.

πŸ‘‰ Yana samarda jini a jiki

πŸ‘‰ Yana wanke qoda da sauran datti.

πŸ‘‰ Maganin ciwon jiyojin jiki.

πŸ‘‰ Yana kare jiki daga barazanar kamuwa da ciwon daji.

πŸ‘‰ Yana wargaza tsakuwar koda.

Maganin zafin fitsari da toshewar Mara.
A yi share zuwa ga yan uwa da abokai.
Bamu ya fewa duk wanda ya kwashi rubutun mu ,ya yi editing ya cire sunan shafin da ya wallafa rubutun ya sanya na shi ba.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YaYan Kankana: Amfanin Shan Kwallon Kankana ga Lafiya"

Post a Comment